Editor

9513 Posts
Tsohon gwamnan Legas ya rasu

Tsohon gwamnan Legas ya rasu

Daga AISHA ASAS Allah ya yi wa gwamnan farar hula na farko a jihar Legas, Lateef Kayode Jakande rasuwa. Marigayin ya bar duniya yana da shekara 91. A halin rayuwarsa, Jakande wanda tohon ɗanjarida ne, ya yi gwamna a Jihar Legas daga 1979 zuwa 1983. Haka nan, ya riƙe muƙamin Ministan Ayyuka a zamanin mulkin marigayi Sani Abacha. An haifi marigayin ne a ranar 23 ga Yulin 1929, a Legas. Gwamnan Legas, Babajide Sanwo-Olu, ya nuna alhinin dangane da rasuwar, tare da bayyana marigayin a matsayin babban rashi.
Read More
Hukumar Kwastam ta kama haramtattun kayayyaki

Hukumar Kwastam ta kama haramtattun kayayyaki

Daga WAKILIN MU Ofishin Hukumar Yaƙi da Fasa-ƙwauri ta Ƙasa na 'Zone C', ya ce ya samu nasarar kama kayayyakin da aka haramta shigo da su cikin ƙasa wanda harajinsu ya haura milyan N869 a Janairun da ya gabata. Kayayyakin da ofishin ya ce ya kama ciki har da katan 1,024 na magungunan da ba a yi musu rajista ba, da shinkafar ƙetare buhu 1,046, da katan 62 na sabulun, da mota ƙirar Toyota da dai sauransu. A cewar Comptroller Yusuf Lawal, haƙƙinsu ne tabbatar da cewa ana kiyaye dukkan ƙa'idojin da gwamnati ta shimfiɗa dangane da haramcin shigo da…
Read More
Jami’ar Bauchi ta yi sabon suna

Jami’ar Bauchi ta yi sabon suna

Daga AISHA ASAS Majalisar Zartarwa ta Gwamnatin Jihar Bauchi ta aminta da batun sauya wa Jami'ar Bauchi, Gadau, suna zuwa Jami'ar Sa'adu Zungur. Sanarwar da Kwamishinan Ilimin Jihar Bauchi, Dr. Aliyu U. Tilde ya fitar, ta nuna an ɗauki matakin sauya wa jami'ar suna ne domin raya sunan marigayi Sa'adu Zungur (1915-1958) a matsayinsa na ɗaya daga cikin mazan jiya da suka bada gudunmawarsu wajen samun 'yancin kan ƙasa. A halin rayuwarsa, Malam Sa'adu Zungur ya riƙe muƙamin sakataren NCNC, ɗan gwagwarmayar sisaya ne wanda basirarsa ta yi tasiri wajen daidaita harkar siyasar Arewa, har wa yau mutum ne wanda…
Read More
BUA ya saya wa Nijeriya rigakafin korona guda milyan ɗaya… da magana – inji CACOVID

BUA ya saya wa Nijeriya rigakafin korona guda milyan ɗaya… da magana – inji CACOVID

Daga FATUHU MUSTAPHA Fitaccen kamfanin nan BUA Group, ya saya wa Nijeriya maganin rigakafin cutar korona guda milyan ɗaya a matsayin gudunmawarsa ga ƙasa wajen yaƙi da annobar korona. Bayanai sun nuna BUA ya sayi maganin ne tare da haɗin guiwar haɗakar masu taimaka wa Gwamnatin Nijeriya da saurarnsu wajen yaƙi da koro da aka fi sani da CACOVID a taƙaice. Ana sa ran magani ya iso Nijeriya a mako mai zuwa wanda idan hakan ya tabbata, a iya cewa shi ne ya zama rigakafi na farko da Nijeriya ta samu tun bayan ɓullar annobar korona. Kamfanin BUA ya ce…
Read More
Tsohon ɗanwasan Super Eagles ya rasu

