Ɗalibai masu nazarin kiwon lafiya za su fara cin albashi a Jigawa

Daga UMAR AKILU MAJERI a Dutse

Gwamnatin Jihar Jigawa ta sanya ɗalibai masu nazarin kiwon lafiya a kan tsarin albashin wata-wata da yake biyan ma’aikata.

Gwamnati ta ɗauki wannan mataki ne da nufin ƙara wa ɗaliban da lamarin ya shafa ƙwarin gwiwa don ganin ta samar da likitoci masu nagarta a jihar.

Kamar yadda bayanai daga ma’aikatar lafiya suka nuna, waɗanda za su ci moriyar shirin sun haɗa da ɗaliabai masu karatun likitanci(MBBS) 38 da ɗaliban Physiotherapy 14 da ɗaliban Pharmacy 15 da ɗaliban Med. Lab 12 da ɗaliban Dental Therapy 17 da ɗaliban Nursing 15 da ɗaliban Radiography 4, dai kuma ɗaliban da kuma ɗaliban BDS 3.

Kwamishinan Lafiya, Dr. Abdullahi A. Kainuwa, ya tabbatar da hakan a alokacin da yake miƙa takardar yarjejeniya ga ɗaliban da suka kai matakin aji huɗu a ɓangarorin karatun da ya shafi kiwon lafiya.

Kainuwa shi ne ya jagoranci miƙa wannan takarda ta hawa matakin albashin ga ɗaliban su 129 da suka fito daga sassa daban-daban na jihar.

Jami’in ya hori ɗaliban da lamarin ya shafa da su jajirce da karatu domin ba da tasu gudunmawa ga cigaban jihar.