Editor

9513 Posts
Garin Alawa a Neja ya kama hanyar zama kufai saboda rashin tsaro

Garin Alawa a Neja ya kama hanyar zama kufai saboda rashin tsaro

Daga BASHIR ISAH Al'ummar garin Alawa da ke Ƙaramar Hukumar Shiroro a Jihar Neja, na ci gaba da ficewa daga garin saboda tsoron barazanar 'yan bindiga. Wannan na faruwa ne sakamakon janye jami'an tsaro da aka yi daga yankin alhalin yankin na daga wuraren da ke fuskantar barazanar 'yan ta'adda a jihar. Ya zuwa yanzu gwamnatin jihar ba ta ce komai kan batun ba. Majiyarmu ta ce muddin hukumomi ba su yi wani abu kan batun ba, yankin Alawa zai za zama kufai nan ba da daɗewa ba.
Read More
Gwamnan Sakkwato ya tuɓe rawanin hakimai 15

Gwamnan Sakkwato ya tuɓe rawanin hakimai 15

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Gwamnatin Sakkwato ta sallami hakimai 15 bisa zargin su da taimakawa rashin tsaro, satar filaye da sauran laifuka. An sallami hakimai 9 daga muqamansu bisa zargin su da rashin biyayya da taimakon rashin tsaro da satar filaye da kuma karkatar da dukiyar jama’a da rashin ɗa’a. Waɗanda aka sallama sun haɗa da hakiman Uguwar Lalle, Yabo, Wamakko, Tulluwa, llela, Dogon Daji, Kebbe, Alkammu, da kuma Hakimin Gyawa. Gwamnatin jihar ta kuma sauke wasu hakimai shida da tsohuwar gwamnatin jihar ta naɗa. Abubakar Bawa, Sakataren yaɗa labarai na Gwamna Ahmed Aliyu, ya bayyana cewa an…
Read More
Jam’iyyun siyasa na shirin ƙalubalantar sojojin Mali a gaban kotun ƙoli

Jam’iyyun siyasa na shirin ƙalubalantar sojojin Mali a gaban kotun ƙoli

Ƙungiyoyin fararen hula da jam’iyyun siyasa a Mali sun buƙaci kotun ƙoli kan ta umarci gwamnatin sojin ƙasar da ta dakatar da haramcin da ta yi game da gudanar da harkokin siyasa.  A wata sanarwa da suka fitar, ƙungiyoyin fararen hular da jam’iyyun siyasa da ke adawa da umarnin Sojojin, sun yi ƙorafi ga babbar kotun ƙasar ta Mali, suna neman a soke hukuncin da suke ganin take haƙƙin ɗan adam ne. Tun a shekarar 2021 ne sojoji a Mali suka yi juyin mulki karo na biyu, inda suka yi alƙawarin gudanar da zaɓe a watan Fabrairun da ya gabata…
Read More
Xavi ya yi amai ya lashe kan batun barin Barcelona

Xavi ya yi amai ya lashe kan batun barin Barcelona

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Kocin Barcelona, Xavi Hernandez ya sauya shawararsa na barin Barcelona a ƙarshen kakar wasa ta bana kuma zai ci gaba da zama koci bayan tattaunawa da shugaban kulob ɗin, Joan Laporta, da shugabannin ƙungiyar a ranar Laraba. An ruwaito Xavi ya gana da shugaban ƙungiyar, Joan Laporta da daraktan wasanni, Deco, a daren Laraba. Bayan taron ya sauya ra'ayi kuma ya amince da sharuɗɗan ci gaba da jagorantar ƙungiyar ta LaLiga. Ƙwararre a harkar wasan ƙwallon aafa Fabrizio Romano ya bayyana hakan a shafinsa na X. Romano ya rubuta: Xavi ya yanke shawarar canja ra'ayinsa ya…
Read More
Tsananin zafi: An buƙaci mutane su dauki matakan kariya na kiwon lafiya

Tsananin zafi: An buƙaci mutane su dauki matakan kariya na kiwon lafiya

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano A halin da ake ciki na yanayin tsananin zafi, an yi kira ga al’umma da su ɗauki matakan kariya na kiwon lafiya domin kare lafiyarsu daga faɗa wa haɗari. Kwamishinan Lafiya na Jihar Kano, Dakta Abubakar Labaran Yusuf ne ya yi kiran a cikin wata sanarwar manema labarai da ma'aikatarsa ta fitar ranar Alhamis wadda aka raba wa manema labarai. Sanarwar wadda ta sami sa hannun Ibrahim Abdullahi, Dakta Labaran ya ce yanayin zafin da ake ciki ya fara ne tun daga watan Maris na wannan shekara, wanda ya sanya ƙaruwar zazzaɓi da mace-mace, ya…
Read More
Fursunoni 118 sun tsere bayan da ruwan sama ya lalata gidan yari a Neja

