Editor

9513 Posts
Gobe Tinubu zai ƙaddamar da taron yaƙi da ta’addanci a Afirka

Gobe Tinubu zai ƙaddamar da taron yaƙi da ta’addanci a Afirka

Daga WAKILINMU A gobe Litinin, 22 ga watan Afrilu idan Allah y'Ya kai mu, Shugaban Ƙasa Bola Tinubu zai buɗe taron yaƙi da ta’addanci a Afirka wanda za a yi a Abuja. Nijeriya tare da goyon bayan ofishin yaƙi da ta'addanci na Majalisar Ɗinkin Duniya (UNOCT) ce ta shirya wannan taro wanda aka yi masa laƙabi da "Ƙarfafa Dangantakar Nahiyar Afirka Don Gina Cibiyoyin Taron Dangin Magance Barazanar Ta'addanci''. Maƙasudin taron na kwana ɗaya shi ne inganta haɗin gwiwar yaƙi da ta'addanci a ɓangarori daban-daban tsakanin ƙasashen yankin, tare da sake fasalin rawar da ƙasashen duniya ke takawa kan batun…
Read More
‘Yan bindiga sun kashe sojoji shida a Neja

‘Yan bindiga sun kashe sojoji shida a Neja

Daga BASHIR ISAH 'Yan bindiga a jihar Neja sun bindige sojoji guda shida da wani maharbi ɗaya. Hakan ya faru ne sakamakon hare-haren da 'yan bindigar suka kai yankunan Karaga da Rumace a gundumar Bassa da ke cikin ƙaramar hukumar Shiroro a jihar. Majiyarmu ta ce lamarin ya ritsa da wasu manoma biyu da suka mutu, sai kuma gidaje da rumbuns'a da babura da aka ƙona yayin harin. Bayanai sun ce harin ya fara ne da misalin ƙarfe 9 na dare a ranar Juma'ar da ta gabata. Sauran yankunan jihohin da suka yi fama da hare-haren ta'addanci sun haɗa Allawa,…
Read More
ASUU ta buƙaci Gwamnatin Tarayya ta sake kafa Majalisar Gudanarwar Jami’ar Sakkwato

ASUU ta buƙaci Gwamnatin Tarayya ta sake kafa Majalisar Gudanarwar Jami’ar Sakkwato

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Ƙungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU), reshen Jami’ar Usmanu Danfodiyo ta Sakkwato, ta buƙaci Gwamnatin Tarayya da ta gaggauta sake kafa Majalisar Gudanarwar Jami'ar. A wata sanarwa da shugaban reshen, Farfesa Mohammed Almustapha, ya fitar, kuma ya raba wa manema labarai a ranar Juma’a, ASUU ta yi Allah-wadai da rusa dukkan kwamitin jami'ar da gwamnatin tarayya ta yi, saboda karya dokar jami’o’i. Sanarwar ta bayyana damuwa kan rusa shugabannin jami’o’in tarayya ba bisa ƙa’ida ba a watan Yunin 2023 da Hukumar Kula da Jami’o’i ta ƙasa ta yi, biyo bayan umarnin da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bayar.…
Read More
Owowoh Princess ta zama ’yar Nijeriya ta farko da ta kammala Kwalejin Sojojin Birtaniya

Owowoh Princess ta zama ’yar Nijeriya ta farko da ta kammala Kwalejin Sojojin Birtaniya

Daga MAHDI M. MUHAMMAD A ranar Juma'a ne Owowoh Princess Oluchukwu, ta zama mace ta farko ’yar Nijeriya da ta kammala karatu a Kwalejin Sojoji ta Sandhurst da ke Birtaniya. Oluchukwu mai shekaru 24, ta kasance ɗaya daga cikin jami'an Cadets 135 da suka kammala karatu yayin wani fareti da aka shirya a birnin Landan a ranar ta Juma'a. A shekarar 2018, Princess ta shiga makarantar horar da sojoji ta Nijeriya (NDA), a Jihar Kaduna. Tun a shekarun 1950, hafsoshin Nijeriya da dama da suka haɗa da tsohon shugaban Nijeriya Yakubu Gowan da shugaban hukumar leqen asiri ta tsaro, Manjo…
Read More
Iran ta rama harin Isra’ila a Damaskas?

Iran ta rama harin Isra’ila a Damaskas?

