20
May
Ƙungiyar Masu Shirya Finafinai ta Nijeriya (MOPPAN), ƙarƙashin jagorancin Alhaji Habibu Barde, ta miƙa saƙon taya murna da fatan alheri ga Alhaji Ismail Mohammed Na'Abba da aka fi sani da Afakallah. MOPPAN ta taya Afakallah murna ne bisa naɗin da aka yi masa na zama ɗaya daga cikin mambobin Hukumar Gudanarwa na Jami’ar Fasaha ta Jihar Jigawa. Bayanin hakan na ƙunshe ne cikin sanarwar da ƙungiyar ta fitar mai ɗauke da kwanan wata 19/5/2024 da kuma sa hannun sakatarenta na ƙassa, Al-Amin Ciroma. Ƙungiyar ta ce Afakallah na ɗaya daga cikin zaƙaƙuran mutanen da suka bunƙasa masa’antar shirya finafinan Hausa…
