Matashin da ya cinna wa masallata wuta a Kano ya amsa laifinsa

Kotu

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

Matashin da ya banka wa masu sallah a Masallaci wuta a jihar Kano, ya amsa laifin da ake tuhumarsa da aikatawa a gaban kotu.

Mutumin mai shekara 39 wanda ya gurfana a gaban wata kotun shari’ar Musulunci da ke birnin na Kano, inda aka tuhume shi da laifuka uku, ya ce ya amince da tuhume-tuhumen da aka karanta masa.

A ranar Laraba 15 ga watan Mayu ne matashin ya cinna wuta a wani masallaci da ke ƙaramar hukumar Gezawa ta jihar Kano, daidai lokacin da ake ibada.

Yanzu haka mutanen da suka rasa rayukansu sanadiyyar wutar sun kai 17, yayin da wasu mutum 12 ke kwance a asibiti.

Kotun ta ɗage sauraron shari’ar zuwa 31 ga Mayu domin bai wa wanda ake zargi damar samun lauya, sannan masu gabatar da ƙara su samu damar tattara shaidu.