11
May
Daga BASHIR ISAH Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya biya tsoffin ma'aikatan jihar bashin giraduti sama da Naira biliyan 4.3 da suke bin gwamnatin jihar tun daga shigar 2011. Mai magana da yawun Gwamnan Zamfara, Sulaiman Bala Idris, an fara biyan waɗanda lamarin ya shafa haƙƙoƙinsu ne tun a watan Fabrairu bayan kammala tantance su. Sanarwar da ya fitar ta ce, gwamnatin Zamfara ta biya biliyan N4,337,087,492.06 ga tsafin ma'aikatan jihar da na ƙananan hukumomi da suka yi ritaya. “A watan Fabrt Gwamna Dauda Lawal ya kafa kwamitin tantance bayanan waɗanda lamarin ya shafa sannan aka biya su bashin giraduti…