Tare da NASIRU ADAMU EL-HIKAYA Babban labarin da ke ɗaukar hankalin duniya a yanzu shi ne harin da ƙasar Iran ta kai da makamai masu linzami da jirage marasa matuƙa kan Isra'ila. Da ma an yi wa duniya kirari da "Duniya mai yayi" in za ka ga a na batun wani sai kwatsam a jingine a shiga wani sabo. Daga bara zuwa bana an ga yadda a ka yi labarin fitinar Sudan tsakanin Janar Abdelfatah Burhan da Hamdan Hameti Daglo bayan an fara gajiya da harin mamaye Yukrain da Rasha ta yi. Ga batun fitinar Yaman tun 2014 bayan 'yan…
Read More
Birnin Leverkusen ya bai wa ɗan Nijeriya, Boniface, shaidar zama ɗan ƙasa

Birnin Leverkusen ya bai wa ɗan Nijeriya, Boniface, shaidar zama ɗan ƙasa

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Majalisar Birnin Leverkusen ta bai wa Victor Boniface, Nathan Tella da sauran zakarun gasar Bundesliga takardar shaidar zama ɗan qasa na girmamawa. A ranar Lahadi Bayer Leverkusen ta lashe gasar Bundesliga ta farko bayan da ta lallasa Werder Bremen da ci 5-0 inda Victor Boniface ya zura ƙwallon farko sannan kuma ya taimaka aka zura sauran ƙwallayen. Victor Boniface yana ɗauke da fasfo na Nijeriya, yayin da Tella baya ga koren fasfo ɗinsa kuma yana da fasfo na ƙasar Birtaniya kamar yadda iyayen Nijeriya suka haife shi a Ingila.
Read More
Nijeriya ta gano inda tserarren Shugaban Binance ya ɓoye a Kenya

Nijeriya ta gano inda tserarren Shugaban Binance ya ɓoye a Kenya

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta bayyana cewa ta gano inda tserarren shugaban Binance da ya tsere, Nadeem Anjarwalla ya voye. Gwamnatin ta ce, ta gano Anjarwalla yana ƙasar Kenya bayan tserewar shugaban Binance daga kulle Nijeriya a kwanakin baya. Dalilin haka ne ma ya sa hukumar EFCC da rundunar 'yan sandan Nijeriya da na Kenya suka fara tattaunawa kan yadda za a dawo da shi Nijeriya. Anjarwalla bayan tserewarsa ya gudu ne ƙasar Kenya domin gujewa hukunci. Wata majiya daga fadar shugaban ƙasa ta tabbatar da haka inda ta ce ana ƙoƙarin dawo da shi Nijeriya. "Mun…
Read More
Masu burin kassara PDP ke adawa da shugabancin Umar Damagun – Biniya Gabari

Masu burin kassara PDP ke adawa da shugabancin Umar Damagun – Biniya Gabari

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano An zargi wasu ‘yan majalisar wakilai 60 na PDP da wasu ƙungiyoyin da ke nuna adawa da shugabancin Ambasador Umar Iliyasu Damagun a matsayin shugaban riƙo na jam’iyyar na ƙasa, da kasancewa karnukan farauta ne da ake amfani da su wajen yin zagon ƙasa ga ci gaban jam’iyyar. Shugaban haɗakar matasa na jam’iyyar na ƙasa PDP Youths Collation Movement Hon. Biniya Yahuza Gabari ya bayyana haka. Ya ƙara da cewa ‘ya’yan  jam'iyyar su ke ƙalubalantar shugaban riƙo na jam'iyyar PDP na da   ɓoyayyen manufa na ruguza jam’iyyar ne, ganin yanda yanzu take samun ƙarin goyon…
Read More
Akwai masu zuga ni na binciki Gwamna Abba – Muhuyi Magaji

Akwai masu zuga ni na binciki Gwamna Abba – Muhuyi Magaji

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Shugaban Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta Jihar Kano (PCACC), Malam Muhuyi Magaji, ya ce wasu mutane na bincikensa domin ƙoƙarin tunzura shi ya binciki Gwamna Abba Kabir. Magaji ya bayyana haka ne yayin da ya halarci shirin Sunrise Daily na gidan talabijin Channels ranar Talata, 16 ga watan Afrilu, 2024. Jami'in ya ce, ya fara binciken shugaban jam’iyyar APC na qasa, Dr. Abdullahi Ganduje, a lokacin da yake kan kujerar gwamnan Jihar Kano. Shugaban hukumar yaƙi da rashawar, wanda ya jaddada cewa ya zama tilas jami'an gwamnati su kiyaye bin doka da oda,…
Read More
Dalilin da ya sa na daina saka baki a siyasar Nijeriya – Rotimi Amaechi

Dalilin da ya sa na daina saka baki a siyasar Nijeriya – Rotimi Amaechi

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Tsohon Ministan Sufuri a Nijeriya Rotimi Amaechi ya ce an daina jin ɗuriyarsa ne a fagen siyasar Nijeriya saboda "babu wani sabon abu" da zai faɗa. Tsohon gwamnan na jihar Ribas ya riƙe muƙamin minista a gwamnatin tsohon Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari daga 2015 zuwa 2022, bayan ya mulki jihar tasa a Kudancin Nijeriya tsawon shekara takwas. "Babu wani sabon abu kwatakwata," inji ɗan siyasar wanda ya nemi takarar shugaban ƙasa a jam'iyyar APC mai mulki cikin hira ta musamman da BBC. "Abubuwan da ake so na yi magana a kan su suna nan…
Read More