20
Apr
Daga MAHDI M. MUHAMMAD Al'ummar Maiduguri, babban birnin Jihar Borno, sun samu kansu a cikin wani yanayi yayin da aka tsinci gawar wani sifeton ’yan sandan a gidansa. Marigayi jami’in (da aka sakaya sunansa) da ke aiki a sashin Gwange na rundunar ’yan sandan jihar Borno an gansa ne kwanaki uku da suka wuce kafin a gano gawarsa a gidansa da safiyar Asabar. Maqwabtansa a Layin Bayan, unguwar Wulari Jerusalem a Maiduguri, sun ɗaga murya wajen kiransa a lokacin da suka lura ya kulle ƙofarsa ta baya, amma wani ɗoyi na fitowa daga gidan. Nan take aka kai rahoton lamarin…
