Editor

9513 Posts
Ina son rubutuna ya zama silar sauyin rayuwar wasu – Safiyya Mukhtar Garba

Ina son rubutuna ya zama silar sauyin rayuwar wasu – Safiyya Mukhtar Garba

"Satar fasaha ce babba matsalar marubuta" Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU Safiyya Mukhtar Garba na daga cikin matasan da suke ƙoƙarin tasowa a tsakanin marubutan adabi. Ta fito ne daga Jihar Kano a Ƙaramar Hukumar Gwale. Tun Safiyya na ƴar shekara 13 ta fara nuna sha'awarta ga karatun littattafan Hausa, har ita ma ta kai ga tunanin fara ƙirƙirar nata labarin, sakamakon yadda ta fahimci cewa marubuta suna ba da gudunmawa ne ga gyaran al'umma ta hanyar rubuce-rubuce na hannunka mai sanda da nuni cikin nishaɗi. A tattaunawarta da wakilin Blueprint Manhaja Abba Abubakar Yakubu, marubuciyar ta bayyana masa burinta na…
Read More
Yanzu-yanzu: Kotu ta ba da belin Abba Kyari

Yanzu-yanzu: Kotu ta ba da belin Abba Kyari

A ranar Laraba Babbar Kotun Tarayya ta ba da belin DCP Abba Kyari, na mako biyu. Kotu ta ba da belin ne don bai wa Kyari damar zuwa kammala jana'izar mahaifiyarsa da ta rasu. Kazalika, Kotun ta tsayar da ranar Juma'a, 31 ga Mayu a matsayin ranar da za ta yi matsaya kan buƙatar belin da Kyari ya gabatar mata. Idan ba a manta ba, Kyari na fuskantar shari'a ne kan tuhume-tuhume masu nasaba da ta'ammali da miyagun ƙwayoyi daga hukumar NDLEA.
Read More
Cikar Tinubu shekara guda kan mulki: Babu wani bukin a-zo-a-gani da za a shirya —Idris

Cikar Tinubu shekara guda kan mulki: Babu wani bukin a-zo-a-gani da za a shirya —Idris

Ministan Labarai da Wayar da Kai, Mohammed Idris, ya bayyana cewa, ba za a shirya wani biki na a-zo-a-gani ba don cikar Shugaba Bola Tinubu shekara ɗaya a kan mulkin Nijeriya. Idris ya shaida wa manema labarai haka ne ranar Laraba a Abuja. A cewar Ministan, an ɗauki wannan mataki ne don cika manufar Tinubu ta yi wa ƙasa hidima yadda ya kamata da kuma yin amfani da dukiyar ƙasa don amfanin 'yan ƙasa. Ya ce, “bukin ba zai zama ƙasaitacce ba, illa iyaka za a bai wa ma'aikatu damar yin bayani kan ayyukansu. “Wannan ya yi daidai da manufar…
Read More
Ƙwarewa a sana’a ita ce gaba da samun digiri – Dogondaji

Ƙwarewa a sana’a ita ce gaba da samun digiri – Dogondaji

Daga AMINA YUSUF ALI A yayin da kafafen yaɗa labarai suke ci gaba da tafka muhawara game da fififkon ilimin digiri a kan sana'a, mun samu zantawa da Malam Yahya Dogondaji wanda matashi ne wanda ya yi wa 'yanuwansa matasa zarra wajen yaƙi da talauci, ta hanyar yi wa kansa fafutuka da kuma horas da matasa masu dama a ƙarƙashin sana'ar sa ta gyaran waya da kuma samar da guraben ayyuka ga matasa da dama. Hakazalika, ya kasance mai tallafa wa marasa galihu ta gidauniyarsa. Wakiliyar MANHAJA BLUEPRINT, Amina Yusuf Ali ta samu tattaunawa da Malam Yahya Dogon daji, kuma…
Read More
Da Ɗumi-ɗumi: Gobara a sakatariyar gwamnatin Kaduna

Da Ɗumi-ɗumi: Gobara a sakatariyar gwamnatin Kaduna

Bayanan da muka samu yanzu-yanzu daga Jihar Kaduna sun ce, an samu aukuwar gobara a sakatariyar gwamnatin jihar, lamarin da ya yi sanadaiyar ƙonewar wasu ofisoshi. Wani ganau, Malam Ibrahim Mohammed, wanda ma'aika gwamnatin jihar ne, ya ce iftila'in ya auku ne da misalin ƙarfe 2:30 na rana wannan Larabar. Ya ce duk da dai ba a kai ga gano musababbin gobarar ba, amma ana zargin hakan ba ya rasa nasaba da wutar lantarki. Ya ƙara da cewa, ba a samu asarar rai ba, amma muhimman kayayyaki da dama sun ƙone ƙurmus. Ya zuwa haɗa wannan labari, babu wani ƙarin…
Read More
Ƙungiyoyin mata sun buƙaci a inganta samar da abinci mai gina jiki ga jarirai

