17
May
Daga MAHDI M. MUHAMMAD Ministar Harkokin mata, Uju Kennedy-Ohanenye, ta kai ƙarar Babban Sufeto Janar ’Yan Sandan Nijeriya, Kayode Egbetokun, tare da neman kotu ta dakatar da Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Neja, Abdulmalik Sarkindaji daga aurar ’yan mata marayu 100 a yankin jihar. Amma kakakin ya caccaki ministar saboda "ta wuce gona da iri," yayin da ya sanar da cewa an soke bikin da aka shirya. Matakin da Kennedy-Ohanenye ta bayyana a wani taron ƙara wa juna sani da aka yi a Abuja, wani martani ne ga sanarwar da Sarkindaji ya yi a baya-bayan nan na cewa za a ɗaura…
