Editor

9513 Posts
Inuwa zafi, rana ƙuna

Inuwa zafi, rana ƙuna

Tare da NASIRU ADAMU EL-HIKAYA A lokacin da a ke tsananin zafi mutane kan nemi ruwa mai sanyi ko wajen mai inuwa don rage kaifin ƙalubalen yanayin. A wasu shekaru ma da idan wasu bai gama wayewa ba su kan ɗora ƙanƙara a kansu su kifa hula har ta kai ga an samu matsalar daskarewar jini da kan iya haifar da asarar rai. Abun da na ke son magana a kai wannan makon shi ne yadda tsananin zafin rana kan ƙare a kan talakawa wajen neman abinci amma ba lallai ne su samu ba don yadda rayuwa a zamanin yau…
Read More
Babban likitan Falasɗinu ya rasu a kurkukun Isra’ila

Babban likitan Falasɗinu ya rasu a kurkukun Isra’ila

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Ƙungiyoyin masu kula da fursunonin Falasɗinu sun ce wani babban likita Bafalasɗine ya mutu a gidan yarin Isra'ila bayan shafe sama da watanni huɗu yana tsare. Dr Adnan Al-Bursh, mai shekaru 50, shi ne shugaban likitoci a asibitin al-Shifa. Ma'aikatar gidan yarin Isra'ila ta tabbatar da cewa wata sanarwa da aka buga a ranar 19 ga Afrilu game da wani fursuna da aka tsare saboda dalilan tsaron ƙasa ya mutu a gidan yarin Ofer shine Dr Al-Bursh. Ba a bayar da cikakken bayani kan musabbabin mutuwar ba, kuma hukumar gidan yarin ta ce ana binciken lamarin.…
Read More
Ministocin Tinubu ne suka sa ba a ganin ƙoƙarinsa – Jimoh Ibrahim

Ministocin Tinubu ne suka sa ba a ganin ƙoƙarinsa – Jimoh Ibrahim

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Yawancin ministocin da Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya naɗa ba sa ƙoƙari a cewar Jimoh Ibrahim, Sanata mai wakiltar Ondo ta Kudu a Jam’iyyar APC. Ibrahim ya kuma ce wasu daga cikin ministocin akwai zargin cin hanci da rashawa a tare da su, yayin da wasu kuma ba sa tavuka komai. Sanatan ya bayyana haka ne a wata hira da gidan talabijin na Channels. A cewar ɗan majalisar tarayyar, Tinubu yana da tsarin “mafi kyau” da zai tafiyar da mulkin ƙasar, amma babu wani tsari da mataimaka da za su sa ga kai gaci.…
Read More
Jami’in KEDCO ya kashe abokin aikinsa a Kano

Jami’in KEDCO ya kashe abokin aikinsa a Kano

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja An bayyana ɓacewar Bello Bukar Adamu, wani mazaunin Kano kuma jami’in Kamfanin Lantarki na Kano (KEDCO), bayan ya samu kiran gaggawa daga Sadik, matashin da ake kyautata zaton amininsa ne kuma abokin aikinsa a Kamfanin na Rarraba Wutar Lantarki na KEDCO. Bayan kwana biyu ne kuma a ka tsinci gawar tasa a wani titi da ke Ƙaramar Hukumar Kumbotso a jihar. Abdullahi Abubakar, ƙanin Bello, ya ce marigayin yana a gida da misalin ƙarfe 12 na daren Lahadi, 5 ga Mayu, 2024, lokacin da Sadiq ya yi masa kira na gaggawa. Ya ce suna…
Read More
Editan FirstNews ya aijiye aikinsa bayan tsare shi da sojoji suka yi

Editan FirstNews ya aijiye aikinsa bayan tsare shi da sojoji suka yi

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Editan FirstNews, Segun Olatunji, ya yi murabus sa’o’i bayan da jaridar ta nemi afuwar shugaban ma’aikatan fadar shugaban ƙasa, Femi Gbajabiamila. Olatunji, wanda ya shafe kwanaki 14 a hannun hukumar leƙen asiri ta tsaro (DIA) da ke Abuja domin bayar da rahoto kan Gbajabiamila, ya ce ya yi murabus ne domin kare lafiyarsa da na iyalansa. Hakan ya faru ne bayan wani rahoto da Olatunji ya rubuta mai taken: “Yadda Gbajabiamila ya yi yunqurin karkatar da dala biliyan 30, gidaje 66 ta hanyar Sabiu”. Kamfanin FirstNews, a cikin wata sanarwa a ranar Laraba, 8 ga Mayu,…
Read More
Tsohon ɗan wasan Super Eagles, Tijjani Babangida ya rasa ɗa da ƙani a hatsarin mota

Tsohon ɗan wasan Super Eagles, Tijjani Babangida ya rasa ɗa da ƙani a hatsarin mota