Ƙungiyoyin mata sun buƙaci a inganta samar da abinci mai gina jiki ga jarirai

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Wasu ƙungiyoyin addini masu zaman kansu na mata sun yi kira da a inganta abinci mai gina jiki ga jarirai da ƙananan yara a ƙasar. Shugabannin Ƙungiyar Mata Musulmi ta Nijeriya; Sakatariyar Katolika ta Nijeriya; Ƙungiyar Matan Kirista ta Nijeriya; da kuma Cocin 'Redeemed Christian Church of God' sun yi wannan kiran ne a lokacin ziyarar da su ka kai na bada shawarwari ta hanyar Cibiyar Sadarwa da Tasirin zamantakewa, ga mata a wasu yankuna, tare da kira da a inganci abincin da mata ke ci domin su samu damar bai wa jarirai abinci mai gina…
Read More
Shugaban ƙasa, talakawa na maka godiya

Shugaban ƙasa, talakawa na maka godiya

Tare da ABBA ABUBAKAR YAKUBU ’Yan Nijeriya sun cika da farinciki da jin daɗi sakamakon amincewar da Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi na dakatar da batun fara cire harajin Yaƙi da Zamba ta Intanet daga kowacce hadahadar kuɗi da ’yan Nijeriya suka yi a wayoyinsu ko kuma ta na'urar sadarwa, wanda Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya sanar da cewa za a fara cirewa a mako mai zuwa. Rahotanni sun bayyana cewa, shugaban ƙasa ya sanar da dakatar da shirin na CBN ne biyo bayan kiraye-kiraye da ƙorafe-ƙorafe daga sassan ƙasar nan kan illar da hakan zai yi a…
Read More
Masarautar Burumawa (1)

Masarautar Burumawa (1)

Daga MAHDI M. MUHAMMAD A yau Manhaja za ta duba irin gwagwarmayar da ’ya’yan kabilar Burumawa suka yi wajen kafa masarautarsu a Jihar Filato. Burumawa, ƙabila ce wacce ta fi yawa a Ƙaramar Hukumar Kanam da ke Jihar Filato, yawanta ya kai kashi 80 cikin 100 na jama’ar ƙaramar hukumar. Haka kuma ana samun su a Ƙaramar Hukumar Wase, inda a can yawansu ya kai kashi 40 cikin 100 na jama’ar ƙaramar hukumar. Sannan ana samun su a garuruwan qananan hukumomin Lantang da Shendem da Kua’an-Pan da sauransu a Jihar Filato da wasu yankunan Tsakiyar Nijeriya kamar Wukari a Jihar…
Read More
Matashin da ya cinna wa masallata wuta a Kano ya amsa laifinsa

Matashin da ya cinna wa masallata wuta a Kano ya amsa laifinsa

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Matashin da ya banka wa masu sallah a Masallaci wuta a jihar Kano, ya amsa laifin da ake tuhumarsa da aikatawa a gaban kotu. Mutumin mai shekara 39 wanda ya gurfana a gaban wata kotun shari'ar Musulunci da ke birnin na Kano, inda aka tuhume shi da laifuka uku, ya ce ya amince da tuhume-tuhumen da aka karanta masa. A ranar Laraba 15 ga watan Mayu ne matashin ya cinna wuta a wani masallaci da ke ƙaramar hukumar Gezawa ta jihar Kano, daidai lokacin da ake ibada. Yanzu haka mutanen da suka rasa rayukansu sanadiyyar…
Read More
Yadda za ka ɓullo wa maganar ƙaro aure (2)

Yadda za ka ɓullo wa maganar ƙaro aure (2)

Tare da AMINA YUSUF ALI Barkanmu da saduwa a wani makon. A makon da gabata mun fara kwararo jawabi a kan yadda namiji zai ɓullo wa maganar ƙaro aure. Mun fara kawo wasu shawarwari yadda za a kauce wa fitina. Yanzu za mu tashi daga inda muka fara a makon da ya gabata. Abu na gaba, akwai wani ma tun yana neman auren matarsa ta fari zai ta yi mata zaƙin bakin ba shi ba yi mata kishiya. Kai da ba ka san me Allah ya shirya maka ba a rayuwa. Ba ka san me zai faru a gaba ba.…
Read More