ASUU ta yi barazanar shiga yajin aikin gama-gari

Ƙungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU), ta yi barazanar shiga yajin aiki na gama-gari domin nuna rashin jin daɗinta kan tshin samun majalisar gudanarwa a ɗaukacin Jami’o’in Gwamnatin Tarayya da ke faɗin ƙasa da sauran buƙatu.

Ƙungiyar ta ce idan za a iya tunawa, a watan Mayun bara ne gwamnatin ta sauke majalisar gudanarwa na Jami’o’in, tare da cewa duk matakin da ta ɗauka dangane da hakan ‘yan Nijeriya su kama gwamnati da laifi.

Shugaban ASUU na ƙasa, Farfesa Emmanuel Osodeke ya yi wannan bayani yayin taron manema labarai da ya shirya a sakatariyar ASUU da ke Abuja a ranar Talata.