Editor

9513 Posts
Badaƙalar N2bn: EFCC ta maka ‘yar gidan Sirika a kotu

Badaƙalar N2bn: EFCC ta maka ‘yar gidan Sirika a kotu

Daga BASHIR ISAH Hukumar yaƙi da rashawa ta EFCC, za ta gurfanar da 'yar gidan tsohon Minista Hadi Sirika, Fatimah, tare da wasu mutum biyu a kotu a ranar Alhamis. Ana zargin waɗanda lamarin ya shafa ne da laifin badaƙalar kwangila ta sama da Naira biliyan 2.7 a ƙarƙashin Ma'aikatar Aufurin Jirgin Sama ƙarƙashin jagorancin Sirika. Gobe Alhamis shi ne zai zama karon farkon da Sirika zai gurfana a gaban Alƙali Sylvanus Oriji a Babbar Kotun Abuja. Ana sa ran Sirika ya bayyana a gaban kotu tare da wasu mutum uku, ciki har da 'yarsa Fatima da kuma kamfanin Al-Duraq…
Read More
Gaza: An kashe mutum 34,789 an jikkata 78,204 – Shawesh

Gaza: An kashe mutum 34,789 an jikkata 78,204 – Shawesh

Daga BASHIR ISAH Jakadan Falasɗinu a Nijeriya, Abdullah M. Abu Shawesh, ya ce kawo yanzu, adadin waɗanda aka kashe a Gaza ya ƙaru zuwa 34,789, sannan 78,204 sun jikkata. Shawesh ya bayyana haka ne a wata sanarwar manema labarai da ofishinsa ya fitar mai ɗauke da kwanan wata 8 ga Mayu, 2024. Sanarwar ta kuma taɓo batun manyan kaburburan da aka gano inda aka turbuɗe mutane dama, tari bayyana lamarin a matsayin abin takaici. Ta ƙara da cewa, abin da ake gani a yau, ba yaƙin Isra'ila da Hamas ba ne, amma yaƙin Isra'ila ne a kan Falasɗinawa. Ta ci…
Read More
Yadda za ka ɓullo wa maganar ƙaro aure

Yadda za ka ɓullo wa maganar ƙaro aure

Tare da AMINA YUSUF ALI Assalamu alaikum wa rahmatullah. Masu karatu sannunku da jimirin karatun shafinmu na zamantakewa daga jaridarku mai farin jini ta Manhaja. Ina muku godiya fatan alkhairi kamar yadda koyaushe kuke yi min ta hanyar kiran waya ko saƙon tes.  Rubutun wannan mako dai na maza ne. Za mu yi magana a kan matakan da ya kamata 'yanuwa maza su ɗauka yayin da suke da nufin ƙaro aure. Ko kuma gwari-gwari a ce ƙaro mata daga ɗaya zuwa biyu, har ma sama da haka. Maza da yawa suna kokawa a kan yadda matansu na gida ke birkice…
Read More
Tinubu ya isa Abuja bayan shafe makonni biyu a ƙetare

Tinubu ya isa Abuja bayan shafe makonni biyu a ƙetare

Daga BASHIR ISAH Shugaban Ƙasa Bola Tinubu, ya isa Abuja daga tafiyar mako biyu da ya yi zuwa ƙetare. MANHAJA ya tattaro cewar, Tinubu ya isa fadar Villa da ke Abuja da safiyar Laraba. A ranar 23 ga Afrilu Tinubu ya bar Nijeriya zuwa ƙasar Netherlands don halartar taron tattalin arziki. Bayan taron yini uku da ya halarta a ƙasa ta Netherlands, daga nan ya cilla zuwa Saudiyya domin halartar babban taro na duniya kan tattalin arziki, wato WEF a taƙaice. Sai dai, babu wani bayani a hukumance dangane da tsawaita zaman da Tinubu ya yi a ƙetare, lamarin da…
Read More
Rashin kyawun jirgi ya hana Shettima tafiya taro a Amurka

Rashin kyawun jirgi ya hana Shettima tafiya taro a Amurka

Daga BASHIR ISAH Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima, ba zai samu halartar babban taron kasuwanci da ke gudana a Amurka ba sakamakon rashin kyawun Jirgin saman Shugaban Ƙasa. Taron wanda haɗin gwiwa ne tsakanin Amurka da Afirka, an shirya Shettima zai halarta ne a madadin Shugaba Bola Tinubu, wanda zai gudana daga ran 6 zuwa 9 ga Mayu, 2024. Sai dai kuma, ala tilas Shettima ya fasa wannan tafiyar saboda rashin kyawun jirgin da zai ɗauke su zuwa Amurka. Mai magana da yawun Mataimakin Shugaban Ƙasar, Stanley Nkwocha, ya faɗa a ranar Litinin cewa, matsalar gyara da jirgin saman da…
Read More
Aminu Ala da Ado Gidan Dabino sun shiga cikin fitattun mutane 100 da suka bada gudummawa don cigaban Jihar Kano

