Editor

9513 Posts
Gwamnatin Tinubu za ta haramta wa ɗalibai ‘yan ƙasa da shekara 18 neman gurbin karatu a manyan makarantu

Gwamnatin Tinubu za ta haramta wa ɗalibai ‘yan ƙasa da shekara 18 neman gurbin karatu a manyan makarantu

Daga BASHIR ISAH Gwamnatin Tarayya ƙarkashin jagorancin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ta ce tana shirin haramta wa ɗalibai 'yan ƙasa da shekara 18 nan gurbin karatu a jami'o'i da sauran manyan makarantu da ke faɗin Nijeriya. Ministan Ilimi Farfesa Tahir Mamman ne ya bayyana haka a lokacin da yake yi wa manema labarai ƙarin haske a lokacin da yake zagayen duba yadda jarrabawar UTME ta 2024 ke gudana a wasu cibiyoyin rubuta jarrabawar ranar Litinin a Abuja. Ministan ya bayyana rashin jin daɗinsa bisa ƙarancin shekarun wasu daga cikin ɗaliban da ya gani suna rubuta jarrabawar, yana mai cewa shekarunsa…
Read More
Gwamna Lawal ya jaddada buƙatar amfani da fasahar zamani wajen yaƙi da rashin tsaro

Gwamna Lawal ya jaddada buƙatar amfani da fasahar zamani wajen yaƙi da rashin tsaro

Daga NASHIR ISAH Gwamna Dauda Lawal na Jihar Zamfara ya jaddada buƙatar da ke akwai ta amfani da fasahar zamani wajen yaƙi da rashin tsaro a Jihar da ma yankin Arewa baki ɗaya. Lawal ya bayyana haka ne a wajen taron da shi da wasu takwarorinsa suka yi da Mataimakiyar Sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya, Amina J. Mohammed, ranar Juma'a a Washington, D.C. Mahalarta taron sun haɗa da gwamnonin Zamfara da Benue da Jigawa da Kaduna da Katsina da Kebbi da kuma Neja, kamar yadda mai magana da yawun Gwamnan Zamfara, Sulaiman Bala Idris, ya bayyana cikin sanarwar da ya fitar…
Read More
Manyan ’yan siyasa sun kira ni sanadin maganata, inji Adam Zango

Manyan ’yan siyasa sun kira ni sanadin maganata, inji Adam Zango

Daga AISHA ASAS A satuka buyu da suka gabata, fitaccen jarumi a Masa’antar Kannywood, Adam A. Zango ya bayyana a kafar sada zumunta na TikTok da bayyanai da za mu iya kira da tura ta kai bango, duk da cewa wasu da yawa na kallon faifan bidiyon na Zango a matsayin ishara ga abinda zai iya faruwa da shi nan gaba idan ba a ɗauki mataki ba, wanda wannan tunanin ne ya sa hankullan masoyan jarumin suka ta shi, yayin da suka shiga aika masa da saƙon nuna soyayya da goyon baya gare shi. Jarumi Adam ya nuna takaicinsa ta…
Read More
Ina ‘ya’yanku suka je yawon sallah?

Ina ‘ya’yanku suka je yawon sallah?

Daga AISHA ASAS Masu karatu barkanmu da yau, barkanmu da ganin ƙarshen watan alfarma, kuma barkanmu da sallah. Allah Ya karɓi ibadunmu, Ya sa mun dace, Ya kuma maimaita mana. A satin farko na sallah aka samu wata 'yar muhawara game da yawon sallah da yaranmu ke yi musamman ma mata. Inda wani ya yi zancen tururuwar da yara maza da shekarunsu bai haura 17 zuwa 19 ke yi wurin siyan kwararon roba a lokacin abin tayar da hankali ne. Da wannan ne wasu suka yi wa wannan kalaman ca, inda suke ƙaryata shi tare da nisanta yaran da abinda…
Read More
‘Yan sandan Kenyan sun cika hannu da shugaban Binance da ya tsere daga Nijeriya

‘Yan sandan Kenyan sun cika hannu da shugaban Binance da ya tsere daga Nijeriya

Daga BASHIR ISAH 'Yan Yaƙi da Manyan Laifuka na Ƙasa da Kasa, sun damƙe shugaban kamfanin Binance, Nadeem Anjarwalla, a ƙasar Kenya. MANHAJA ta tattaro cewar, 'yan sandan na nan suna shirin miƙa Anjarwalla ga Gwamnatin Nijeriya bayan kammala ɓangarensu. Majiya ta kusa da gwamnati wadda ba ta amnince a ambaci sunanta ba, ita ce ta tabbatar da kama Anjarwalla ran Lahadi da daddare. Idan za a iya tunawa, MANHAJA ta rawaito Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta bayyana cewa ta gano inda tserarren shugaban Binance da ya tsere, Nadeem Anjarwalla ya ɓoye. Gwamnatin ta ce, ta gano Anjarwalla yana ƙasar Kenya…
Read More
Jigawa za ta yi wa yara miliyan ɗaya allurar riga-kafin shan inna

