Editor

9513 Posts
Kano: Hisbah ta kama maza da mata 20 suna wanka tare

Kano: Hisbah ta kama maza da mata 20 suna wanka tare

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta ce ta kama wasu mutum 20 da suka haɗa da maza da mata bisa laifin yin wanka tare. Jami’an Hukumar ɓangaren ‘Operation Kau Da Baɗala’ sun kama su ne a wani wurin shaƙatawa da ke kan titin Ring Road sakamakon ƙorafin da mazauna yankin suka yi. Mataimakin babban kwamandan hukumar, Dakta Mujahidin Aminuddin Abubakar, ya ce laifin ya sab'ɓa wa dokar Hisbah domin ta hana haɗa jinsin biyu a cikin ruwa domin yin wanka. Ya nuna damuwarsa kan lamarin, wanda a cewarsa, za a iya maye gurbinsa da wani…
Read More
‘Yan Sandan a Kano sun cika hannu da wanda ake zargi da cinna wa masallata wuta a masallaci

‘Yan Sandan a Kano sun cika hannu da wanda ake zargi da cinna wa masallata wuta a masallaci

*Ba na badamar abin da na aikata - Wanda ake zargi Daga Rabiu Sanusi Rundunar 'Yan Sandan jihar Kano ƙarkƙashin jagorancin CP Muhammad Usaini Gumel, ta damƙe matashi Shafi'u Abubakar bisa zargin ƙona mutane a Masallaci. Matashin wanda ke zaune a ƙauyen Gadan dake ƙaramar hukumar Gezawar jihar Kano, ya faɗa komar hukumar ne bisa aikata laifin cinna wa wasu masallata wuta a yayin da suke sallar Asubahi. Rundunar ta ce yayin da suka samu kiran waya daga mabambantan mutane cewa akwai matsala a wannan yankin, wanda babu ɓata lokaci Kwamishinan 'Yan Sandan ya bada umarni ga dakarun dake kula…
Read More
Yanzu-yanzu: Emefiele ya sake ƙin amincewa da tuhumar EFCC a kotu

Yanzu-yanzu: Emefiele ya sake ƙin amincewa da tuhumar EFCC a kotu

Hukumar yaƙi da rashawa ta (EFCC), ta sake gurfanar da tsohon Shugaban Babban Bakin Nijeriya (CBN), Godwin Emefiele a kotu bisa zargin ba da damar buga Naira miliyan 684.5 a kan Naira biliyan 18.96 da sauransu. Da yake jawabi a gaban Alƙali Maryann Anenihna Babbar Kotun Abuja, Emefiele ya ce sam bai yarda da zarge-zarge huɗun da EFCC ke tuhumarsa ba. EFCC ta yi zargi Emefiele ya saɓa wa doka da gangar da nufin yi wa al’umma illa a lokacin da ya aiwatar da canjin kuɗi a matsayinsa na Shugaban CBN a tsohuwar gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari. Haka nan, hukumar…
Read More
UTME 2024: JAMB ta saki ƙarin sakamako 36,540

UTME 2024: JAMB ta saki ƙarin sakamako 36,540

Hukumar shirya jarrabawar neman gurbin karatu a manyan makarantu (JAMB), ta saki ƙarin sakamako 36,540 na jarrabawar UTME da aka rubuta kwanan baya. Ƙarin sakamakon ɓangare ne na sakamakon da hukumar ta riƙe don gudanar da bincike kan zargin tafka maguɗin jarrabawa. Zuwa yanzu, adadin sakamakon UTME na ba bana da hukumar ta fitar, ya kama 1,879,437. JAMB ta bayyana haka ne cikin sanarwar da ta fitar a ranar Talata ta bakin Kakakinta, Fabian Benjamin. Sanarwar ta ƙaryata rahoton da aka yaɗa a soshiyal midiya kan cewa, hukumar za ta sake shirya jarrabawar sakamon wai an yi mata kutse ta…
Read More
In Sha’Allah sai Allah Ya kunyata fasiƙan cikinmu kuma ya shirye su

In Sha’Allah sai Allah Ya kunyata fasiƙan cikinmu kuma ya shirye su

Daga MUSTAFA KABIR SORON ƊINKI Allahu Akbar! Gaskiya idan ni ne Malam Aminu Ibrahim Daurawa sai na sheƙa kuka saboda farin ciki. Tunda abun ya faru a game da shi a kan sha'anin na shiga cikin "Opinion poll". Gaskiya Allah bai bar Shaiɗan ya yi galaba a kan mutanen Kano da soyayyar wani abu wanda ya fi addininsa ba. Ban ji daɗin abun da ya faru tsakanin Malam da Gwamnan Kano ba. Amma kuma na yi farin ciki yadda na ga mutane cikakkun 'yan kwankwasiyya suna bayyana damuwarsu ƙarara a kan haka. Idan na ce mutane, ba fa ina nufin…
Read More
Matsalolin haƙora da yadda za a magance su

