Editor

9513 Posts
Kamfanonin waya sun nemi Tinubu ya ba su haɗin kai don tsauwala farashi

Kamfanonin waya sun nemi Tinubu ya ba su haɗin kai don tsauwala farashi

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Kamfanonin manyan layikan sadarwar da su ke aiki a Nijeriya, wato Glo, MTN, Airtel da 9Mobile, sun roƙi Gwamnatin Tarayya a karƙashin jagorancin Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ta sassauta wasu ƙa'idojin da ta saka wa kamfanonin, don ba su damar ƙara tsauwala farashin kuɗin kiran waya da na data. A cewar kamfanonin, tsarin kula da farashin na yanzu bai dace da yanayin matsin tattalin arziki ba, don haka suke neman taimakon gwamnati, don magance ƙalubalen farashin. Kamfanonin sadarwa guda huɗu sun ce, su kaɗai ne ba su yi ƙari kan farashinsu ba, wanda hakan ke…
Read More
EFCC ne ko FCCPC?

EFCC ne ko FCCPC?

Tare da NASIRU ADAMU EL-HIKAYA Daga makon jiya zuwa wannan makon a Nijeriya sunayen hukumomi biyu na Gwamnatin Tarayya sun yi ta bayyana a labaru. Kai tsaye hukumomin sun haɗa da hukumar yaqi da cin hanci wato EFCC da hukumar kare haƙƙin masu sayan kaya wato FCCPC. Hukumomin biyu sun bayyana a labaru ne don ayyukan da su ka gudanar a ɓangaren hurumin da ya shafi aikin su. Ga hukumar EFCC babban labarin da ya fito da sunan ta shi ne na yunƙurin cafke tsohon gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello. Ita kuma hukumar FCCPC ta dau matakan sauko da farashin…
Read More
Don kare Nijeriya daga faɗawa fatara ya sa na cire tallafin fetur — Tinubu

Don kare Nijeriya daga faɗawa fatara ya sa na cire tallafin fetur — Tinubu

Daga BASHIR ISAH Shugaban Ƙasa, Bola Tinubu, ya jaddada cewa matakin cire tallafin fetur da gwamnatinsa ta ɗauka abu ne da ya zama wajibi don hana ƙasar faɗawa cikin fatara. Tinubu ya bayyana haka a ne sa'ilin da yake jawabi a wajen taron tattalin arzikin duniya da ke gudana a birnin Riyadh na ƙasar Saudiyya a ranar Lahadi. Ya ce akwai buƙatar cire tallafin na fetur domin sake farfaɗo da tattalin arzikin ƙasar. Ta bakinsa, “Ga Nijeriya, mun yi amannar haɗin gwiwar tattalin arziki da haɗa kai ya zama dole don samar da kwanciyar hankali a sauran ƙasashen duniya. "Game…
Read More
Batun samar da ’yan sandan jihohi a Nijeriya

Batun samar da ’yan sandan jihohi a Nijeriya

Ƙirƙirar 'yan sandan jihohi dai ta kasance batun da ya daɗe ana muhawara a kai a Nijeriya. A ranar Litinin ne Majalisar Wakilan Nijeriya ta gudanar da taron jin ra’ayin jama’a kan maganar samar da ’yan sandan jihohi a faɗin ƙasar. An jima ana tafka muhawara kan batun samar da ’yan sandan jihohi a Nijeriya, sai dai a wannan karon majalisar ta fito ƙarara domin sanya zancen a bainar jama’a. Masu ruwa da tsaki da dama ne suka halarci taron a ranaf Litinin, ciki har da wasu tsofaffin shugabannin qasar da shugabannin addinai da sarakunan gargajiya da sauran su. Amma…
Read More
Ruwan sama da ’yan bindiga sun ruɗa Neja

Ruwan sama da ’yan bindiga sun ruɗa Neja

*Jama’a na tserewa saboda janye sojoji*Fursunoni 118 sun tsere daga kurkukun Suleja Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Jama’a sun yi hijira bayan an rufe sansanin soji da kuma janye sojoji da ke aikin samar da tsaro a ƙauyen Allawa da ke Ƙaramar Hukumar Shiroro ta Jihar Neja. Wannan ya zo ne a daidai lokacin da fursunoni guda 118 suka arce daga gidan yarin Suleja sakamakon mamakon ruwan saman da ya rikita gidan kurkukun. A ranar Alhamis ne sojojin Nijeriya suka rufe sansaninsu bayan bayar sa rahoton yi mu su kisan kiyashi, wanda ya janyo firgici a tsakanin al’ummar yankin…
Read More
American International School ta miƙa wa EFCC N1.1bn wanda Yahaya Bello ya biya wa ‘ya’yansa kuɗin makaranta