*Yayin da matarsa ta rasa idonta guda Tsohon ɗan wasan ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Super Eagles, Tijjani Babangida, ya rasa ɗansa Fadil mai kimanin shekara guda da haihuwa a wani mummunan hatsarin mota da ya rutsa da su. Haka nan, an ce matarsa Maryam ta rasa idonta ɗaya a sakamakon hatsarin wanda ya auku ranar Alhamis a hanyar Zariya zuwa Kaduna. Kazalika, wani ɗan uwan mahaifin Tijjanin, mai suna Ibrahim Babangida shi ma ya rasu sakamakon hatsarin. Har wa yau, bayanai sun ce wani ƙarnin Tijjani mai suna Ibrahim wanda shi ma yake cikin motar, nan take rai ya yi…
Read More
Gwamnati ta sanar da lokacin da za a kammala hanyar jirgin ƙasan Kano-Daura

Gwamnati ta sanar da lokacin da za a kammala hanyar jirgin ƙasan Kano-Daura

Daga BASHIR ISAH Gwamnatin Tarayya ƙarƙashin jagorancin Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ta ce za a kammala aikin layin dogo na Kano-Daura ya zuwa 2025. Ministan Sufuri, Said Alkali, ya ba da tabbacin hakan ne yayin zantawarsu da manema labarai ranar Juma'a a Abuja bayan ziyarar gani da idon da ya kai inda ayyukan hanyar jirgin ƙasan Kano-Maradi da Kaduna-Kano ke gudana. A cewar Ministan, wannan aikin na daga cikin muhimman ayyukan da Ma'aikatar ke ƙoƙarin ganin ya kammala don a fara cin moriyarsa. Bayanin haka na ƙunshe ne cikin sanarwa mai ɗauke da sa hannun Mataimakin Daraktan Yaɗa Labarai…
Read More
Ba a dakatar da shugaban APC na Zamfara ba, cewar uwar jam’iyya ta jiha

Ba a dakatar da shugaban APC na Zamfara ba, cewar uwar jam’iyya ta jiha

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau Jam’iyyar APC reshen jihar Zamfara ta buƙaci magoya bayanta da su yi watsi da batun dakatar da shugaban jam’iyyar na jihar, Hon. Tukur Umar Danfulani. Hakan na ƙunshe ne a wata sanarwa da aka miƙa wa Blueprint Manhaja a ranar Asabar mai ɗauke da sa hannun sakataren yaɗa labaran jam’iyyar na jihar, Yusuf Idris, a Gusau. A cewar sanarwar, dakatarwar da aka yi wa shugaban ya samo asali ne daga wasu ɓata-garin mambobin jam'iyyar da ke nuna kansu a matsayin shugabannin jam’iyyar a mazaɓar Galadima da ke ƙaramar hukumar Gusau. "Hedikwatar Jiha, Kwamitin Ayyuka na…
Read More
Manyan jami’an sojin Nijeriya 29 sun yi murabus

Manyan jami’an sojin Nijeriya 29 sun yi murabus

Daga BASHIR ISAH A ranar Juma'ar da ta gabata wasu Janar-janar na sojin Nijeriya 29 suka yi murabus daga aiki a barikin soji da ke Jaji, Jihar Kaduna. Majiyarmu ta ce 19 daga cikinsu Manjo-janar ne, yayin da 10 ke da muƙamin Birgediya-Janar. Daga cikin jami'an da lamarin ya shafa har da Manjo Janar Victor Ezugwu, wanda ya wakilci takwarorinsa wajen yin jawabi. Da yake jawabin, Victor ya ce yaƙi da 'yan ta'adda zai zo ƙarshe ne idan aka ƙarfa wa dakaru salon yaƙin dare da sauransu. Ezugwu ya yi kira ga manya da ƙananan sojojin da ke bakin aiki…
Read More
Yanzu-yanzun: An kori shugaban jam’iyyar APC na Jihar Zamfara, Tukur Danfulani

Yanzu-yanzun: An kori shugaban jam’iyyar APC na Jihar Zamfara, Tukur Danfulani

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau Jam’iyyar APC reshen Galadima dake ƙaramar hukumar Gusau ta jihar Zamfara, ta kori shugaban jam’iyya na jihar, Alhaji Tukur Danfulani Maikatako, daga jam’iyyar inda ta ce ba shi da ikon jagorantar jam’iyyar a jihar. A yayin ganawa da manema labarai ranar Asabar a Gusau, babban birnin jihar, ’yan majalisar zartarwa na jam’iyyar APC dake mazaɓar Galadiman, sun bayyana cewar sun ƙuduri aniyar ceto jam’iyyar daga mummunan shugabancin Alhaji Tukur Danfulani. Kakaki kuma mataimakin shugaban jam’iyyar APC Gundumar Galadima na ƙaramar hukumar Gusau inda shugaban jam’iyyar na jiha, Alhaji Garba Bello ya bayyana cewa 16 daga…
Read More