Matsalolin haƙora da yadda za a magance su

Daga AISHA ASAS Ciwon haƙora na ɗaya daga cikin curuta mafi ɗaukar hankalin mai tare da su, kuma ciwon ya zama ruwan dare a tsakanin mutane, wataƙila hakan ba ya rasa alaƙa da rashin sanin hanyoyin da ke iya haddasa matsala a haƙoran namu na daga hanyoyin kula da su. Akwai ɗabi'u da dama da muka maida ba komai ba, amma sukan zama silar kamuwa da wata nau'in cutar haƙora. Darasin namu na wannan sati zai karkata ne kan matsalolin da kuma yadda za a iya magance su, don haka ba za mu samu damar nutsewa cikin bayanin yadda muke…
Read More
ASUU ta yi barazanar shiga yajin aikin gama-gari

ASUU ta yi barazanar shiga yajin aikin gama-gari

Ƙungiyar Malaman Jami'o'i (ASUU), ta yi barazanar shiga yajin aiki na gama-gari domin nuna rashin jin daɗinta kan tshin samun majalisar gudanarwa a ɗaukacin Jami'o'in Gwamnatin Tarayya da ke faɗin ƙasa da sauran buƙatu. Ƙungiyar ta ce idan za a iya tunawa, a watan Mayun bara ne gwamnatin ta sauke majalisar gudanarwa na Jami'o'in, tare da cewa duk matakin da ta ɗauka dangane da hakan 'yan Nijeriya su kama gwamnati da laifi. Shugaban ASUU na ƙasa, Farfesa Emmanuel Osodeke ya yi wannan bayani yayin taron manema labarai da ya shirya a sakatariyar ASUU da ke Abuja a ranar Talata.
Read More
Ta sanadiyyar ƙawata na shiga shirin ‘Kwana 90’ – Hajiya Ƙarama

Ta sanadiyyar ƙawata na shiga shirin ‘Kwana 90’ – Hajiya Ƙarama

Daga IBRAHIM HAMISU, a Kano Saratu Abubakar da aka fi sani da Hajiya Karama, a cikin ga a cikin fim cin 'Kwana 90' ce baƙuwar shafin Nishaɗi na wannan makon. A tattaunawar ta da Ibrahim Hamisu a Kano, za ku ji tarihinta da kuma yadda aka yi ta tsunduma masana'antar Kannywood. Ku biyomu: MANHAJA: Za mu so ki gabatar mana da kanki? HAJIYA ƘARAMA: Sunana Saratu Abubakar, ni 'yar asalin Niger ce a garin Suleja, an haife ni a yankin Gauraka, na yi Primary da Secondry a nan, sannan na yi NCE a Niger State College of Education Minna, inda…
Read More
Gidauniyar CFDF ta yi wa masu ɗauke da cutar kumburin fuska 4000 tiyata kyauta — Dokta Bello

Gidauniyar CFDF ta yi wa masu ɗauke da cutar kumburin fuska 4000 tiyata kyauta — Dokta Bello

DAGA JOHN D. WADA, a LAFIYA Babban daraktan gidauniya Cleft & Facial Deformity Foundation, Dokta Saidu Bello, ya ce kawo yanzu gidauniyar ta yi wa masu fama da cutar kumburin fuska su sama da 4000 tiyata kyauta. Ya ce waɗanda suka ci gajiyar wannan shiri an zaɓo su ne daga sassan ƙasa, kuma an yi aikin cikin nasara batare da fuskantar wata matsala ba. Bello ne ya sanar da haka ne a jawabin sa a wajen taron ƙaddamar da ci gaba da aiwatar da shirin a jihar Nasarawa wanda aka gudanar a asibitin tarayya, wato Federal Medical Centre, da ke…
Read More
Jami’an tsaro sun kuɓutar da mutum 17 da ‘yan bindiga suka sace a Katsina

Jami’an tsaro sun kuɓutar da mutum 17 da ‘yan bindiga suka sace a Katsina

Daga UMAR GARBA a Katsina Rundunar haɗin gwiwar jami'an tsaro a jihar Katsina, ta samu nasarar kuɓutar da wasu fasinjoji 17 mafi yawansu maza da ‘yan ta’adda suka sace a yankin Solar General na ƙaramar hukumar Batsari dake jihar Katsina. A cewar wata majiyar soji, nasarar da aka samu ta biyo bayan kiran gaggawa da aka yi wa jami'an tsaron a ranar 11 ga Mayu, 2024, da misalin ƙarfe 12:00 na dare. Saboda haka ne, rundunar sojojin Nijeriya ta 9, tare da haɗin gwiwar rundunar ‘yan sanda a Katsina, da jami’an tsaro na al’umma, da mafarauta na musamman, da mafarauta…
Read More