Editor

9513 Posts
NYSC ta yi bikin kammala horar da masu hidimar ƙasa sama da 2,000 a jihar Nasarawa

NYSC ta yi bikin kammala horar da masu hidimar ƙasa sama da 2,000 a jihar Nasarawa

Daga JOHN D. WADA a Lafiya An yi kira na musamman ga duka hukumomi da ofishohi daban-daban da ake turo ‘yan hidimar qasa a sassan jihar Nasarawa baki ɗaya su tabbar suna bai wa sabbin masu hidimar ƙasar waɗanda aka turo hukumominsu cikakken kulawa da goyon baya a koyaushe don basu damar gudanar da ayyukansu yadda ya dace. Kodinetan hukumar masu hidimar ƙasar wato NYSC a turance na jihar Nasarawa Abdullahi Jiqamshi ne ya yi wannan kira a jawabinsa a wajen bikin kammala horon na bana na rukunin A sama da mutum 2000 wadda aka gudanar a sansanin ‘yan yi…
Read More
Farfesa Sa’adatu ta karɓi ragamar jagorancin Jami’ar Nasarawa a hukumance

Farfesa Sa’adatu ta karɓi ragamar jagorancin Jami’ar Nasarawa a hukumance

Daga JOHN D. WADA a Lafiya A yanzu haka sabuwar Shugabar Babbar Jami’ar Jihar Nasarawa dake birnin Keffi hedikwatar Ƙaramar Hukumar Keffi a jihar, Farfesa Sa’adatu Hassan Liman da aka naɗa ta kwanan nan ta kama aiki gadan-gadan. Farfesa Sa’adatu Hassan Liman ta kama aiki a hukumance ne a matsayin mace ta farko da aka naɗa a matsayin sabuwar shugabar jami’ar ta jihar Nasarawa bayan ta karɓi ragamar mulkin jami’ar a hukumance daga gun mai riƙon ƙwaryar muƙamin wato Farfesa Sallau Modibbo wanda shine muƙaddashin shugabar jami’ar ta fannin ilimi a yayin wani zaman karɓan karagar aikin wadda aka gudanar…
Read More
An yi garkuwa da jariri ɗan wata huɗu

An yi garkuwa da jariri ɗan wata huɗu

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja ’Yan bindiga sun yi garkuwa da wani jariri ɗan wata huɗu da haihuwa a Jihar Akwa Ibom. Da misalin ƙarfe 3 na daren Asabar ne wasu ’yan bindiga biyu suka kutsa cikin gidan wani magidanci mai suna Mista Edeme Eyo suka ƙwace jaririn nasu. Mista Edeme Eyo ya ce maharan da suka zo ɗauke da bindigogi da adduna sun kutsa har cikin uwar ɗakinsu ne suka ɗora musu bindiga a kai da matarsa, suka nemi a ba su jaririn. A cewarsa, ’yan bindigar sun fi ƙarfinsa, matarsa tana ihu, amma suka ƙwace jaririn daga…
Read More
Za mu yi gagarumar zanga-zanga idan ba a soke harajin tsaron intanet ba – TUC

Za mu yi gagarumar zanga-zanga idan ba a soke harajin tsaron intanet ba – TUC

Daga SANIAHMAD GIWA a Abuja Ƙungiyar Ƙwadago ta TUC a Nijeriya ta yi barazanar gudanar da gagarumar zanga-zanga tare da dakatar da al'umura a faɗin ƙasar matuƙar gwamnatin tarayya ba ta soke sabon harajin tsaron intanet da Babban Bankin ƙasar ya ɓullo da shi ba. Ƙungiyar ta yi barazanar ce a wata sanarwa da ta fitar ranar Laraba, wadda ta samu sa hannun shugaban ƙungiyar, Festus Osifo. Hakan na zuwa ne bayan ita ma ƙungiyar ƙwadago ta TUC ta soki lamirin sabon harajin, wanda ta bayyana a matsayin wani gagarumin nauyi da gwamnati ke ɗora wa talaka. A ranar Talata…
Read More
Dortmund ta fitar da PSG daga gasar Zakarun Turai

Dortmund ta fitar da PSG daga gasar Zakarun Turai

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Borussia Dortmund ta kai wasan ƙarshe a gasar Zakarun Turai, bayan da ta yi nasarar cin Paris St Germain 1-0 ranar Talata a Faransa. Ƙungiyoyin sun je hutu babu ci ko ɗaya, bayan da suka koma zagaye na biyu ne Dortmund ta ci ƙwallo ta hannun Mats Hummels. A ranar Talata a makon jiya a wasan farko a daf da ƙarshe a Jamus, Dortmunda ta yi nasara 1-0, kuma Niclas Fullkrug ne ya ci mata ƙwallon tun kan hutu. Kenan Dortmund ta kai wasan ƙarshe a gasar zakarun Turai ta bana da cin ƙwallo 2-0 gida…
Read More
Adadin yaran da ba sa tafiya makaranta ya kai miliyan 18 a Nijeriya — UNICEF

