Oyo: An gano manomi a mace a gonarsa

Daga AISHA ASAS

An gano wani manomi mai suna Bashiru Akinlota mace a gonarsa da ke Itigbo a hanyar Apodun, Igangan a cikin ƙaramar hukumar Ibarapa ta Arewa a jihar Oyo.

Binciken Manhaja ya gano cewa wannan al’amari ya auku ne a Larabar da ta gabata bayan da marigayin ya fahimci gonarsa ta koko da kashu ta kama da wuta inda ya je don kashe wutar.

Bayanai sun nuna marigayin ɗan shekara 65, ya yanke jiki ne ya faɗi a daidai lokacin da ya yi ƙoƙarin kashe wutar da ta kama gonarsa.

Kwamandan Rundunar Tsaro ta Amotekun a Oyo, Col Olayinka Olayanju (mai murabus) ya tabbatar cewa ba makiyaya ne suka kashe marigayin ba, haka ma ba wani ne ya kashe shi ba.