Galibin makiyayan da ke halaka mana mutane ba ‘yan Nijeriya ba ne, inji Ortom

Daga BASHIR ISAH

An bayyana cewa galibin makiyayan da ke halaka mutane a ƙasar nan ba ‘yan asalin Nijeriya ba ne.

Bayanin haka ya fito ne ta bakin Gwamna Samuel Ortom na jihar Binuwai yayin wani taron manema labarai da ya gudana a Abuja a ranar Alhamis da ta gabata.

Ortom ya yi kira ga Shugaba Muhammadu Buhari da ya buƙaci a sake waiwayar dokokin ECOWAS don yin gyarar fuska dangane da sha’anin zirga-zirgar mutane da kayayyaki a nahiyar Afirka.

Ya ce makiyaya daga wajen Nijeriya na amfani da damar zirga-zirga wajen ruruta matsalolin tsaro.

Ta bakinsa, “Ƙasashe maƙwabta irin Ghana da Benin, sai an ɗauki bayanan mutane kafin a bari su shiga ƙasa. Kamata ya yi a riƙa ɗaukar bayanan masu sha’awar shiga Nijeriya kafin a ƙyale su su shigo. Wannan tsari nan a cikin dokokin ECOWAS na karanta na gani, haka ma lauyoyina za su karanta.

“Galibin makiyayan da kashe mana mutane ba ‘yan Nijeriya ba ne, hatta shi kansa Shugaban Ƙasa ya faɗi haka yayin da ya ziyarci Daular Larabawa.”

Da yake tsokaci kan alfanun dokar hana kiwo barkatai a Jihar Binuwai, Ortom ya ce majalisar dokokin jihar ita ce silar zaman lumanar da ake gani yanzu a Binuwai.

Yana mai cewa, “Tun bayan da wannan doka ta soma aiki mun kama tare da hukunta makiyaya sama da 400 da suka ƙi yin aiki da dokar. Wasunsu an ci su tara an sake su, wasunsu kuma har yanzu suna tsare a gidan kaso a Makurɗi.”