Aminu Ala da Ado Gidan Dabino sun shiga cikin fitattun mutane 100 da suka bada gudummawa don cigaban Jihar Kano

DAGA MUKHTAR YAKUBU Ƙungiyar DHS int'l& Project Rescue Nigeria Team ta yi nazari tare da binciko mutane 100 da suka yi fice wajen kawo cigaba tare da havvaka al'amuran da suka samar da bunƙasar Jihar Kano. Binciken wanda ya hada kama daga malamai, 'yan kasuwa, 'yan siyasa da sarakuna da masu fasaha da ƙungiyar ta gudanar a cikin al'ummar Jihar Kano domin duba da kuma zaƙulo mutanen da suka kawo cigaban Jihar Kano domin karrama su in da suka shafe tsawon lokaci suna gudanar da binciken. A ranar Asabar ɗin da ta gabata ne dai aka yi babban taro a…
Read More
Gudunmawar ’yan jarida ga inganta muhalli

Gudunmawar ’yan jarida ga inganta muhalli

Tare da ABBA ABUBAKAR YAKUBU Yau Juma'a 3 ga watan Mayu, ake bikin Ranar Kare ’Yancin ’Yan Jarida ta Duniya. Ana raya wannan rana ne, domin yabawa da irin faɗi tashin da manema labarai ke yi, a fagage daban-daban, don bayyanawa jama'a halin da duniya ke ciki, cikin gaskiya da ’yanci. Har wa yau, ranar na kasancewa lokacin tunatar da masu faɗa a ji da gwamnatoci muhimmancin mutunta ’yancin ’yan jaridu, da kuma su kansu manema labarai a tuna musu haqqin da ke kansu na tsare gaskiya da adalci da kiyaye ƙa'idojin aikin jarida a duk lokacin da suke bakin…
Read More
Gwamna Abba ya rattaɓa hannu kan dokar tantance lafiya kafin aure a Kano

Gwamna Abba ya rattaɓa hannu kan dokar tantance lafiya kafin aure a Kano

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya amince da dokar tantance lafiyar mata kafin aure a jihar Kano a hukumance, wadda ta tanadi duba lafiyar duk masu son yin aure. Kamar yadda sabuwar dokar ta tanada, ba za a yi aure ba a Kano ba tare da ba da takardar shaidar tantance lafiyar jinsin halitta, hepatitis B da C, HIV/AIDS, da sauran cututtuka masu alaƙa da su ba. A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar, ya ce samar da dokar ya zama dole domin rage…
Read More
Kwamitin ayyuka na ƙasa ne kaɗai ke da ikon dakatar da Ganduje — Kana

Kwamitin ayyuka na ƙasa ne kaɗai ke da ikon dakatar da Ganduje — Kana

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Mai bai wa jam’iyyar APC shawara kan harkokin shari’a, Abdulkarim Kana, ya ce kwamitin ayyuka na jam’iyyar APC na ƙasa, wato National working committee (NWC), shi ne kaɗai ke da alhakin dakatar da shugaban jam’iyyar na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje. Kana ya bayyana haka ne yayin hira a shirin siyasa na gidan talabijin na Channels a ranar Litinin. Ya yi wannan martani ne kan dakatarwar da wasu shugabannin jami'yyar APC a mazaɓar Ganduje da ke Ƙaramar Hukumar Dawakin Tofa a Jihar Kano, suka yi wa shugaban jam'iyyar na ƙasa. Shugabannin jam'iyyar a mazaɓar sun dakatar…
Read More
Da Ɗumi-ɗumi: Kano Pillars ta dakatar da kocinta Abdu Mai-Kaba

Da Ɗumi-ɗumi: Kano Pillars ta dakatar da kocinta Abdu Mai-Kaba

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Shugaban ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Kano Pillars, Alh. Babangida Little, ya bayyana dakatar da mai horar da 'yan wasan ƙungiyar, Abdu Maikaba, a ranar Talata. Babangida Little ya bayyana dakatarwar da kuma kafa wani kwamiti wanda zai binciki kocin kuma idan aka same shi da laifi, to, zai fuskanci ladaftarwa. Kawo yanzu ba a bayyana ainihin dalilin dakatarwar da aka yi masa ba, sai dai wasu na zargin furucin da Abdu Mai-kaba ya yi a lokacin wani taro da ƙungiyar magoya bayan Kano Pillars suka yi a cibiyar 'yan Jaridu ta jiha ne ya haifar…
Read More