Editor

9513 Posts
Masu kwaɗayin kujerar shugabancin Nijeriya su rungumi ƙaddara, Tinubu sai ya yi takwas – Ganduje

Masu kwaɗayin kujerar shugabancin Nijeriya su rungumi ƙaddara, Tinubu sai ya yi takwas – Ganduje

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Shugaban Jam’iyyar APC na Ƙasa, Dr. Abdullahi Ganduje ya bayyana cewa Shugaban Ƙasa Bola Tinubu zai ci gaba da zama shugaban Nijeriya har bayan 2027. Ganduje ya bayyana haka a lokacin da ya ke jawabi ga dandazon magoya bayan Jam’iyyar APC a sakatariyar jam’iyyar da ke Abuja. Ganduje ya ƙara da cewa tun ba a kai ko'ina ba jam’iyyun adawa sun fara kermar tsoron yin gaba da gaba da APC a zaɓuka masu zuwa bayan ɗan karan kayen da suka sha a zaɓen 2923. "Jam’iyyar NNPP sun fi duk jam’iyyun kiɗimewa. Sai tsalle-tsalle suke…
Read More
Ɗan majalisar Birnin Kano ya raba wa mutane 100 tallafin jari a mazaɓar Ɗan’agundi

Ɗan majalisar Birnin Kano ya raba wa mutane 100 tallafin jari a mazaɓar Ɗan’agundi

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano Ɗan majalisar dokokin Jihar Kano mai wakiltar Ƙaramar Hukumar Birnin Kano Hon. Ambasada Sarki Aliyu Daneji ya yi rabon tallafin jari ga al'ummar mazaɓar Ɗan'agundi. Da yake bayani game da tallafin ɗan majalisar Hon. Ambasada Sarki Aliyu Daneji ya ce tallafin na mutum 100 ne kuma da yardar Allah nan gaba za su sake dawowa su baiwa wasu duk waɗanda ba su samu a wannan karo ba su kwantar da hankalinsu har sai ya kai kowa ya dangwali romon dimukraɗiyya. Ya ce daga cikin ayyuka da ya gudanar cikin watanni 9 da zuwansu majalisar Jihar…
Read More
Kawar da ciwon hanta kafin 2030

Kawar da ciwon hanta kafin 2030

A baya-bayan nan ne ƙasashen duniya suka gudanar da bikin ranar yaƙi da cutar 'Hepatitis' wanda ake kira da ciwon hanta a Hausance, domin ƙara wayar da kan jama’a game da wannan mummunar cuta da ta yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama. Hepatitis ya kasu iri daban-daban har guda biyar, inda suka haɗa da; Hepatitis A, da Hepatitis B, da Hepatitis C, da Hepatitis D, da kuma Hepatitis E. Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce, kimanin mutum miliyan 325 ke fama da ciwon hanta nau'in B da C a duniya. A yayin da ciwon hanta nau'in B kawai ke kashe…
Read More
Gwamna Zulum ya samu nasarorin bunƙasa rayuwar al’ummarsa – Hon. Ayuba

Gwamna Zulum ya samu nasarorin bunƙasa rayuwar al’ummarsa – Hon. Ayuba

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Shugaban Jam'iyyar APC na Jihar Borno, Hon. Bello Ayuba ya lissafo wasu nasarorin da mai girma gwamnan jihar Farfesa Baba Gana Umara Zulum ya samu, inda ya bayyana gwamnan a matsayin mutum mai kishin al'umma da jiharsa. Hon Bello Ayuba ya ce Gwamna Babagana Umara Zulum ya samu ɗumbin nasarori musamman  a fannin inganta rayuwar bil'adama da sauransu. Shugaban Jam'iyyar APCn ya ce Gwamna Zulum ya bunƙasa ababen more rayuwa da shirye-shiryen da suka shafi jama'a kaitsaye kamar gina gidaje, gina manyan tituna a cikin gari da ƙauyaku a ƙananan hukumomi 27 da gina…
Read More
Shin za a tsagaita wuta bayan kashe sama da Gazawa 34,000?

Shin za a tsagaita wuta bayan kashe sama da Gazawa 34,000?

Tare da NASIRU ADAMU EL-HIKAYA Tambayar sanin yiwuwar tsagaita buɗe wuta da Isra'ila ke yi a Gaza na da muhimmanci don yadda a ke ta yunƙurin yiwuwar hakan amma sai a ke ta fuskantar cikas. Ba mamaki rashin niyyar Isra'ila ta dakatar da yaqin gabanin kashe duk 'yan Hamas ke kawo kwan gaba kwan baya. Tun mayar da martanin Isra'ila a sanadiyyar kutsawar mayaƙan Hamas cikin Isra'ila ranar 7 ga Oktobar bara a ke ta samun labaru masu ban takaici na yanda hare-haren Isra'ila ke yawan kashe mata da ƙananan yara. Ko yanzu ai Isra'ila ta wuce ramuwar gaiya ga…
Read More
Masu zanga-zanga sun buƙaci a sake buɗe tuhumar N70bn da ake yi wa Matawalle

