Editor

9513 Posts
Faransa ta sha alwashin kawo ƙarshen hare-haren da ake kai wa matasa

Faransa ta sha alwashin kawo ƙarshen hare-haren da ake kai wa matasa

Gwamnatin Faransa na duba yuwuwar yadda za a kawo ƙarshen hare-haren da ke faruwa a tsakanin matasa, bayan cakawa wani ɗan shekara 15 wuƙa da wani matashi ya yi a ƙarshen mako, ɗaya daga cikin jerin hare-haren da ya girgiza al’ummar ƙasar. Firaministan Faransa Gabriel Attal ya shirya tarurrukan da jam'iyyun siyasa kan yadda za a tunkari wannan matsala da ke neman wuce gona da iri. Ƙasar Faransa dai ta fuskanci jerin hare-hare kan matasa daga takwarorinsu a 'yan makonnin nan, inda masu tsatsauran ra'ayi da masu ra'ayin mazan jiya suka danganta wannan matsala da manufofin gwamnati na sassauta sha’anin…
Read More
Man United ta fi nuna ƙwarewarta a Firimiya – Ten Hag

Man United ta fi nuna ƙwarewarta a Firimiya – Ten Hag

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Erik ten Hag ya bayyama cewa Manchester United ɗaya ce daga cikin ƙungiyoyin da ta fi nuna bajinta a gasar Firimiya ta bana. Kocin ya faɗi hakan duk da ƙungiyar Old Trafford na fama da kalubalen cin wasa ko dai a gida ko a waje a kakar nan. Ranar Asabar United ta tashi 1-1 da Burnley a firimiya, wadda take ta biyun ƙarshe, inda mai tsaron raga, Andre Onana ya yi kuskuren da aka farke a bugun fenariti ta hannun Zeki Amdouni. Hakan na nufin Ten Hag ya samu nasarar wasa daya a cikin minti 90…
Read More
Tinubu ya taya Idris murnar zagayowar ranar haihuwarsa

Tinubu ya taya Idris murnar zagayowar ranar haihuwarsa

Daga BASHIR ISAH Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya taya Ministan Labarai da Wayar da Kan 'Yan Ƙasa, Mohammed Idris, murnar zagayowar ranar haihuwarsa. Hakan na ƙunshe ne cikin sanarwar da mai magana da yawun Shugaban Ƙasa, Ajuri Ngelale, ya fitar a ranar Laraba. Sanarwar ta ce, Ministan hadimin gwamnati ne wanda ya zo a daidai lokacin da ake buƙatarsa. Ta ƙara da cewa, Ministan wanda mawallafi ne kuma ɗan siyasa, yana aiki da ƙwarewa a matsayinsa na Ministan Labarai da Wayar da Kan 'Yan Ƙasa. Haka nan, ta ce Idris na daga cikin 'yan sahun gaba a fagen yaɗa labarai…
Read More
Kafa makarantun boko na farko a Ƙasar Hausa

Kafa makarantun boko na farko a Ƙasar Hausa

Daga SADIQ TUKUR GWARZO Kafin a gabatar da ilimin boko a Jihohin Arewa, sai da Gwamna Lugga ya sa aka yi bincike aka gano yawan makarantun allo da ake da su, da yawan almajiransu. A cikin wani kintaci-faɗi an gano cewa a farkon ƙarni na ashirin, akwai makarantun allo guda 25,009 masu yawan ɗalibai 218,618 a garuruwan jihar Arewa. Ganin ƙarfin ilimin addininin Musulunci, sai Gwamna Lugga ya ga cewa ba daidai ba ne a gabatar musu da ilimin boko kamar yadda ake tafiyar da shi a Ingila. Mun dai riga mun sani tun wajen shekarar 1900 aka buɗe makarantun…
Read More
Ana yi wa harkar rubutu shiga shantun ƙadangare – Abou Othaymeen

Ana yi wa harkar rubutu shiga shantun ƙadangare – Abou Othaymeen

"Ina fatan na narka ruwan gwalagwalan hikimomin da aka yi mini baiwar sa" Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU Malam Nura Isma'il, wanda aka fi sani da Abou Othaymeen, ba voyayye ba ne a tsakanin marubutan adabi na Hausa da Turanci, har ma da Larabci. Ya daɗe yana ba da gudunmawa a ɓangaren adabin zube da rubutattun waƙoƙi. Sannan kuma har wa yau hafizi ne na Alƙur'ani Mai Girma, kuma malamin makaranta. Shi ne ya jagoranci tilawar haddar Alƙur'ani Mai Girma da marubuta suka gudanar a zauren marubuta na manhajar WhatsApp. A tattaunawar sa da Abba Abubakar Yakubu, Malam Nura, ya bayyana…
Read More
Ranar Ma’aikata: Gwamnan Zamfara ya jaddada ƙudurinsa na kyautata rayuwar ma’aikatan jihar

