Editor

9513 Posts
Majalisar Dokokin Kano ta kama hanyar yi wa Dokar Masarauta kwaskwarima

Majalisar Dokokin Kano ta kama hanyar yi wa Dokar Masarauta kwaskwarima

Majalisar Dokokin Jihar Kano ta kama hanyar yi wa Dokar Masarautu kwaskwarima bayan shan kiraye-kiraye kan a dawo da Sarkin Kano na 14, Muhammad Sanusi, wanda tsohuwar gwamnatin Umar Ganduje ta tsige. Majalisar ta yanke shawarar yi wa dokar kwaskwarima ne bayan da Shugaban Masu Rinjaye, Hussien Dala, mai wakiltar Mazaɓar Dala, ya miƙa ƙorafinsa yayin zaman majalisar a ranar Talata. An fara yi wa wannan doka kwaskwarima ne a 2019 bayan da ruwa ya yi tsami tsakanin gwamnan jihar na wancan loakci, Abdullahi Umar Ganduje da Sarkin Kano na 14, Sunusi. Sakamakon gayaran da aka yi wa dokar a…
Read More
Kotu ta hana kama jaruma Mansura Isa kan zargin cin zarafi

Kotu ta hana kama jaruma Mansura Isa kan zargin cin zarafi

Daga AISHA ASAS Fitacciyar jarumar finafinan Kannywood Mansura Isah ta kai qarar Hukumar Hisbah ta Kano da kwamishinan ‘yan sandan Kano, inda ta shigar da ƙara a Babbar Kotun Tarayya da ke jihar. Mansura wadda ta samu wakilcin lauyanta Barista Ibrahim Abdullahi Chedi, ya ce, ƙarar Mansura ta zo ne a matsayin mayar da martani kan zargin da ake mata na cin zarafin wata ƙaramar yarinya a wata makarantar firamare da ke jihar ta Kano, wanda ta bayyana ta dandalinta na sada zumunta, inda ta yi kira don gwamnati ta shiga tsakani. Sai dai gwamnatin Jihar Kano, ta bakin Kwamishinan…
Read More
‘Yan bindiga sun kashe sama da mutum 40 a Filato

‘Yan bindiga sun kashe sama da mutum 40 a Filato

Bayanan da suka iso mana yanzu daga jihar Filato sun ce, 'yan bindiga sun kai ƙazamin hari ƙauyen Zurak da ke Gundumar Bashar District cikin ƙaramar hukumar Wase, Jihar Filato, inda suka kashe sama da mutum 40. A cewar mazauna yankin lamarin ya faru ne ranar Litinin da misalin karfe 5 na yamma yayin da jama'a ke gudanar da harkokinsu. Sun ƙara da cewa, ba su samau damar sanar da abin da ya auku d wuri ba ne sakamakon rashin kyawun sabis a yankin. Wani shugaban matasan yankin mai suna Sahpi’i Sambo, ya tabbatar da aukuwar harin ga jaridar Daily…
Read More
Ku yi amfani da finafinaku wurin haɓaka zaman lafiya da haɗin kai, Sanata Barau ga Kannywood

Ku yi amfani da finafinaku wurin haɓaka zaman lafiya da haɗin kai, Sanata Barau ga Kannywood

Daga AISHA ASAS Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau I. Jibrin, ya buqaci ‘yan wasan kwaikwayo a masana’antar nishadantarwa ta Kannywood da su yi amfani da finafinansu wajen tallafa wa ƙoƙarin Gwamnatin Tarayya na magance matsalar ‘yan fashi da garkuwa da mutane da sauran ƙalubalen da ke addabar ƙasar nan. Sanata Barau ya yi wannan kiran ne a lokacin da ya karvi bakuncin shugabannin ƙungiyar jaruman Kannywood a ofishinsa da ke harabar Majalisar Dokokin Ƙasa da ke Abuja. A wata sanarwa da mai ba shi shawara na musamman kan harkokin yaɗa labarai Ismail Mudashir ya fitar, Sanata Barau ya jaddada…
Read More
Ni ke zuwa ta ƙarshe a duk lokacin da aka yi jarrabawa a makaranta, cewar jaruma Toke Makinwa

Ni ke zuwa ta ƙarshe a duk lokacin da aka yi jarrabawa a makaranta, cewar jaruma Toke Makinwa

Daga AISHA ASAS Shararriyar jaruma kuma sananniyar ‘yar soshiyal midiya, Toke Makinwa ta bayyana kanta amatsayin wadda ba ta bar abin a yaba ba alokacin da take makaranta. Jarumar ta bayyana cewa, a cikin ɗalibai 52, ita ke zuwa ta karshe a duk lokacin da aka yi jarrabawa. Toke ta bayyana wannan ɓoyayen lamari game da rayuwarta wanda ba kasafai mutane ke iya faɗar rashin ƙoƙarin da suka yi a makaranta ba, asalima ire-iren waɗannan mutane sun fi ɓoye wannan ɓangare na rayuwarsu musamman ma ga ‘ya’yansu. A cewar jarumar, “A kullum aka yi jarrabawa ni ke rufe aji, a…
Read More
Zamfara: Gwamna Lawal ya ƙaddamar da shirin rabon tallafin kayan masarufi ga mabuƙata

