18
May
Daga WAKILINMU Gwamnonin yankin Arewa maso Yamma na Nijeriya sun yi taro tare da tawagar Majalisar Ɗinkin Duniya, ƙarƙashin jagorancin mai kula da harkokin jinƙai, Mohamed Malick Fall, a Abuja ranar Juma'a. Manufar taron dai ita ce neman tallafi don tunkarar babban ƙalubalen ci gaban yankin. Taron wanda Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin Arewa Maso Yamma kuma Gwamnan Jihar Katsina Malam Dikko Umaru Radda ya jagoranta, ya samu halartar gwamnan Jihar Kaduna Sanata Uba Sani, Injiniya Abba Kabir Yusuf na Kano, Mallam Umar Namadi na Jigawa; Mataimakin Gwamnan Sokoto, Alhaji Idris Muhammad Gobir, da Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal. Taron wanda aka…
