Editor

9513 Posts
Yadda babban kantin ƙasar Sin da ke Abuja ya hana ‘yan Nijeriya shiga

Yadda babban kantin ƙasar Sin da ke Abuja ya hana ‘yan Nijeriya shiga

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Wani babban kanti na kasar China da ke Abuja ya fuskanci suka bayan da aka ce ya hana kwastomomin Nijeriya shiga shagon. Babban kantin da ke Babbar Cibiyar Kasuwanci na ƙasar Sin, dake kan titin Umaru Musa Yar’adua a Abuja, an yaba shi a matsayin wurin da ake amfani da abinci da abin sha na ƙasar Sin. A cikin faifan bidiyo, ana iya ganin mutumin ɗan Nijeriya da ba a san ko wanene ba yana nuna ɓacin rai da kaɗuwa yayin da aka kore shi a ƙofar babban kantin. Rahotanni sun ce hukumar ta…
Read More
Yadda ‘yan bindiga suka kashe mutum uku, suka yi garkuwa da mutum takwas a Kaduna

Yadda ‘yan bindiga suka kashe mutum uku, suka yi garkuwa da mutum takwas a Kaduna

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja ‘Yan bindiga sun kashe mutane uku tare da sace wasu 8 a wasu hare-hare biyu a jihar Kaduna a ranakun Litinin da Talata. An yi garkuwa da mutanen ne a Unguwan Habuja da ke unguwar Kakangi a Ƙaramar Hukumar Birnin Gwari a jihar, inda kuma aka ce an kashe mutane biyu. Ƙauyen yana da tazarar kilomita uku daga garin Kakangi, inda mazauna ƙauyen suka ce harin bazata ne aka kai da yammacin ranar Talata. A cewar wani mazaunin garin, an kashe wani mutum a daya harin da ya faru a Gonan Alhaji Muntari da…
Read More
Mabiya Shi’a a Legas sun koka da ƙasashen Yahudawa bisa kisan gilla a Falasɗinu

Mabiya Shi’a a Legas sun koka da ƙasashen Yahudawa bisa kisan gilla a Falasɗinu

Daga DAUDA USMAN a Legas 'Yan uwa Musulmi al'majiran Sheikh Ibrahim Elzakzaki mabiya Shi'a da ke Jihar Legas mazauna Unguwar Mile-12 sun koka a game da abin da yake faruwa a ƙasar Falasɗinu na kashe-kashen rayukan al'ummar Musulmi da zubar da jini tare da jikkata waɗansu waɗanda ba su san hawa ba ballantana sauka kamar yadda Malam Abdullahi Ahmed wani babban malamin Shi'a a unguwar da sauran 'yan uwa Musulmi mabiya mazahabar Shi'a a Legas suka bayyana wa jaridar Blueprint Manhaja jim kaɗan bayan kammala taron su na walimar cin abincin ƙaramar Sallah ranar Larabar makon jiya. Babban Shehin malami…
Read More
 Binciken gwamnatin El-Rufai: Majalisar Kaduna ta gayyaci ma’aikatar kuɗin jihar ta bayyana gabanta

 Binciken gwamnatin El-Rufai: Majalisar Kaduna ta gayyaci ma’aikatar kuɗin jihar ta bayyana gabanta

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Kwamitin wucin gadi na majalisar dokokin jihar Kaduna da ke binciken yadda ake tafiyar da harkokin kuxi da kadarorin jihar a ƙarƙashin tsohon gwamna Nasir El-Rufai ya gayyaci kwamishinan kuɗi na jihar. Kwamitin na binciken yadda ake sayar da kadarorin gwamnati da basussukan da gwamnati ta karva a ƙarƙashin gwamnatin El-Rufai. Magatakardar majalisar, Sakinatu Idris, a cikin wata wasiƙa mai ɗauke da kwanan wata 22, Afrilu ta buƙaci ma’aikatar kuɗi ta bayyana a ranar Alhamis a gaban kwamitin wucin gadi da wasu takardu da suka shafi bayanan jimillar rancen da gwamnati ta karɓa tsakanin…
Read More
Gwamnatin Nijeriya ta ɗora alhakin katsewar lantarki a kan kamfanonin wuta da masu zagon ƙasa

Gwamnatin Nijeriya ta ɗora alhakin katsewar lantarki a kan kamfanonin wuta da masu zagon ƙasa

Daga SANI AHMAD GIWA a AbujaMinistan Wutar Lantarki, Adebayo Adelabu, ya yi tir da ayyukan ‘yan zagon ƙasa a harkar wutar lantarki, inda ya ɗora alhakin katsewar wutar lantarki a ƙasar nan a kansu. Mista Adelabu ya bayyana hakan ne yayin wani shiri mai taken “Confronting Nigeria’s Power Challenge as the Nation Migrates to Multi-Tier Electricity Market” a ranar Talata a Abuja. Kwamitin samar da wutar lantarki na majalisar wakilai ne ya shirya shirin. Ministan ya ce ‘yan zagon ƙasa da ‘yan daba suna aikata muggan laifuka ne don son kai domin daƙile yunƙurin tabbatar da samar da wutar lantarki…
Read More
Nijeriya za ta duba batun ƙarin kuɗin DSTV da GOtv

