Editor

9513 Posts
Ta’addanci na haifar da illa musamman ga mata — Amina Mohammed

Ta’addanci na haifar da illa musamman ga mata — Amina Mohammed

Daga WAKILINMU Mataimakiyar Sakatare Janar ta Majalisar Ɗinkin Duniya, Amina Mohammed, ta jaddada muhimmancin magance matsalolin ta'addanci da tallafa wa al'ummomin da abin ya shafa a faɗin Afirka. Mataimakiyar ta bayyana haka ne a yayin da aka yi wani taro na yaƙi da ta’addanci da aka gudanar a ranar Litinin a Birnin Tarayya Abuja. Ofishin Mai Ba Da Shawara kan Harkokin Tsaro (ONSA) tare da hadin gwiwar ofishin yaƙi da ta'addanci na Majalisar Dinkin Duniya UNOCT ne suka shirya. Taron ya aka yi wa taken 'Karfafa Hadin Gwiwar Yanki Da Ci Gaban Cibiyoyi Don Tinkarar Barazanar Ta'addanci a Afirka'. Amina…
Read More
Hankalina na tashi idan na ga wanda baya da abin ci da iyalinsa – Aunty Sadiya Kaduna

Hankalina na tashi idan na ga wanda baya da abin ci da iyalinsa – Aunty Sadiya Kaduna

"Burina in ga maraya cikin farin ciki kamar kowa" Daga AISHA ASAS Hajiya Sadiya Abdullahi wadda mutane da yawa suka fi sani da Antin KD, kuma wadda ta kasance 'yar gwagwarmaya da fafutikar ganin marayu da gajiyayyu sun ɗanɗana irin daɗin da masu iyaye da masu hali suke ji a rayuwarsu, ta fuskar tallafa masu da abinci, suturu, da kuma ƙoƙarin inganta lafiyarsu ta hanyar gidauniyar ta. A cikin tattaunawar ta da jaridar Blueprint Manhaja za ku ji wacce ce ita, gwagwarmayar ta da kuma sirrin shaharar ta. MANHAJA: Bari mu fara da jin taƙaitaccen tarihinki. SADIYA KADUNA: Assalamu alaikum.…
Read More
Zan yi murabus muddin ba a hukunta Yahaya Bello ba — Shugaban EFCC

Zan yi murabus muddin ba a hukunta Yahaya Bello ba — Shugaban EFCC

Daga BASHIR ISAH Shugaban Hukumar Yaƙi da Rashawa ta EFCC, Ola Olukoyede, ya lashi takobin bin diddigin zargin almundahanar Naira biliyan 80.2 da ake yi wa tsohon Gwamnan Jihar Kogi, State Yahaya Bello har zuwa ƙarshe. Olukoyede ya furta haka ne a hirar da ya yi da manema labarai a Babban Ofishin hukumar da ke Abuja, inda ya ce babu makwa zai yi murabus muddin ba a hukunta Bello ba. "Idan ni da kaina ban ga ƙarshen wannan binciken game da Yahaya Bello ba, zan a jiyen' muƙamina a matsayin Shugaban EFCC Chairman,” in ji Olukoyede. Ya ce Bello ya…
Read More
Yadda rabuwar aure ke kawo damuwa ga iyalai

Yadda rabuwar aure ke kawo damuwa ga iyalai

Tare da ABBA ABUBAKAR YAKUBU Zaurukan sada zumunta sun ɗauki hankali a makon da ya gabata, sakamakon wasu maganganu da fitaccen jarumin Kannywood kuma mawaƙi Adam A. Zango ya yi a wani ƙaramin bidiyo da ya ɗora a shafinsa, a matsayin martani ga masu yaɗa maganganu marasa daɗi a kansa. Tun bayan da jarumin finafinan Hausan ya sanar da rabuwa da matarsa ta baya-bayan nan surutai suke yawa a kansa, ana zarginsa da rashin iya riƙon aure, ko kuma auri-saki, kasancewar duk matan da ya aura ba sa jimawa tare da shi ake rabuwa, bisa wasu dalilai daban-daban. Ɓacin ran…
Read More
Tarihin Daular Usmaniyya ba zai cika ba sai da Ummarunmu Alkammu – Sa’idu Mu’azu Alkammawa

Tarihin Daular Usmaniyya ba zai cika ba sai da Ummarunmu Alkammu – Sa’idu Mu’azu Alkammawa

Daga AISHA ASAS A ranar Asabar ɗin da ta gabata ne aka yi taro mafi girma a tarukan sada zumunta da ke gudana a Jihar Sakkwato, kasancewarsa taro mafi tara mutane da suka haɗa lungu da saƙo na jihar har ma da baƙi daga wasu jihohi. Dalilin kenan da duk girman ɗakin taron da aka ɗauka bai iya kwashe kashi biyu cikin ukun malaharta taron ba. Ummarunmu Alkammu bai kasance mutumin da ke buƙatar doguwar gabatarwa ba musanmman ga masana tarihi, wanda za mu iya cewa, duk inda aka juya a tarihin Daular Usmaniyya to fa ya cancanci a ambaci…
Read More
NDE ta horas da matasa 50 dabarun noma da kiwo a Jigawa

