Masarautar Burumawa (1)

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

A yau Manhaja za ta duba irin gwagwarmayar da ’ya’yan kabilar Burumawa suka yi wajen kafa masarautarsu a Jihar Filato.

Burumawa, ƙabila ce wacce ta fi yawa a Ƙaramar Hukumar Kanam da ke Jihar Filato, yawanta ya kai kashi 80 cikin 100 na jama’ar ƙaramar hukumar. Haka kuma ana samun su a Ƙaramar Hukumar Wase, inda a can yawansu ya kai kashi 40 cikin 100 na jama’ar ƙaramar hukumar.

Sannan ana samun su a garuruwan qananan hukumomin Lantang da Shendem da Kua’an-Pan da sauransu a Jihar Filato da wasu yankunan Tsakiyar Nijeriya kamar Wukari a Jihar Taraba da sauransu.

Asalin sunan wannan ƙabila shi ne Bogghom, kuma ana ambatonta da mabambantan sunaye a tsakanin sauran ƙabilu. Hausawa ne suka kira su da Burum, wanda shi ne sunan da ya fi karɓuwa kuma ya danne saura. Saboda haka sai ƙabilar ta fi shahara da sunan Burumawa.

Kafuwa:

Wani maharbi mai suna Nimmam, ɗan asalin garin Zinn, wacce a yanzu take Ƙaramar Hukumar Lantang ta Arewa, shi ya kafa garin. Tun farko mahaifan Nimman sun tashi daga garinsu na asali mai suna Tal, wanda a yanzu yake Ƙaramar Hukumar Pankshin a jihar, suka koma Zinn da zama, inda suka haifi Nimman da sauran ’yan uwansa a garin.

Bayan Nimmam ya girma, sai ya riqi harbi a matsayin sana’arsa. A cikin irin yawace-yawancensa na harbi ne Allah Ya kai shi wani dutse wanda ya ga cewa dutsen ya yi masa daidai da rayuwa a wurin saboda akwai namun daji a wurin. Sai ya share waje ya zauna a kan dutsen shi da iyalansa.

Sannu a hankali, Nimman ya riqa kashe dabbobin daji yana ci tare da iyalansa sannan yana adanawa. Kasancewar wannan dutse mai tsawon da ake iya hango shi daga garuruwan nesa musamman da daddare idan sun kunna wuta domin ganin haske, sai jama’a suka fara zuwa kan dutsen domin ganin abin da ke gudana ko wanda ke raye a wurin.

Nimman, mutum ne mai karvar baƙi, saboda haka duk mutanen da suka zo, sai ya ɗebo nama daga cikin irin wanda yake adanawa ya ba su. Waɗansu idan suka karɓa, sai su yi godiya su qara gaba, wadansu kuma su share wuri su zauna tare da iyalansu, sun samu wurin rayuwa. A kwana a tashi dutsen ya zama gari. Saboda haka sai aka riƙa kiran wannan dutse da Dutsen Nimmam.

Suna:

Jama’ar da suka riƙa zuwa ƙungiya-ƙungiya suna zama a kan wannan dutse tare da Nimmam, sai furta sunansa ya wuyata ga wasu ƙabilun suka riƙa kiransa da Namwang. Da Hausawa suka yawaita a garin, bayan Jihadin Shehu Ɗan Fodiyo, su ma furta kalmar ta yi nauyi a bakinsu. Saboda haka sai suka riƙa kiran garin da Namaran ka-tsaye, inda daga bisani da Turawa suka zo suka karve shi yadda Bahaushe yake furtawa. Saboda haka sai wannan suna ya zama shi ne sunan wannan gari a hukumance.

Bigire:

Garin Namaran yana nan a Kudu maso Yamma da garin Kanam, ya yi iyaka da Ƙaramar Hukumar Lantang ta Arewa a Kudu maso Yamma. Sannan ya yi iyaka da Ƙaramar Hukumar Wase a Kudu maso Gabas.

Yunƙurin danne ’yanci da binne tarihin Burmawa daga ɓangaren Sarkin Kanam, Alhaji Muhammadu Ibrahim, shi ne abin da ya qyasta ashanar hura wutar wannan fafutika ta neman kafa Masarautar Burum (Masarautar Bogghom), wacce ta fara daga 1982.

An ɗauki tsawon shekara 35 (1982-2017), ana varje gumi tsakanin ɓangarorin biyu; sarakunan Kanam da kuma Burmawa, ta hanyar amfani da ƙarfin faɗa-a-ji da baje kolin hujjoji da kowane ɗaya daga cikinsu yake da su.

