Da Ɗumi-ɗumi: Gobara a sakatariyar gwamnatin Kaduna

Bayanan da muka samu yanzu-yanzu daga Jihar Kaduna sun ce, an samu aukuwar gobara a sakatariyar gwamnatin jihar, lamarin da ya yi sanadaiyar ƙonewar wasu ofisoshi.

Wani ganau, Malam Ibrahim Mohammed, wanda ma’aika gwamnatin jihar ne, ya ce iftila’in ya auku ne da misalin ƙarfe 2:30 na rana wannan Larabar.

Ya ce duk da dai ba a kai ga gano musababbin gobarar ba, amma ana zargin hakan ba ya rasa nasaba da wutar lantarki.

Ya ƙara da cewa, ba a samu asarar rai ba, amma muhimman kayayyaki da dama sun ƙone ƙurmus.

Ya zuwa haɗa wannan labari, babu wani ƙarin haske kan batun daga ɓangaren gwamnati.