Shugaban ƙasa, talakawa na maka godiya

Tare da ABBA ABUBAKAR YAKUBU

’Yan Nijeriya sun cika da farinciki da jin daɗi sakamakon amincewar da Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi na dakatar da batun fara cire harajin Yaƙi da Zamba ta Intanet daga kowacce hadahadar kuɗi da ’yan Nijeriya suka yi a wayoyinsu ko kuma ta na’urar sadarwa, wanda Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya sanar da cewa za a fara cirewa a mako mai zuwa.

Rahotanni sun bayyana cewa, shugaban ƙasa ya sanar da dakatar da shirin na CBN ne biyo bayan kiraye-kiraye da ƙorafe-ƙorafe daga sassan ƙasar nan kan illar da hakan zai yi a rayuwar talakawan Nijeriya. An ce shugaban ya koka kan yadda aka kawo tsarin a daidai lokacin da ‘yan ƙasa ke cikin wani irin yanayi na ƙuncin rayuwa. Don haka ya nuna damuwa sosai ga halin da ‘yan ƙasar ke ciki da jaddada cewa ba zai bari a ƙara musu wata wahala ba!

Ba sabon labari ba ne, jin cewa tun bayan da aka rantsar da gwamnatin shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu a ranar 29 ga watan Mayu na shekarar 2023 a matsayin shugaban Nijeriya na 16, kuma zaɓaɓɓen shugaban ƙasa na biyar a ƙarƙashin zangon dimukraɗiyya na huɗu, ’yan Nijeriya ke ta bayyana damuwa kan salon mulkinsa da irin matakan da gwamnatinsa ke ɗauka na farfaɗo da darajar tattalin arzikin ƙasa. Kamar yadda muka sani ne, shugaba Tinubu ya karvi ragamar jagorancin ƙasar nan ne a wani mawuyacin yanayi, sakamakon yadda tsare-tsaren gwamnatin da ya gada ta tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ta riƙa ɗauka a can baya.

Tun a jawabinsa na farko, bayan an rantsar da shi a matsayin shugaban ƙasa, Bola Tinubu ya sanar da janye tallafin da gwamnatin tarayya ta saba bayarwa don shigo da tataccen man fetur cikin ƙasa, abinda ’yan Nijeriya suka riƙa yi wa kallon gwamnatinsa da ta shigo da taken sauya yanayin rayuwar ’yan ƙasa da bai wa talaka damar ya sarara, ba ta shigo da ƙafar dama ba.

Domin kuwa halin ƙunci da tsadar rayuwa da suka fuskanta a ƙarƙashin gwamnatin baya wanda kuma suke ganin za a samu canjinsa a wannan gwamnati, ya haifar da tsoro da fargaba kan halin da tattalin arzikin Nijeriya zai ƙara samun kansa a ciki. A dalilin haka rayuwa ta canzawa ’yan Nijeriya ba kaɗan ba, har ta kai ga wasu ’yan ƙasa suka fara zanga-zangar lumana ta nuna wa gwamnati damuwarsu kan halin da aka shiga.

Kodayake za mu iya cewa, gwamnati ta yi rawar gani wajen ɗaukar matakan gaggawa don ganin an shawo kan waɗannan matsaloli ta hanyar samar da tallafin sauƙaƙa raɗaɗin talauci da tsadar rayuwa, ta hanyar rabon kayan abinci, da jari ga ’yan kasuwa masu ƙananan sana’o’i, har ma kuma da samar da tsarin sufuri mai rahusa ga matafiya, ma’aikatan gwamnati da sauran ‘yan ƙasa.

Har wa yau kuma gwamnati ta yi ƙoƙari wajen tabbatar da ganin an sauke farashin Dala a kasuwannin sayar da kuɗaɗen ƙasashen waje na bayan fage, sakamakon tsauraran matakan da Babban Bankin Nijeriya ya ɗauka. Hakan da aka yi ya taimaka ainun wajen rage raɗaɗin da ake fuskanta a wasu ɓangarorin rayuwa.

Bincike ya tabbatar da cewa, kimanin Naira Tiriliyan 4.1 ne gwamnatin Nijeriya ta ce ta fitar don samar wa ’yan Nijeriya Miliyan 50 tallafin rage raɗaɗin talauci, sakamakon cire tallafin man fetur. Wannan ya haɗa har da tallafin Naira Biliyan 200 da aka raba wa manyan masu masana’antu 75 don sassauta farashin kayan da suke sarrafawa, da bashin Naira Biliyan 75 da aka rabawa qananan masu masana’antu, da kuma tallafin Naira Biliyan 50 da aka ce an raba wa ’yan Nijeriya masu neman ƙananan jari don yin sana’o’in dogaro da kai.

Ko ba komai dai ba zai yiwu a ce gwamnati ta yi kunnen uwar shegu ga koke-koken talakawanta ba. Ko da kuwa ba kowanne ɗan Nijeriya ne ya amfana da tallafin ba, wanda dama a bayyane yake ba kowa zai samu ba, sai waɗanda aka tsara bai wa tallafin, saboda kasancewarsu mabuƙata na musamman, masu masana’antu da ’yan kasuwa.