Masu zanga-zanga sun buƙaci a sake buɗe tuhumar N70bn da ake yi wa Matawalle

Daga BASHIR ISAH Wasu masu zanga-zanga da suka mamaye harabar ofishin hukumar yaƙi da rashawa ta EFCC da ke Abuja, sun buƙaci a sake buɗe ƙarar zargin da ake yi wa tsohon gwamnan Jihar Zamfara, Bello Matawalle, na karkatar da kuɗaɗen jihar zuwa aljihunsa. A ranar Juma'ar da ta gabata aka ga masu zanga-zangar ɗauke da alluna da kwalaye masu ɗauke da saƙonnin buƙatar EFCC ta sake buɗe kes din badaƙalar almundahana a kan Matawalle. Masu zanga-zangar sun nuna rashin gamsuwarsu kan yadda EFCC ke tafiyar da batun Matawalle, inda suka buƙaci hukumar ta ƙara himma sannan ta tabbatar da…
Read More
An gano kaburbura ɗauke da ɗaruruwan gawarwaki a Gaza – Ofishin Jakadancin Falastinu

An gano kaburbura ɗauke da ɗaruruwan gawarwaki a Gaza – Ofishin Jakadancin Falastinu

Daga MAHDI M. MUH’D Ofishin Jakadancin Falastinu a Nijeriya ya bayyana cewa a rana ta 209 na ƙazamin yaƙin kisan ƙare dangi da ake yi wa al'ummar Palastinu, an gano kaburbura masu yawa a zirin Gaza. Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwar da Jakadan Falastinu a Nijeriya, Abdullah Shawesh ya fitar ga manema labarai a Alhamis. Sanarwar ta ce, "yaƙin ya bar kimanin tan miliyan 37 na tarkacen bama-bamai da suka fashe. An yi hasashen cewa za a ɗauki shekaru 14 kafin a kwashe ɓaraguzan da suak fashe ɗin. "Ya zuwa ranar 1 ga watan Mayu, adadin shahidan…
Read More
’Yan ƙwadago sun buƙaci soke ƙarin kuɗin lantarki

’Yan ƙwadago sun buƙaci soke ƙarin kuɗin lantarki

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Shugabannin ƙungiyoyin ƙwadago na Nijeriya, Joe Ajaero da Festus Osifo, yayin da su ke gabatar da jawabi na haɗin gwiwa a bikin ranar ma'aikata a Abuja, a ranar Laraba, sun buƙaci Gwamnatin Tarayya da soke ƙarin kuɗin wutar lantarki tare da sausauta duk wani nau'i na haraji ga al'umma. A cikin buƙatu guda 18 da shugabannin ƙwadagon suka gabatar, sun ce ya kamata a sake duba aikin sayar da wutar lantarki a ƙasar don kar da a samu koma baya. Bugu da ƙari, suna son gwamnati ta gaggauta fitar da motocin bas ɗin CNG a faɗin…
Read More
’Yan sanda sun cafke jigon kai harin jirgin ƙasan Abuja-Kaduna

’Yan sanda sun cafke jigon kai harin jirgin ƙasan Abuja-Kaduna

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Rundunar ’yan sandan Nijeriya ta ce jami’anta sun kama wani Ibrahim Abdullahi, wanda aka fi sani da Mande, wanda ake kyautata zaton shi ne ya kitsa kai harin jirgin ƙasa daga Abuja zuwa Kaduna a watan Maris ɗin 2022 da kuma yin garkuwa da ɗaliban Jami’ar Greenfield da kuma yawan sace-sacen da aka yi a Abuja. An kama Mande tare da wasu da dama da ake zargi. Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, ACP Olumuyiwa Adejobi, ne ya bayyana hakan a yayin ganawa da manema labarai a jihar Kaduna. Yayin da yake gabatar da waɗanda ake…
Read More
KNEP da AFAN za su tallafa wa manona da takin a Jigawa

KNEP da AFAN za su tallafa wa manona da takin a Jigawa

Daga UMAR AKILU MAJERI a Dutse Ƙungiyar manoma a Jihar Jigawa mai Suna Kenap ƙarƙashin jagorancin Alh Nura Ahmed Sale, ta ce za su haɗin gwiwa da ƙungiyar AFAN wajen samar wa anoma taki mai inganci cikin sauki a Jihar jigawa . Sale ya buƙaci haɗin kan ƙungiyar Afan ne saboda karfinta da kuma yadda take taimakon manoma a Nijeriya. Ya ce haɗinkansu ya zama dole domin saida haɗakai ne za su iya cimma burinsu na nuna wa manoma yadda ake amfani da wannan takin mai cokali. Ya ce takin na da inganci fiye da buhun takin zamani mai nauyin…
Read More