NDE ta horas da matasa 50 dabarun noma da kiwo a Jigawa

Daga UMAR AKILU MAJERI a Dutse Hukumar Samar da Aikin yi ta Ƙasa, NDE, reshen Jihar Jigawa, ta zaɓo matasa maza da mata su 50 daga sassan jihar tare da ba su horo a kan harkar noman rani da kiwon dabobi da kiwon kaji da noman kifi da nufin inganta rayuwarsu. Matasan da suka ci gajiyar shirin sun haɗa maza 20 da mata 30. Shugaban NDE a jihar, Alhaji Sa'adu Iya Yarima, shi ne ya shaida wa manema labarai haka jim kaɗan bayan kammala bai wa matasan da lamarin ya shafa horo a cibiyar hukumar da ke Jigawa . Yarima…
Read More
Da Ɗumi-ɗumi: EFCC ta tsare Hadi Sirika kan almundahanar N8bn

Da Ɗumi-ɗumi: EFCC ta tsare Hadi Sirika kan almundahanar N8bn

Daga BASHIR ISAH Hukumar yaƙi da rashawa ta EFCC, ta tsare tsohon Ministan Sufurin Jirgin Sama, Hadi Siriki, sakamakon binciken da take gudanarwa kan badaƙalar karkatar da biliyan N8,069,176,864.00 na Kamfanin Nigeria Air. Jaridar Punch ta rawaito tsohon Ministan ya isa ofishin EFCCda ke Abuja da misalin ƙarfe 1:00 na rana a ranar Talata, 23 ga Afrilun 2024. Majiyarmu ta ce, bayan da ya isa ofishin na EFCC, an yi ea Sirika tambayo kan wasu kwangiloli da ake zargin ya bayar bisa ƙa'ida ba ga kamfanin Engirios Nigeria Limited mallakar wani ƙaninsa, Abubakar Sirika. Majiya ta kusa da EFCC wadda…
Read More
Bayan shekara 26, tsohon Gwamnan Imo, Emeka Ihedioha ya fice daga PDP

Bayan shekara 26, tsohon Gwamnan Imo, Emeka Ihedioha ya fice daga PDP

Daga BASHIR ISAH Bayan shafe shekara 26 a matsayin mabiyin jam'iyyar PDP, tsohon Gwamnan Jihar Imo, Emeka Ihedioha, ya sauya sheƙa daga jam'iyyar zuwa wata. Ihedioha ya ce ya fice daga jam'iyyar ta PDP ne bisa ra'ayinsa. A cewarsa, abin takaici ne ganin yadda PDP ta ɗare kan turbar da ta saɓa wa ra'ayinsa. Ya ce, "Duk da ƙoƙarin da na yi na bai wa jam'iyyar shawarwari, jam'iyyar ta kasa samar da sauye-sauyen cigaba a cikin gida, tabbata ra da kiyaye dokokinta, ko kuma zama 'yar hamayya mai ƙarfi ga jam'iyyar APC mai mulki. “Bisa wannan dalili ne na rage…
Read More
Maza masu dukan mata

Maza masu dukan mata

Tare da AMINA YUSUF ALI Masu karatu barkanmu da sake haɗuwa a wani makon a filinmu mai albarka, Zamantakewa na jaridarku mai farin jini ta Blueprint Manhaja. Yanzu za mu ci gaba a kan maudu'in da muka saba kawo muku wato nasiha kan zamantakewa, wato a wani maudu'inmu mai suna Maza masu dukan mata. Mun fara kawo muku wasu daga dalilan da suke jawo maza su yi duka, da muma dalilina na ganin bai kamata a ɗora musu laifi ba. Yanzu za mu ci gaba daga inda muka tsaya. A sha karatu lafiya. To dalilin na biyu da nake ganin…
Read More
Yaƙi da Ta’addanci: Akwai buƙatar samar da dakarun yanki don daƙile safarar makamai — Tinubu

Yaƙi da Ta’addanci: Akwai buƙatar samar da dakarun yanki don daƙile safarar makamai — Tinubu

Daga BASHIR ISAH Shugaban Ƙasa Bola Tinubu, ya jaddada kira kan samar da dakarun yanki masu zamn ko-ta-kwana a matsayin kayan aikin magance dukkan matsalolin tsaron da ake fuskanta a yanzu da ma waɗanda ka iya tasowa a gaba a yankin Afirka Kazalika, ya ce samar da dakarun zai taimaka ainun wajen daƙile safarar makamai a tsakanin ƙasashen Afirka. Tinubu ya bayyana haka ne sa'ilin da yake jawabi a wajen buɗe babban taron yaƙi da ta'addanci a Afirka wanda aka shirya ranar Litinin a Abuja. Shugaban ya ƙara da cewa, ya zama wajibi a kawo ƙarshen ta'addanci a yankin Afirka…
Read More