Editor

9513 Posts
Gwamna Abba ya umarci a biya kuɗaɗen ’yan shara cikin gaggawa

Gwamna Abba ya umarci a biya kuɗaɗen ’yan shara cikin gaggawa

Daga RABIU SANUSI a Kano A yanayin damuwa kan cece-kuce da ake yi da kuma iƙirari na ƙin biyan kuɗaɗen alawus-alawus na masu shara, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ba da umarnin biyan ma’aikatan cikin gaggawa. Wannan na zuwa ne daidai lokacin da Gwamnan ya yi wata ganawa ta musamman da ma'aikatan kwashe sharar da shuwagabanninsu a makon nan a ɗakin taro na Coronation dake fadar gwamnati. Gwamna Abba Yusuf ya umarci ma’aikatar muhalli da kula da tsaftar muhalli (REMASAB) da ta tabbatar da biyan duk wasu kuɗaɗen alawus-alawus na masu shara da suka gada daga gwamnatin da ta gabata.…
Read More
Muna zaune lafiya da sauran ƙabilu – Ƙungiyar Mahautan Legas

Muna zaune lafiya da sauran ƙabilu – Ƙungiyar Mahautan Legas

Daga DAUDA USMAN a Legas Shugaban Haɗaɗɗiyar Ƙungiyar Mahauta a Jihar Legas, wadda ta ke zaune a Mayankar Shanu Abbatuwa a Ƙaramar Jukumar Okoba Agege da ke Legas, Alhaji Abdullahi Ahmed ya bayyana cewa, su na zaune lami lafiya tare da sauran ƙabilu mahauta masu gudanar da harkokin sana'ar fawa a Legas da kewayanta gabaɗaya. Shugaban ƙungiyar ya yi wannan tsokaci ne a ofishin ƙungiyar da ke Okoba agege jim kaɗan bayan tashi daga taron su na ƙungiyar mahautan Legas da kewayanta bakiɗaya. Wakilin Jaridar Manhaja ya tattauna da shugaban ƙungiyar a game da nasarorin da suka samu ta fannin…
Read More
Shawara ga ma’aurata

Shawara ga ma’aurata

Daga ZUWAIRA DAUDA KOLO MANHAJA: Me ya kamata mace ta yi wa mijinta yayin da ya sanar da ita zai ƙara aure? Nutsuwa da kauce wa biye wa burin zuciya hakika lokaci ne mafi ƙunci da damuwa kuma a wannan lokacin ana rasa hankali da tunani wanda idan an biye dokin zuciya sai a ga ƙarshe an yi ɓatacciya shi kuma ya yi aurensa. Abu ne da dole za a ga kishi a tare da ita, amma ba irin kishi na cin mutunci, da nuna bai isa ba. A'a kishi dai mai tsafta da zai gane tabbas ta ji ba…
Read More
Ƙungiyar Tabarakallah ta yi alƙawarin cigaba da koya wa matasa sana’o’i

Ƙungiyar Tabarakallah ta yi alƙawarin cigaba da koya wa matasa sana’o’i

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano Darakta Janar na Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kano Alhaji Lamin Baba Ɗanbaffa ya bayyana jin daɗinsa akan ƙoƙarin da ƙungiyar koyar da sana'o'i ta Tabarakallah ta ke wajen horar da matasa akan sana'o'i da cusa musu tarbiyya da inganta tsaro. Ya bayyana haka ne a wajen taron gabatar da ayyuka da ƙungiyar take da kuma yaye waɗanda suka amfana da koyon sana'o'i da aka gudanar filin makarantar Galafima. Ya ce, duk inda aka ce za a koyawa matasa sana'o'i ba ƙaramin abin alkhairi bane ƙungiya in an kafata akan alkhairi al'umma za su…
Read More
An buƙaci Hukumar Kiyaye Haɗurra ta saka matasa cikin masu aikin sa kai

An buƙaci Hukumar Kiyaye Haɗurra ta saka matasa cikin masu aikin sa kai

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Kwamitin Matasa kan Tattaunawa da wayar da kan Jama’a, ya buƙaci Hukumar Kiyaye Haɗurra ta Ƙasa (FRSC) da ta taimaka wajen kafa ’yan sa-kai ‘Road Marshals’ wanda ya ƙunshi matasa a kowace jiha ta ƙasar nan. Darakta Janar na kwamitin, Cif Obinna Nwaka ne ya yi wannan roƙo yayin wata ziyarar ban girma da ya kai wa rundunar Corps Marshal Dauda Ali-Biu a ranar Laraba a Abuja. Ya ce baya ga jawo hankalin matasa domin su zama masu hazaƙa, ƙoƙarin da ake yi zai kai ga samar da hanyoyin da za a samar da tsaro a…
Read More
Bashin tiriliyan N6: SERAP ta maka gwamnonin Nijeriya a kotu