Wannan fafutika ta riqa sauya salo daga wannan mataki zuwa wancan tsakanin ɓangarorin biyu, ta yadda a wani lokaci har sai da ta kai ga raunata waɗansu aka samu salwantar rayukan waɗansu da kuma varnata dukiya.

Gwamnan Jihar Filato, Solomon Baqo Lalong, shi ya samu nasarar kawo ƙarshen wannan balahira a tsakanin masarautun Kanam da Burumawa, bayan abin ya faskari gwamnonin da suka gabace shi ciki har da sojoji.

Masomi

Shirye-shiryen bikin tabbatar da ɗaukaka daraja da Mai martaba Sarkin Kanam, Alhaji Muhammadu Ibrahim, OFR ya samu daga Sarki Mai Daraja ta Biyu zuwa Mai Daraja ta Daya a 1982, shi ne masomin wannan fafutika.

Sarkin Kanam Alhaji Muhammadu Ibrahim, ya fito ne daga zuriyar Kh’n Nang, wacce Turawa suka jirkita ta koma Kanam. Wannan zuriya tushenta shi ne wani mutum mai suna Muhammadu Maki, wanda shi kuma asalinsa mutumin Kano ne.

Muhammadu Maki da jama’arsa sun je, sun samu Nimman a Dutsen Nimwang; wanda yanzu ya zama garin Namaran, suka zauna tare da shi. Domin a bambance zuriyar Muhammadu Maki da sauran haulolin da ya tarar a wurin, sai aka riƙa kiransu da Kh’n Nang, wacce ke da ma’ana ta “Daga Arewa,” ko kuma a ce “Mutanen Arewa,” saboda daga Arewa suka fito. Sunan ya jirkice daga Kh’n Nang ya koma Kanam.

Da aka zo shirye-shiryen bikin ƙarin girma da Sarkin Kanam ya samu, sai ya rubuta cewa dukkan jama’ar Burumawa da ke wannan yanki daga Kano suka je wurin, a jikin ajandar taro. Kasancewar, daga cikin manyan baƙin da ya gayyata domin halartar wannan biki nasa akwai marigayi Mai martaba Sarkin Kano, Alhaji Ado Bayero. Sannan ya sauya sunan sarautarsa zuwa Emir, wanda masaratun Daular Usmaniyya ke amfani da shi, waccan gaɓa ta alaƙanta sauran Burumawa da Kano, ta jirkita tarihin Burumawa baki ɗaya, saboda shi Nimman wanda ya kafa garin Namaran, daga Zinn ya ƙaura zuwa wannan dutse a yawonsa na harbi, ya zauna a wurin, sannu a hankali jama’a suna zuwa suna samunsa har wurin ya zama gari.

Saboda haka, ba tare da jinkiri ba, waɗansu daga cikin mambobin wannan kwamitin shirye-shiryen suka ƙalubalanci mayar da su Kanawa a tarihance. Dole aka sauya wannan ajandar taro da ta kore dukkan sauran haulolin Burmawa da dangantakar tarihi da Kano in ban da tsurar su haular Kanam ɗin. Wannan cece-ku-ce ya faru a cikin watan Fabrairun 1983. Shi kuma bikin an gudanar a shi a ranar 9 ga Afrilun shekarar.

Shelar bore:

Bayan cin zarafin da aka yi wa Burumawa a yunƙurinsu na gudanar da bikin raya al’adunsu, sai suka yi wata ganawa a garin Fyel, cikin tsananin sirri a ranar 12 ga watan Afrilun 1986, saboda dukkan mahalarta taron, suna cikin hilar jami’an tsaron Ƙaramar Hukumar Kanam. Taron, ya samu halatar duk wani mai faɗa-a-ji ɗan ƙabilar Burum. A wannan taro aka yanke shawarar cewa:

Dole a ɗauki matakin dakatar da duk wani cin zarafin Burumawa da ake yi, a shari’ance.

Al’ummar Burumawa ta yanke duk wata dangantakar sarauta da Masarautar Kanam. Sannan dole a sanar da gwamnatin jiha game da wannan ci gaba ta hannun Shugaban Ƙaramar Hukumar Kanam.

Burumawa su samu wata kafa ta sanar da duniya halin da suke ciki, tare da nuna rashin amincewarsu da duk wani tsoma baki da Masarautar Kanam za ta yi a cikin harkokin Burumawa.