Nijeriya za ta duba batun ƙarin kuɗin DSTV da GOtv

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta ce, za ta duba batun ƙarin farashin da kamfanin MultiChoice, mamallakin tashoshin tauraron ɗan adam na DSTv da GOTv, ya yi kwanan nan ta hanyar masu ruwa da tsaki don tabbatar da walwawar Nijeriya da kuma ganin cewa sun more kuɗin su. Muƙaddashin Shugaban Hukumar Kula da Masu Sayayya ta Tarayya (FCCPC), Adamu Abdullahi, ya bayyana haka a gidan Talabijin na Channels a Abuja ranar Alhamis. A yayin tattaunawar, ya bayar da cikakken bayani kan sammacin da aka yi wa wani kantin sayar da kayayyaki na ƙasar Sin da ke Abuja da…
Read More
Shugaban EFCC bai yi wa Yahaya Bello adalci ba – Farfesa Chijioke

Shugaban EFCC bai yi wa Yahaya Bello adalci ba – Farfesa Chijioke

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Tsohon Mataimakin Shugaban Kotun ECOWAS, Farfesa Nwoke Friday Chijioke, ya yi kakkausar suka ga taron manema labarai da Shugaban Hukumar Yaqi da yi wa Tattalin Arziki Tu’annati (EFCC) ya gudanar, musamman dangane da tattaunawar da ya yi kan Yahaya Bello, tsohon Gwamnan jihar Kogi. Da ya ke magana a shirin 'Siyasa A Yau’ na gidan Talabijin na Channels, Farfesa Chijioke ya soki tsarin na EFCC, inda ya yi Allah wadai da shi a matsayin shari’ar da ba ta dace ba tare da bayyana ta a matsayin wani nau’i na shari’ar kafafen yaɗa labarai. Ya…
Read More
Kwankwaso zai ƙare rayuwarsa a fafutukar zama Shugaban Ƙasa – Lukman

Kwankwaso zai ƙare rayuwarsa a fafutukar zama Shugaban Ƙasa – Lukman

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Tsohon Mataimakin Shugaban Jam'iyyar APC na Arewa Maso Yamma, Malam Salihu Lukman, ya ce, hanyar da Kwankwaso ya ke bi ta kaiwa ga Fadar Shugaban Ƙasa "za ta ɗauke shi shekaru masu tarin yawa wurin tattaunawa da jama'a a sassan Nijeriya, wanda zai iya wuce lokacinsa na rayuwa ma”. Lukman, wanda ya kasance baƙo a shirin siyasar gidan Talabijin na Channels a ranar Laraba, ya ce jam’iyya mai mulki za ta iya hanzarta aiwatar da muradin Kwankwaso ta hanyar buɗe masa ƙofar jam’iyyar domin ya dawo ya sake gina gada da aka ƙona a…
Read More
Mutum 10 sun mutu a haɗarin jiragen sama masu saukar ungulu a Malaysia

Mutum 10 sun mutu a haɗarin jiragen sama masu saukar ungulu a Malaysia

Mutane 10 ne suka mutu a lokacin da wasu jirage masu saukar ungulu na sojojin Malaysia biyu sun yi karo da juna, yayin wani atisaye da suke yi. Babban jami’in gudanarwa na hukumar kwana-kwana da aikin ceto ta ƙasar, Suhaimy Mohamad Suhail ne ya tabbatar da faruwar lamarin. Firaministan ƙasar Anwar Ibhrahim ya miƙa saƙon ta’aziyarsa ga iyalan waɗanda suka rasa rayukansu a haɗarin da ya bayyana a matsayin mai tada hankali, inda ya ce za a gudanar da bincike don gano musabbabin faruwansa. An gayamin cewar ma’aikatar kula da harkokin tsaro za ta gudanar da bincike, musammanma rundunar sojojin…
Read More
Ɗalibai masu nazarin kiwon lafiya za su fara cin albashi a Jigawa

Ɗalibai masu nazarin kiwon lafiya za su fara cin albashi a Jigawa

Daga UMAR AKILU MAJERI a Dutse Gwamnatin Jihar Jigawa ta sanya ɗalibai masu nazarin kiwon lafiya a kan tsarin albashin wata-wata da yake biyan ma'aikata. Gwamnati ta ɗauki wannan mataki ne da nufin ƙara wa ɗaliban da lamarin ya shafa ƙwarin gwiwa don ganin ta samar da likitoci masu nagarta a jihar. Kamar yadda bayanai daga ma'aikatar lafiya suka nuna, waɗanda za su ci moriyar shirin sun haɗa da ɗaliabai masu karatun likitanci(MBBS) 38 da ɗaliban Physiotherapy 14 da ɗaliban Pharmacy 15 da ɗaliban Med. Lab 12 da ɗaliban Dental Therapy 17 da ɗaliban Nursing 15 da ɗaliban Radiography 4,…
Read More