Ranar Ma’aikata: Gwamnan Zamfara ya jaddada ƙudurinsa na kyautata rayuwar ma’aikatan jihar

Daga BASHIR ISAH Gwamna Dauda Lawal na Jihar Zamfara ya jaddada ƙudurin gwamnatinsa na kyautata wa rayuwar ma'aikatan jihar. Ya bayyana haka ne a wajen taron bikin Ranar Ma'aikata na bana wanda aka saba gudunarwa ran 1 ga Mayun kowace shekara. Bikin bana a jihar ya gudana ne a ranar Laraba a Sakatariyar JB Yakubu, Gusau, babban birnin jihar. Cikin sanarwar da ta fitar, Kakakin Gwamna, Sulaiman Bala Idris, ya ce gwamnatin jihar ba za ta baro ma'aikatan jihar a baya wajen gudanar da harkokinta. Sulaiman ya rawaito Lawal na cewa, “Gwamnatina na sane da muhimmiyar rawar da ma'aikata ke…
Read More
A saka hankali yayin zaɓin aure

A saka hankali yayin zaɓin aure

Assalam alaikum. Da fatan kowa ya yi sallah lafiya? Allah ya albarkaci Jaridar Blueprint Mahaja. A yau zan yi wasiƙa ne a kan zaɓin ma'aurata, domin shi ne babban abin da ke ci wa kowa tuwo a ƙwarya a halin yanzu. Wanda kuma hakan ke jawo yawan mace-macen aure, domin ana auren ne kawai barkatai ba tare da sanin wa ya kamata a aura ba. Babban hadafin da ya ke sanya mu zaɓar wanda zamu rayuwa da shi ko wacce zamu rayu da ita a matsayin rayuwar aure shi ne samun nutsuwar rayuwa, shi kuwa samun nutsuwar ruhi da abokiyar…
Read More
1 ga Mayu sabon albashi mafi ƙaranci zai fara aiki – Gwamnati

1 ga Mayu sabon albashi mafi ƙaranci zai fara aiki – Gwamnati

*Ba mu amince da ƙarin albashin kashi 35 ba — NLC Daga BSHIR ISAH Gwamnatin Tarayya ta ba da tabbacin cewa sabon albashi mafi ƙaranci zai fara aiki daga 1 ga Mayu. Kodayake, Gwamnatin ta ce kwamitin da ke da ruwa da tsaki kan batin ƙarin albashin bai kammala aikinsa ba tukuna. Ƙaramin Ministan Ƙwadago, Nkeiruka Onyejeocha, ita ce ta yi wannan babayin a wajen taron bikin Ranar Ma'aikata da aka shirya ranar Laraba a Abuja. Ta ce abin takaici ne ƙarin albashin bai kammalu ba zuwa wannan lokaci, amma cewa ana ci gaba da tattaunawa domin tabbatar dukkanin bayanai…
Read More
Shawara ga ‘yan uwa mata

Shawara ga ‘yan uwa mata

Daga SALIHA ABUBAKAR ABDULLAHI Assalamu alaikum. 'Yan uwa mata barkanmu da wannan lokaci. Allah Ya shirya mana zuri'a bakiɗaya. Zan yi amfani da wannan damar da na samu wurin yi mana tuni da kuma lurar da mu kan muhimmancin tarbiyya musamman a wannan zamanin da muka samu kanmu. Shawarata gare mu 'yan uwa mata dukka, duba da irin yanayin da muke ciki yanzun na taɓarɓarewar tarbiyya, 'yan uwa mu farka daga barci, mu san ƙima da darajojin da Allah SWT yai mana ba kaɗan ba ne, mu san ciwon kanmu, mu tashi tsaye wajen ganin ɗiyanmu sun samu tarbiyya ta…
Read More
Ki kame kanki ’yar uwa!

Ki kame kanki ’yar uwa!

A wannan zamani da muka tsinci kawunanmu ciki, mace wacce ta kame kanta daga aikata alfasha da nesantar shiga ta bayyana tsiraici, da ƙin kula samarin banza bisa hanya, ita ake wa kallon mace mai girman kai. To duk irin abinda al'ummah za su ce a kanki matuƙar kin kiyaye dokokin Allah, da yin koyi da mata salihan bayi na zamanin Manzon Allah (SAWW), kar ki tava damuwa, duk mai ƙaunarki da gaskiya, to ya bi tsarin neman aure yadda addini ya shar'anta domin ke ma'abociyar tsadace. Bayyana tsiraici alamu ne na fushin Allah, shi ya sa lokacin da Allah…
Read More