Zamfara: Gwamna Lawal ya ƙaddamar da shirin rabon tallafin kayan masarufi ga mabuƙata

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya ƙaddamar da shirin raba tallafin kayayyakin masarufi ga mabuƙata a jihar. Mai magana da yawun Gwamna, Bala Sulaiman ya ce, bikin ƙaddamarwar ya gudana ne ranar Litinin a ofishin Kwamishinar Jinƙai da ke Gusau, babbn birnin jihar. Sanarwar da Sulaimanya rattaɓa wa hannu ta ce, Hukumar ba da Agajin Gaggawa ta Ƙasa (NEMA), ta miƙa wa Gwamnatin Jihar kayayyakin masurufi da dama don raba wa marasa galihu a jihar. A cewar sanarwar, Daraktan NEMA na shiyyar Arewa maso-Yamma, Dr. Ishaya Chonoko, shi ne ya wakilci Shugabar NEMA ta ƙasa, Hajiya Zubaida Umar, a wajen…
Read More
An naɗa Shugaban Ƙasa na riƙon-ƙwarya a Iran

An naɗa Shugaban Ƙasa na riƙon-ƙwarya a Iran

Jigon ƙasar Iran, Ayatollah Ali Khamenei, ya naɗa Mataimakin Shugaban Ƙasar, Mohammad Mokhber, a matsayin mai riƙon ƙwaryar shugabancin ƙasar biyo bayan mutuwar Shugaba Ebrahim Raisi, wanda ya cimma ajali a hatsarin jirgin sama. An jiwo jigon na cewa, “Bisa la'akari da Doka ta 131 ta kundin tsarin mulkin ƙasar, yanzu Mokhber shi ne jagoran ɓangaren zartarwa." Khamenei ya bayyana haka ne a sanarwar da ya fitar, inda ya ce Mokhber na buƙatar yin aiki tare da shugabannin ɓangaren doka da shari'a domin shirye-shiryen zaɓen shugaban ƙasa a cikin wa'adin kwana 50.
Read More
Zama da kishiya

Zama da kishiya

Daga SA'ADATU SAMINU KANKIA MANHAJA: Wacce shawara za ki ba wa matan da mazajensu ke shirin ƙara aure? Shawarata ga mata da mazansu ke shirin ƙara aure shi ne, su yi haƙuri, kuma su sanya a ransu ba don mijinsu baya sonsu ba ne za ya ƙara aure, kowa da irin ƙaddarar rayuwarshi. Abu na gaba da mace zata yi shi ne ta dage da addu'a, akan samun zaman lafiya a gidansu, ta natsu ta fahimci mijinta, sannan ta kauce ma sauraren maganganun mutane, saboda wani lokaci su ne ke hana zaman lafiya. Haka nan ta kame kanta kada ta…
Read More
MOPPAN ta kafa muhimman kwamitoci biyu

MOPPAN ta kafa muhimman kwamitoci biyu

A ƙoƙarin da take yi na ci gaba da ingata harkokinta, Ƙungiyar Masu Shirya Finafinai ta Nijeriya (MOPPAN), ta kafa muhimman kwamitoci guda biyu. Ƙungiyar ta kafa Kwamitin Ladabtarwa da ayyuka na MOPPAN/Kannywood mai mabobin 14 domin ci gaba da tsaftace ayyukan masana'atar finafinai. Sai kuma kwamitin tara kuɗi da kai ziyara, shi ma mai mambobi 14. Ƙungiyar ta bayyana haka ne a cikin sanarwar manema labarai da ta fitar mai ɗauke da sa hannun Sakatare na Ƙasa, Al-Amin Ciroma. Sanar ta ce an ƙalubalanci 'yan kwamitin da su yi aiki daidai da tanadin dokokin MOPPAN. Shugabam MOPPAN na ƙasa,…
Read More
Isra’ila ta aukawa Rafah

Isra’ila ta aukawa Rafah

Tare da NASIRU ADAMU In dai Isra'ila ta ce za ta kai hari to a jira lokaci sai ta kai ko da kuwa hakan zai yi sanadiyyar mutuwar waɗanda ba su da laifin komai. Kazalika ƙasar ta Yahudawa da ta mamaye ƙasar Falastinawa kan samu goyon baya ne na kai tsaye ko ta bayan fage daga manyan ƙasashe musamman na yammancin duniya. Isra'ila kan iya aibata hukuncin kotun duniya kuma ta kwana lafiya. Haqiqa akwai wasu ƙasashe da in sun gwada kaɗan daga ɗabi'un Isra'ila za su iya fuskantar wariya da ma kai yaqin ƙasashe na taron dangi. A ɓangaren…
Read More