13
Feb
Daga FATUHU MUSTAPHA Gwamnan Jihar Bauchi Sanata Bala Mohammed, ya ce Fulani makiyaya kan riƙe bindiga ne saboda kare kai. Gwamnan ya faɗi a haka ne a lokacin da yake magana a wajen taron bikin Makon 'Yan Jarida wanda Reshen Wakilai na Ƙungiyar 'Yan Jarida a Jihar Bauchi ya shirya. Ya riƙe bindiga kan taimaka wajen hana ɓarayi su kai musu hari su kashe su sannan su yi gaba da shanunsu. Yana mai cewa gazawar gwamnati wajen bai wa makiyayan kariya shi ya ya sa su kuma suka ɗauki matakin kare kansu daga ta'addancin 'yan ta'adda. "Saboda shi Bafulatani mutum…