Fursunoni 118 sun tsere bayan da ruwan sama ya lalata gidan yari a Neja

Daga BASHIR ISAH Rahotanni daga garin Suleja a Jihar Neja sun ce, aƙalla fursunoni 119 ne suka tsere daga gidan yarin Suleja biyo bayan ruwan sama mai ƙarfi da aka samu a garin a daren Laraba wanda ya lalata wani sahshe na gidan yarin. Mai magana da yawun Hukumar Kula da Gidajen Yari na yankin FCT, Adamu Duza ya tabbatar da aukuwar hakan cikin wata sanarwa da ya fitar da safiyar Alhamis. Ya ce, “Ruwan sama mai ƙarfi da aka yi na awanni masu yawa a ranar Laraba, 24 ga Afrilun 2024, ya haifar da akasi a matsakaicin gidan yarin…
Read More
Tasgaron zuwan Turawa Ƙasar Hausa

Tasgaron zuwan Turawa Ƙasar Hausa

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Duk da irin alfanu da muka zayyana waɗanda suka samu a Ƙasar Hausa sakamakon zuwan Bature, ba kuma za a rasa tasgaro, cigaban mai haƙar rijiya, da kuma koma baya waɗanda zuwan Turawa ya haifar ba. Tabbataccen abu ne a tsarin rayuwa, cewa, duk lokacin da aka samu sauyi ko cuɗanya da wasu baƙin jama’a, waɗanda tasirinsu ya kai ga wata jama’ar ta sauya salon yadda take gudanar da rayuwarta, babu makawa, sai an samu abubuwan da za su saɓa da abin da yake karɓaɓɓe a tafarkin rayuwar waɗannan jama’a da aka zo aka taras. Zuwan…
Read More
Yana da kyau marubuta su ƙirƙiro da hanyar mayar da rubutunsu kan sauti – Farfesa Sufyan Wase

Yana da kyau marubuta su ƙirƙiro da hanyar mayar da rubutunsu kan sauti – Farfesa Sufyan Wase

"Ya kamata marubuta su riƙa tafiya da zamani" Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU Marubuta sun kasu kashi daban-daban. Akwai marubutan labaran hikaya, akwai marubutan tarihi, akwai marubutan faɗakarwa, akwai kuma na ilimi. Sufyanu Adamu Yakubu mai laƙabi da Farfesan Marubuta, marubucin kalmomin hikima ne da faɗakarwa, musamman abin da ya shafi zamantakewa da tarbiyya. Kasancewarsa malamin makaranta, hakan ya taimaka masa wajen yin rubuce-rubuce da suka shafi ilimi da cigaban rayuwa. A zantawarsa da Abba Abubakar Yakubu, Farfesan ya bayyana burinsa na zama cikakken Farfesa na gaske, kuma mawallafin littattafan kimiyya. A yi karatu lafiya. MANHAJA: Zan so ka fara gabatar…
Read More
Majalisar Dokokin Kano ta amince da naɗin Lawan Badamasi matsayin Kwamishinan KANSIEC

Majalisar Dokokin Kano ta amince da naɗin Lawan Badamasi matsayin Kwamishinan KANSIEC

Daga RABIU SANUSI Kwamitin tantance abinda ya shafi harkokin zaɓe a Majalisar Dokokin Jihar Kano ƙarƙashi shugabancin Rt. Hon Jibrin Falgore, ta kammala tantace Alhaji Lawan Badamasi, wanda aka ambata a mastayin sabon Kwamishinan Zaɓe na Jihar Kano ta miƙa dukkan bayanai ga zauren majalisar don dubawa. Majalisar ta bayyana hakan ne a lokacin da take zamanta, a yayin da shugaban kwamitin, Hon Murtala Muhammad Kadage mai wakiltar Garko ya ce, wanda aka wanda naɗin ya shafa ya cancanta da matsayin kwamishinan zaɓen na jiha. Injiniya Murtala Kadage ya kuma ce, cancantar Badamasin yana dai-dai da abin da kundin tsarin…
Read More
Gwamnan Kano ya isa Amurka don halartar taron zaman lafiya

Gwamnan Kano ya isa Amurka don halartar taron zaman lafiya

Daga RABIU SANUSI Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano ya isa ƙasar Amurka domin halartar babban taron tattaunawa da Cibiyar Zaman Lafiya ta Amurka ta shirya a ranar Talatar da ta gabata Wannan na ƙunshe ne a wata sanarwar da Darakta-Janar mai kula da harkokin yaɗa labarai na gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya sanyawa hannu. Bature ya ce, taron na kwanaki uku da gwamnonin Kano, Katsina, Zamfara, Kaduna, Niger, Sokoto, Kebbi, Jigawa, Plateau ke halarta, an shirya shi ne domin magance matsalar rashin tsaro a Arewacin Nijeriya da kuma mafi kyawun zaɓi na daƙile ƙalubalen. "Haɗin kai mai…
Read More