Jigawa za ta yi wa yara miliyan ɗaya allurar riga-kafin shan inna

Daga UMAR AKILU MAJERI a Dutse Gwamnatin Jihar Jigawa ta shirya tsab don yi wa ƙananan yara su miliyan ɗaya da rabi allurar rigakafin shan inna a matsayin ƙoƙarin da gwamnatin jihar ke yi na hana cutar ɓulla a jihar. Darakta a hukumar lafiya matakin farko, Dakta Shehu Sambo, shi ne ya sanar da hakan ga taron manema labarai jim kaɗan bayan ƙaddamar da shirin allurar na bana a fadar Sarkin Dutse, Alhaji Hamim Nuhu Muhammed Sunusi a ranar Litinin. Jami'in ya ce yara miliyan ɗaya da rabi ake sa sunasa ran za su amshi allurar a fadɗn Jihar. Ya…
Read More
Yadda bikin Hawan Daushe ya laƙume rayuka huɗu a Bauchi

Yadda bikin Hawan Daushe ya laƙume rayuka huɗu a Bauchi

Daga BAKURA MUHAMMAD a Bauchi Mutane huɗu ne cikinsu har da ɗan wani fitaccen hakimi aka kashe a wani taho-mugama da ya auku a tsakanin wani gungun abokan adawa biyu yayin da ake yin Hawan Daushe na ƙaramar Salla a garin Bauchi. Taho-mugamar ta kuma haifar da raunuka ga wasu jama'a mabiya tawagar mahaya dawaki dake cikin jerin gwano hawan na daushe, wadda mai Martaba Sarkin Bauchi, Dokta Rilwanu Suleiman Adamu yakan yi kashegarin sallah, walau Eid-el fitr ko Eid-el Kabir na kowace shekara. Gungun abokan adawar biyu sune da ta 'Yan-Babeli, wacce zaunanniya ce dake bayar da gudummawa kan…
Read More
Kotun Tarayya ta soke dakatarwar da aka yi wa Ganduje

Kotun Tarayya ta soke dakatarwar da aka yi wa Ganduje

*Ɗan Ganduje ya yaba wa gwamnatin Kano bisa tuhumar mahaifinsa Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Babbar Kotun Tarayya da ke Kano ta jinjine dakatarwar da aka yi wa Shugaban Jam’iyyar APC na Ƙasa, Abdullahi Ganduje, a mazabarsa. Mai Shari’a Abdullahi Liman ya umarci shugabannin Mazaɓar Ganduje da ke Ƙaramar Hukumar Dawakin Tofa, kada su yi aiki da umarnin babbar kotun jihar na dakatar da shugaban jam’iyyar. Umarnin Babbar Kotun Tarayyar na zuwa ne awa 24 da babbar kotun jihar ta amince da bukatar shugabannin mazavar ta dakatar da tsohon gwamnan jihar, saboda gwamnatin jihar mai ci na zarginsa da…
Read More
EFCC na son tsoma sojoji a dambarwa EFCC da Yahaya Bello

EFCC na son tsoma sojoji a dambarwa EFCC da Yahaya Bello

Daga MAHDI M. MUHAMMAD A ranar Larabar da ta gabata ne dai tsohon Gwamnan Jihar Kogi, Alhaji Yahaya Bello, ya yi kira ga Shugaban Qasa Bola Tinubu da ya ja wa Hukumar Yaƙi da Masu yi wa Tattalin Arzikin Ƙasa Zagon Ƙasa ta EFCC kunne bisa zargin ƙin bin umarnin kotu, wacce ta hana a kama shi. To, sai dai kuma a ranar Alhamis Hukumar ta EFCC ta bayyana cewa, ta na duba yiwuwar tsoma rundunar sojojin Nijeriya a cikin dambarwar, don kamo shi ɗin. Tsohon gwamnan, a wata sanarwa da jami’in yaɗa labaransa, Mista Onogwu Muhammed, ya fitar a…
Read More
Yadda wasu yara biyar suka mutu lokaci guda a Neja

Yadda wasu yara biyar suka mutu lokaci guda a Neja

Daga BASHIR ISAH Wasu yara biyar sun mutu a cikin wata mota da suka shiga suna wasa, inda motar ta kulle kanta suka kasa fita. Lamarin wanda ya faru a ranar Lahadi, an ce an sha famar neman yaran a unguwa alhali ba a san cewa suna kulle cikin motar ba, daga bisani aka gano su baki ɗayansu a mace. Shafin Tsalle Ɗaya ya ce iftila'in ya faru ne a Unguwar Albishiri da ke daura da yankin Gurara a hanyar Bida, Minna, Jihar Neja. Majiyarmu ta ce huɗu daga cikin yaran mata ne, sannan ɗaya namiji. An ce uku daga…
Read More