A daidai lokacin da ake wannan dambarwa ta tsadar rayuwa da hauhawar farashin kayayyakin masarufi a ƙasar nan, sai gashi kuma gwamnatin tarayya ta sanar da cire tallafin da take bai wa ɓangaren wutar lantarki. A wata sanarwa da Ministan Kula da Ma’aikatar Lantarki Adebayo Adelabu ya fitar, inda ya sanar da cewa Nijeriya ba za ta iya cigaba da biyan tallafi a kan wutar lantarki ba saboda tarin basussukan da kamfanonin samar da lantarki ke bin gwamnati.

A cewarsa, basussukan da kamfanonin wuta da masu samar da iskar gas ke bin gwamnati sun zarce Naira Tiriliyan uku. Don haka ɗaukar matakin ya zama dole domin gwamnati ta samu damar magance basusssukan da ke kanta waɗanda ke ƙaruwa.

Biyo bayan wannan sanarwa ne, sai Hukumar da ke Kula da Wutar Lantarki ta Nijeriya ta ce ta ƙara kuɗin wutar ga abokanan hulɗarsu da ke ajin Band A – masu samun wuta tsawon sa’a 20 a rana. Mataimakin shugaban Hukumar, Musliu Oseni ya bayyana cewa masu amfani da wutar lantarki za su biya Naira 225 a kowacce sa’a ɗaya a maimakon yadda a baya suke biyan Naira 66. Sannan ya ce, waɗanda ke samun wuta tsawon sa’a 20 a kowacce rana su ne kashi 15 cikin 100 na kwastamomin hukumar.

’Yan Nijeriya da dama ba su ji daɗin wannan ƙarin kuɗin wutar lantarki ba, domin kuwa hakan na nufin ƙarin farashi ne kan duk wani abu da ake sarrafa shi da wutar lantarki, har ma da wanda bai shafi lantarki ba. Hakan ƙarin damuwa ne kan wacce ake ciki na tun bayan janye tallafin man fetur.

Sai dai kamar wannan bai isa ba sai ga shi kuma Babban Bankin Nijeriya ya fitar da wata sanarwa ta cire sabon harajin yaƙi da zamba ta Intanet. Babban Bankin dai ya umarci sauran bankuna ne da su fara cire harajin kaso 0.5 a kan duk wata hulɗar tura kuɗi ta waya ko Intanet da za a yi. Wannan na zuwa ne biyo bayan kafa Dokar Yaƙi da Hana Sata ta Intanet ta Shekarar 2024 da Shugaban Ƙasa ya sanyawa.

Sabon harajin ya zo ne ’yan kwanaki bayan bankunan kasuwanci sun dawo da biyan haraji a kan kuɗi masu yawa da aka kai ajiya a banki daga ɗaiɗaikun mutane da ƙungiyoyi ko kamfanoni. Waɗannan kuɗaɗe da ake cirewa kaso biyu da kaso uku ne a kan ajiyar da ta kai Naira dubu 500 a asusun ɗaiɗaikun mutane, da miliyan 3 a asusun ƙungiyoyi ko kamfanoni an dakatar da shi tsawon wata shida kafin a dawo da shi. Wannan ƙari ne a kan sauran kuɗaɗen da ake cirewa a harkokin kuɗi a bankuna kamar harajin tura kuɗi ta waya ko Intanet (EMTL) da kuɗin da ake cira kan aika saƙon waya (SMS) da sauransu.

Kuɗin EMTL da ake cira wa shi ne Naira 50 idan aka tura ta Intanet ko aka karva yayin tura kuɗi a bankin kasuwanci ko cibiyar kuɗi ko ma kowanne asusu da kuɗin ya kai Naira 10,000 zuwa sama. Sai dai Bankin CBN ya umarci bankunan kasuwancin su dakatar da cirar kuɗi a kuɗin da aka kai ajiyewa har zuwa ranar 30 ga Satumban 2024.

Biyo bayan ƙorafe-ƙorafe da wasu ’yan Nijeriya suka yi ne irin su ƙungiyar Kare ’Yancin Rayuwa da Tattalin Arziki da Tabbatar da Amana ta (SERAP), ƙungiyar Ƙwadago ta NLC, da wasu masu faɗɗa a ji a harkar tattalin arziki da walwalar jama’a game da halin da ’yan Nijeriya za su iya sake shiga idan har aka fara cire wannan haraji, shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da a dakatar da wannan batu.

Babu shakka wannan mataki da shugaban ƙasa ya ɗauka babban abin a yaba ne sosai, kasancewar sa mai jin koken talakawansa da bin shawarar ƙwararru na kusa da shi. Muna fatan gwamnatin tarayya, musamman Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu za ta cigaba da kasa kunne tana sauraron koke-koken jama’ar ƙasa, tana auna irin matsalolin da talakawan da suka zaɓe ta za su shiga idan aka aiwatar da wani tsari ko wata doka.