Bashin tiriliyan N6: SERAP ta maka gwamnonin Nijeriya a kotu

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Ƙungiyar SERAP mai fafutukar yaƙi da cin hanci da rashawa a Nijeriya, ta yi ƙarin haske akan dalilan kai ƙarar gwamnonin ƙasar 36 da kuma ministan birnin tarayyar Abuja gaban kotu. Ƙungiyar ta ce ta shigar da wannan ƙara ne saboda rashin bayar da bayanai kan yadda gwamnonin jihohin Nijeriya 36 da ministan Abuja, suka kashe kuɗaɗen da suka ciyo na bashin naira tiriliyan kusan shida, da kuma sama da dala billiyan 4 da rabi, ba tare da bahasi ba. SERAP ta buƙaci kotun da ta gayyaci hukumar EFCC da ICPC domin ƙaddamar da bincike kan…
Read More
Atiku da Obi sun yi ganawar farko tun bayan shan kaye a zaɓen 2023

Atiku da Obi sun yi ganawar farko tun bayan shan kaye a zaɓen 2023

Daga BASHIR ISAH Ɗan takarar Shugaban Ƙasa na Jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar da takwaransa na Jam'iyyar Labour, Peter Obi, sun yi ganawa domin tattauna gwagwarmayar siyasarsu. Wannan dai shi ne karon farko da aka ga ƙusoshin siyasar sun gana tun bayan da suka sha kaye a hannun Bola Tinubu a babban zaɓen 2023. Atiku da ne ya tabbatar da ganawar tasu a shfinsa na X a ranar Litinin. Ganawar tasu ba ta rasa nasaba da neman haɗewa a don kafa jam'iyya wadda za su yaƙi Tinubu da ita a 2027. Idan ba a manta ba, kwanakin baya aka jiwo masanin…
Read More
Ƙarin kuɗin wuta: NLC ta jijjiga kamfanonin JEDC, YEDC

Ƙarin kuɗin wuta: NLC ta jijjiga kamfanonin JEDC, YEDC

Daga BASHIR ISAH Ƙungiyar Ƙwadago ta Ƙasa (NLC), ta rufe babban ofishin kamfanin rarraba wutar lantarki na Jos Electricity Distribution Company (JEDC) a Jihar Filato kan ƙarin kuɗin wuta. Binciken Manhaja ya gano NLC ta rufe babbar ƙofar shiga kamfanin lamarin da ya haifar wa ma'aikatan DisCo tsaiko wajen shiga ofishin. Kazalika, NLC ta girgiza kamfani rarraba wutar lantarki na Yola Electricity Distribution Company (YEDC) a Jalingo, babban birnin Jihar Taraba duk dai kan batun ƙarin kuɗin wuta. Dukkan wannan ya faru ne a ranar Litinin a ci gaba da gwagwarmayar da NLC ke yi wajen tabbatar da 'yan ƙasa…
Read More
Za a kashe wa ‘yan majalisun tarayya da na jihohi N724bn a 2024

Za a kashe wa ‘yan majalisun tarayya da na jihohi N724bn a 2024

Daga BASHIR ISAH Majalisun tarayya da na jihohi 36 a Nijeriya za su kashe kimanin Naira biliyan 724 wajen gudanar da harkokinsu a 2024 da ake ciki. Bayanai kan yanayin kuɗaɗen da za a kashe wa 'yan majalisun tarayya da na jihohin a wannan shekarar sun ce, a ɓangare albashi da alawus-alawus kaɗai kimanin Naira biliyan 50 aka ware a kasafin ƙasa. Sannan biliyan N673.94 wajen sauran harkokin majalisun na tarayya da jihohi da kuma hukumomin da ke ɗamfare da su. Yayin da za kashe biliyan N8.67 wajen biyan albashi da alawus-alawus na 'yan majalisa 109 a matakin tarayya, a…
Read More
Tinubu ya umarci CBN ya dakatar da aiwatar da harajin tsaron intanet

Tinubu ya umarci CBN ya dakatar da aiwatar da harajin tsaron intanet

Daga BASHIR ISAH Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya umarci Babban Bankin Nijeriya (CBN) da ya dakatar da aiwatar da harajin rabin kashi ɗaya (0.5%) na tsaron internet wanda ya tada ƙura a ƙasa, tare da neman a sake nazarin dokar. Idan ba a manta ba a ranar 6 ga Mayu, CBN ya fitar da sanarwa tare da umuryar bankuna da su ɗabbaƙa sabon haraji na tsaron intanet. Sabuwar dokar ta nuna za a riƙa biyan kashi 0.5 na hada-hadar kuɗaɗe ta intanet sannan a tattara a zuba a asusun Taaron Intanet ƙarƙashin kulawar Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara…
Read More