American International School ta miƙa wa EFCC N1.1bn wanda Yahaya Bello ya biya wa ‘ya’yansa kuɗin makaranta

Daga BASHIR ISAH Hukumar yaƙi da rashawa ta EFCC ta tabbatar da ta karɓi kuɗi $760,000 wanda Abuja American School ta maido a matsayin kuɗin makarantar da tsohon Gwamnan Jihar Kogiya, Yahaya Bello, ya biya wa 'ya'yansa. Mai magana da yawun EFCC, Dele Oyewale, shi ne ya bayyana hakan rabar Juma'a a Abuja. “Makarantar ta maido da $760,000 ga EFCC,” in ji shi Wannan na zuwa ne ƙasa da sa'o'i 24 bayan da makarantar da lamarin ya shafa ta buƙaci EFCC ta ba ta asusun da za ta yi amfani da shi wajen maido da kuɗin da Bello ya miƙa…
Read More
An gano matasa 1843 ɗauke da lalurar sikila a Jigawa

An gano matasa 1843 ɗauke da lalurar sikila a Jigawa

Daga UMAR AKILU MAJERI a Dutse Aƙalla matasa 1843 ne aka gano suna fama da larurar amosanin jini ko kuma sikila a faɗin Jihar Jigawa. Shugabar ƙungiyar masu fama da sikila ta Jihar Jigawa, zainab Shuaibu Koyawa, ita ce ta bayyana haka a zantawar da ta yi da manema labarai yayin taron bitar da aka shirya wa 'yan ƙungiyar a tsohuwar sakatariyar Gwamnatin Jihar wanda Kamfanin Global in Medicine Fellowship ya ɗauki nauyin ba da horon. Zainab ta ce kamfanin na Global zai horar da matasan da suke fama da sikila a ɓangaren zane-zane da calligraphy da kuma yadda ake…
Read More
Gwamnatin Jigawa ta ware N250m don gyara filin wasannin motsa jiki na Dutse – Eka

Gwamnatin Jigawa ta ware N250m don gyara filin wasannin motsa jiki na Dutse – Eka

Daga UMAR AKILU MAJERI a Dutse Gwamnatin Jihar Jigawa ta ware Naira miliyan 250 domin gyaran filin wasnnin motsa jiki na Dutse, hedikwatar jihar Jigawa . Gyaran fulin ya ƙunshi samar da ƙarin gine-gine irin na zamani da wurin dama da fitilu da dasa ciyawa irin ta zamani domin filin ya yi daidai da filin wasa na zamani da ake yayi a duniya. Shugaban ƙungiyar wasan ƙwallon kafa na Jihar Jigawa, Alh Sabo Abdullahi Eka, shi ne ya tabbatar da hakan a lokacin da yake ganawa da manema labarai a filin wasa na Dutse.  Eka  ya ce tuni gwamnatin Jihar…
Read More
Ministan Yaɗa Labarai ya kafa Kwamitin Kare Haƙƙoƙin Nakasassu

Ministan Yaɗa Labarai ya kafa Kwamitin Kare Haƙƙoƙin Nakasassu

Daga WAKILINMU Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Jama’a, Mohammed Idris, ya ba da umarnin kafa wani kwamiti mai mambobi biyar domin tsara aiki da hukumar nakasassu ta ƙasa domin wayar da kan jama’a game da ‘yancin nakasassu da kuma damar da suke da a rayuwa. Mataimaki na musamman ga ministan,Rabiu Ibrahim ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya raba wa manema labarai. Ministan ya bayar da wannan umarnin ne a ranar Laraba, a babban birnin tarayya Abuja, lokacin da ya karbi baƙuncin babban sakataren hukumar nakasassu na ƙasa, Dr. James Lalu, a wata ziyarar ban girma…
Read More
Sarkin Bade, Abubakar Umar ya hori masu hali su rinƙa taimakon mabuƙata

Sarkin Bade, Abubakar Umar ya hori masu hali su rinƙa taimakon mabuƙata

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Mai Martaba Sarkin Bade, Alhaji Abubakar Umar Suleiman III ya hori masu hannu da shuni da su ci gaba da taimakon mabuƙata duba da halin da ake ciki na tsadar rayuwa a ƙasar. Sarkin ya bayyana haka ne cikin makon da ya gabata a lokacin da yake tattaunawa da wakilinmu. Alhaji Abubakar Umar Suleiman ya ce a halin da ake ciki yanzu na taɓarɓarewar tattalin arziki, akwai buƙatar attajirai su da masu hali su dinga taimakon na ƙasa "domin ɗorewar zumunci da ƙaunar juna". Haka kuma mai martaba Sarkin Alhaji Abubakar Umar Suleiman, ya…
Read More