Adadin yaran da ba sa tafiya makaranta ya kai miliyan 18 a Nijeriya — UNICEF

Daga BASHIR ISAH Asusun Kula da Ƙananan Yara na Majalisar Ɗinkin (UNICEF) ya koka kan yadda ake samun ƙaruwar yaran da ba sa tafiya makaranta a Nijeriya, tare da cewa, yanzu adadin waɗannan yara ya kai miliyan 18.3. Ya ce wannan adadi ya sa Nijeriya ta zama ƙasar da ta fi kowace ƙasa a faɗin duniya yawan yaran da ba sa tafiya makaranta. Babban Jami'in UNICEF a Bauchi, Dokta Tushar Rane, shi ne ya bayyana haka a wajen taron masu ruwa da tsaki na yini biyun da aka shirya a Gombe kan batun ƙananan yaran da ba sa tafiya makaranta…
Read More
Ni ban ɗauki rubutun batsa a matsayin matsala ba – Mukhtar Yakubu

Ni ban ɗauki rubutun batsa a matsayin matsala ba – Mukhtar Yakubu

"Rubutu abu ɗaya ne, abin da za a rubuta ne ke bambanta su" Daga AISHA ASAS A wannan karon dai shafin adabi ɗan gida ya ɗauko maku, domin mun tattauna ne da ɗaya daga cikin daɗaɗɗun wakilan Manhaja, kuma marubuci da ya rubuta littafan hikaya da kuma na addinin Musulunci. A tattaunawar mai karatu zai ji yadda ɗan jaridar ya rikiɗe zuwa marubucin ƙagaggun labarai da kuma dangantakar da ke tsakanin aikin jarida da rubutun labari.Idan kun shirya, Aisha Asas ce tare da Mukhtar Yakubu; MANHAJA: Duk da kai ba baƙo ba ne a Manhaja za mu so jin tarihin…
Read More
Hajjin 2024: Gwamna Bago ya ɗauke wa maniyyatan Neja nauyin Hadaya

Hajjin 2024: Gwamna Bago ya ɗauke wa maniyyatan Neja nauyin Hadaya

Daga BASHIR ISAH Gwamnan Jihar Neja, Mohammed Umaru Bago, ya ɗauke wa maniyyatan bana a jihar nauyi hadaya yayin aikin Hajjin bana. Gwamnan ya ɗauke wa maniyyatan nauyin ne ta hanyar biya wa kowannensu Dala 200. Amirul Hajji na jihar, Attahiru Gunna, shi ne ya bayyana haka ga manema labarai a Minna, babban birnin jihar. Attahiru ya ce za a maida wa maniyyatan da suka riga suka miƙa kuɗin hadayar da kuɗaɗensu. Maniyyata sama da 3000 ake sa ran a bana za su sauke farali daga jihar. Ya ƙara da cewa, maimakon tashi ta Abuja zuwa Saudiyya kamar yadda aka…
Read More
Kotu ta ba da belin Sirika da ‘yarsa kan N100m

Kotu ta ba da belin Sirika da ‘yarsa kan N100m

Daga BASHIR ISAH Babbar Kotun Tarayya mai zamanta a Abuja ta ba da belin tsohon Minista a Gwamnatin Buhari, Hadi Sirika 'yarsa tare da wasu mutum biyu kan kuɗi Naira miliyan 100 da shaidu guda biyu. Idan za a iya tunawa hukumar yaƙi da rashawa ta EFCC ta maka waɗanda lamarin ya shafa a kotu ne bisa zargin laifuka shida. EFCC na zargin Sirika da yin amfani da damar ofishins wajen aikata ba daidai ba tsakanin Afrilun 2022 da Maris, 2023 a Abuja. Kazalika, hukumar tana zargin tsohon ministan da yin sama da faɗi da biliyan N1.3 wajen ba da…
Read More
Namiji ko yau ya fara mu’amalantar mace a shimfiɗa to farfesa ne a fannin – Likitar Ma’aurata

Namiji ko yau ya fara mu’amalantar mace a shimfiɗa to farfesa ne a fannin – Likitar Ma’aurata

Ba laifi ko rashin so ke sa maza ƙarin aure ba - Sa'adatu Kankia (Ci gaba daga makon jiya) Daga AISHA ASAS A satin da ya gabata, mun fara tattaunawa kan sha’anin ƙarin aure, inda shafin Gimbiya ya gayyato maku ƙwararru kan zamantakewar aure, wato Sa’adatu Saminu Kankia da kuma Zuwaira Dauda Kolo, wadda ku ka fi sani da Likitar Ma'aurata.A wannan satin, kamar yadda muka yi maku alƙawari, za mu ɗora ne daga inda muka tsaya. A sha karatu lafiya; MANHAJA: Har yau dai muna kanki Sis Kolo, zancen sha'awa da ki ka yi a matsayin dalilin da ke…
Read More