01
May
Tare da ABBA ABUBAKAR YAKUBU Littafi abu ne mai muhimmanci ga rayuwar ɗan adam, duba da yadda littafi ke taimakawa wajen adana muhimman bayanai da labarai da suka jiɓanci harkokin rayuwa daban-daban, kama daga tarihi, bayanan da suka shafi harkokin kimiyya da fasaha da tattalin arziki, tarihin ƙasa da muhimman mutane da al'adu da sauransu. Ranar littafi da kare 'yancin mallakar fasaha ta duniya ta samo asali ne tun a shekarar 1616 lokacin da aka yi rashin wasu fitattun marubuta irinsu Cervants, da Sharkspare da Inca Garcilaso de La vega. Kana a shekarar ce kuma aka samu wanzuwar wasu fitattun…
