04
May
Daga MAHDI M. MUHAMMAD Rundunar Sojojin Nijeriya ta bayyana cewa, ta kammala binciken da aka daɗe ana dakon sakamakonsa kan bom ɗin da aka jefa bisa kuskure kan mutanen ƙauyen Tudun Biri a Ƙaramar Hukumar Igabi da ke Jihar Kaduna. Ta kuma ce, sojojin da aka samu da laifi a kai harin, za su gurfana a gaban kotun soji, domin fuskantar hukunci. Daraktan yaɗa labarai na hedikwatar tsaron Nijeriya, Edward Buba, ne ya bayyana haka a taron manema labaran da aka gudanar a Abuja. A Disambar bara ne wani jirgin sojoji ya jefa bom kan mutanen da ke bikin Maulidi,…
