Toni Kroos: Ɗan wasan Real Madrid da Jamus zai yi ritaya bayan kammala gasar Euro 2024

Spread the love

Daga MAHDI M. MUH’D

Ɗan wasan tsakiya na Real Madrid da Jamus, Toni Kroos zai rajaye takalmansa daga buga wasan ƙwallon ƙafa bayan gasar Euro 2024 da za ta gudana a Jamus ɗin.

Ɗan wasan mai shekaru 34, ya yi fice a ƙwallon ƙafa, inda ya lashe kofuna da dama tare da Real Madrid tun bayan da ya koma ƙungiyar daga Bayern Munich a watan Yulin shekarar 2014, inda ya lashe kofin La Liga da na zakarun Turai sau 4 kowanne.

Kroos na cikin tawagar ƙwallon ƙafar Jamus da ta lashe gasar kofin duniya a shekarar 2014.

A watan Yulin shekarar 2021, ya yi murabus daga buga wa ƙasarsa wasa, amma kuma ya dawo, bayan wata tattaunawa da mai horar da tawagar ƙwallon ƙafar Jamus, Julian Nagelsmann.

Kroos ya fara buga wa Bayern Munich wasa a gasar Bundesliga yana ɗan shekaru 17 a watan Satumban sshekarar 2007, kuma a kakar ce ya lashe kofin Bundesliga.

By Editor