Daga IBRAHIM HAMISU, a Kano
Saratu Abubakar da aka fi sani da Hajiya Karama, a cikin ga a cikin fim cin ‘Kwana 90’ ce baƙuwar shafin Nishaɗi na wannan makon. A tattaunawar ta da Ibrahim Hamisu a Kano, za ku ji tarihinta da kuma yadda aka yi ta tsunduma masana’antar Kannywood. Ku biyomu:
MANHAJA: Za mu so ki gabatar mana da kanki?
HAJIYA ƘARAMA: Sunana Saratu Abubakar, ni ‘yar asalin Niger ce a garin Suleja, an haife ni a yankin Gauraka, na yi Primary da Secondry a nan, sannan na yi NCE a Niger State College of Education Minna, inda na kammala a shekarar 2014, a yanzu haka ina Jami’ar Bayero aji na biyu inda nake karanta English/Education.
Ta yaya kika samu kanki a masanartar Kannywood?
Yadda akai na fara fim, na farko dai akwai sha’awa, na biyu kuma gaskiya abin zai zama kamar da wasa domin akwai wani group na ƴan Suleja da nake ciki, akwai wani wani ɗan Kannywood Aminu Maje to ana hira a group to sai ya ce ga su a hanyar Abuja za su je ɗaukar fim cin ‘Hajiya Babba’, kamar wasa sai na ce mu kuma yan Suleja a me za mu fito a fim ɗin? Kawai sai ya yi min magana ta ‘private’ ya ce, idan ina sha’awa so na yi masa magana, akwai wasu sinasinai da za a iya ware min, na ce masa zan yi. Ya ce ba damuwa to ka ji daga inda na fara.
Da wane fim kika fara?
fim ɗin ‘Hajiya Babba’ shi ne fim ɗina na farko da na fara, wanda muka yi da marigayi Rabilu Musa Ibro da AK da Baba mai Aya.
A wacce shekara kenan kika fara?
A shekarar 2014 a lokacin na dawo gida mun gama jarrabawa, muna hutun zangon karatu na farko, shi ne a lokacin aka kai ni Abuja, da na gama sin ɗin da aka ba ni shi ne na dawo gida.
To ya aka yi kika dawo Kano da zama?
A shekarar 2020 ne na dawo Kano, da ya ke ina da ‘yar uwa a nan Kano, kuma dama ina zuwa Kano sarin kaya, amma bayan na samu aiki da fim ɗin ‘Kwana 90’ ne sai na dawo Kano. Da ya ke a Jigawa ake ɗaukar fim ɗin ‘Kwana 90’, to mutum ya je ya yi aiki yau sai a ce gobe ya koma, to ganin irin nisan da ke akwai tsakanin Jigawa da Suleja, hakan ya sa babbar yayata ta ce na dawo Kano da zama wajen ƴar uwata. Da kuma dalilin karatu, ka ji dalilin dawowata Kano.
Ya aka yi kika samu aka ɗauke ki a cikin shirin ‘Kwana 90’ kin san wani a a tashar Arewa 24 ne?
Da ya ke ni gaskiya ina yawan yin magana a social media, Duk wanda yake yi yasan ni, domin ina da yawan surutu. To a lokacin akwai wani bidiyo da muka yi da ƙawata Hajara Haidar, to bidiyon ya yi tashe a lokacin, da yake ita ƙawata cin tasan daraktan ‘Kwana 90’, wato Bozy, to da ya ga bidiyon sai ya tambaye ta wacce ce wannan gaskiya tana da surutu?
Sai ta ce ai qawata ce, sai ya shiga shafi na ya ga ire-iren bidiyon da nake yi, sai ya gaya mata cewa gaskiya an samu ‘actress’, to sai ya karɓi lambata a hannunta ya yi min magana, muka riƙa magana da shi ana nan wannan sai na yi masa magana na ce, darakta tunda ina da kai ya kamata ace muna cikin ‘Kwana 90’, sai ya ce dama ina son fim ne? Na ce masa ai ni dama ‘actress’ ce, ya ce, to ba damuwa.
To a season na huɗu kawai sai ya turo min ‘script’ sai na je na yi audition, shikenan sai aka ɗauke ni.
Zaki iya tuna wani wuri da ya baki wahala a wajen ɗaukar shirin a fim ɗin ‘Kwana Casa’i’?
Gaskiya kamar babu, saboda sinasinaina ba su da yawa, duk da ya ke yanzu za ka ga sun fara yawa. Amma akwai wani wuri a zango na shida, da na kasa riƙe maganar, maganganun suna da tsawo, har sai da ya ce na kusa ba shi matsala, don haka wannan ne kawai za a iya cewa ya ba ni wahala.
Mun gode.
Ni ma na gode.
