07
May
Daga MAHDI M. MUHAMMAD A shekara ta 1839, an saci Sengbe Pieh, wani manomi kuma ɗan tireda daga Saliyo a matsayin bawa. Kan hanyar zuwa Amurka ya jagoranci tawaye a cikin jirgin ruwan jigilarsu, abin da ya kawo ƙarshen cinikin bayi a Amurka. Babu dai takamaimen lokacin da ake iya cewa shi ne lokaci da aka haifi Sengbe Pieh, sai dai masana tarihi sun yi ittifakin cewa, an haife shi ne a shekarar 1814 a ƙasar da a yanzu ake kira Saliyo. An yi imanin an haife shi a wani tsibiri da ke gundumar Bonthe, wajen da ya yi ƙaurin…
