Nijeriya za ta duba batun ƙarin kuɗin DSTV da GOtv

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta ce, za ta duba batun ƙarin farashin da kamfanin MultiChoice, mamallakin tashoshin tauraron ɗan adam na DSTv da GOTv, ya yi kwanan nan ta hanyar masu ruwa da tsaki don tabbatar da walwawar Nijeriya da kuma ganin cewa sun more kuɗin su.

Muƙaddashin Shugaban Hukumar Kula da Masu Sayayya ta Tarayya (FCCPC), Adamu Abdullahi, ya bayyana haka a gidan Talabijin na Channels a Abuja ranar Alhamis.

A yayin tattaunawar, ya bayar da cikakken bayani kan sammacin da aka yi wa wani kantin sayar da kayayyaki na ƙasar Sin da ke Abuja da ake zargin sa da nuna wariya ga ’yan ƙasa.

Ya kuma yi tsokaci game da bin dokokin da aka kafa wa Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki ta Abuja, inda ya bayyana cewa akwai shirin sanya takunkumi ga duk wasu ire-iren su da hukumar ta gano.

MultiChoice, babban gidan talabijin na tauraron ɗan adam a yankin kudu da hamadar sahara da ke da hedikwata a ƙasar Afrika ta kudu, a baya-bayan nan ya sanar da ƙarin farashin ayyuka a DSTV da na GOtv, yana mai cewa ƙarin farashin ya zama dole saboda hauhawar farashin ayyukan kasuwanci.

A cewar kamfanin, ƙarin zai fara aiki ne a ranar 1 ga Mayu, 2024.

Tsarin Premium na DSTV wanda a baya farashinsa ya kai Naira 29,500, yanzu zai koma Naira 37,000, yayin da tsarin Compact Plus da ke kan Naira 19,800 a halin yanzu an kara shi zuwa Naira 25,000.