27
Apr
Daga BASHIR ISAH Ƙasar Falasɗinu ta bayyana cewa Amurka ta ƙi amince mata ta zama cikakkiyar mamba a Kwamitin Sulhu na Majalisar Ɗinkin Duniya. Jakadan Falasɗinu a Nijeriya, Abdullah M. Abu Shawesh, shi ne ya bayyana haka cikin sanarwar manema labarai da ya fitar mai ɗauke bayyanada kwanan wata 25 ga Afrilun 2024. Sanarwar ta ce sama da kwanaki 200 ke nan da fara kisan ƙare dangin da ake yi wa Falasɗinawa. A cewar Shawesh, "A ranar 19 ga Afrilu, Amurka ta ƙi amincewa da buƙatar Falasdinawa ga kwamitin sulhu na Majalisar Ɗinkin Duniya na samun cikakken mamba da zama…