Tsohon ɗanwasan Super Eagles ya rasu

Daga WAKILIN MU Tsohon ɗan wasan Super Eagles Yisa Sofoluwe, ya rasu. Sofoluwe ya rasu ne a Talatar da ta gabata a Asibitin Koyarwa ta Jami'ar Legas bayan fama da ya yi da lalurar ƙwaƙwalwa. Tun farko sai da aka kai marigayin wata asibiti a yankin Ikorodu kafin daga bisani aka ɗauke shi zuwa asibitin jami'ar Legas. A halin rayuwarsa, marigayin ya buga wa Nijeriya wasa da dama, ciki har da gasar cin kofin Afirka (AFCON) a 1984 da 1988. Haka nan, ya samu zarafin buga ma wasu manyan ƙungiyon ƙwallon ƙafa na ƙasa, irin su 3SC da Julius Berger…
Read More
A shirye muke mu samar wa makiyaya wuraren kiwo –   Gwamnonin Arewa

A shirye muke mu samar wa makiyaya wuraren kiwo – Gwamnonin Arewa

Daga AISHA ASAS Gwamnonin Arewa sun yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta tallafa musu da kuɗaɗen da za su yi amfani da su wajen samar da gandun dazazzuka a sassan yankinsu don amfanin makiyaya. Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin Arewa kuma gwamnan jihar Filato Simon Lalong shi ne ya yi wannan kira yayin wani shirin talabijin da aka yi da shi a Talatar da ta gabata. Yana mai cewa, da dadewa gwamnonin Arewa sun yi na'am da shirin samar da gandun dazuzzukan. Ya ce duba da yadda harkokin sace sacen mutane ke ta ƙaruwa da kuma batun umarnin ficewa da aka…
Read More
Buhari ya ƙaddamar da aikin layin dogo daga Kano Zuwa Nijar

Buhari ya ƙaddamar da aikin layin dogo daga Kano Zuwa Nijar

Daga BASHIR ISAH A Talatar da ta gabata Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya ƙaddamar da aikin gina layin dogo wanda zai tashi daga Kano-Katsina-Jibiya-Maraɗi, da kuma wanda zai ratse zuwa Dutse a jihar Jigawa. Da yake jawabi ta bidiyo daga fadarsa da ke Abuja yayin bikin ƙaddamawar, Buhari ya ce bayan kammala aikin hakan zai taimaka wajen bunƙasa harkokin tattalin arzikin ƙasa musamman ma hada-hadar kasuwanci a tsakanin Nijeriya da Nijar. Daga nan ya kira ga 'yan kasuwa da su yi amfani da wannan dama wajen gudanar da harkokin kasuwancin da ba su saɓa wa dokoki ba da nufin bunƙasa…
Read More
Yawan masu zaɓe a Nijeriya ya tsaya tsakanin kashi 30 zuwa 35 cikin ɗari – inji INEC

Yawan masu zaɓe a Nijeriya ya tsaya tsakanin kashi 30 zuwa 35 cikin ɗari – inji INEC

Daga WAKILIN MU Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta bayyana cewa yawan masu zaɓe a Nijeriya bai fi kashi 30 zuwa 35 cikin ɗari na waɗanda su ka yi rajista a zagaye biyu na zaɓuɓɓukan da aka yi na baya-bayan nan ba. Shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, shi ne ya bayyana haka a wajen taron tuntuɓa na farko da hukumar ta shirya tare da ƙungiyoyi masu zaman kan su (CSOs) na shekarar 2021 wanda aka yi a ranar Talata a Abuja. Yakubu ya ce a yayin da wasu zaɓuɓɓukan sun fi samu yawan fitowar masu zaɓe, a wasu kuma ba…
Read More
Zan taimaki Nijeriya wajen yaƙi da matsalolin tsaro muddin na lashe zaɓe – inji Bazoum

Zan taimaki Nijeriya wajen yaƙi da matsalolin tsaro muddin na lashe zaɓe – inji Bazoum

Daga WAKILIN MU A makon da ya gabata ne ɗan takarar Shugaban Ƙasar Nijar ƙarkashin jam'iyyar PNDS Tarayya, Alhaji Mohammed Bazoum, ya kai wa Shugaba Muhammadu Buhari ziyara ta musamman a Daura domin neman goyon bayansa. Yayin ziyarar, Buhari da Bazoum sun tattauna muhimman batutuwa ciki har da batun takarar Bazoum da batun kwararar ɓatagari daga Nijar zuwa Nijeriya da kuma akasin haka. Haka nan tattaunawar tasu ta taɓo batun matsalolin tsaron da Nijeriya ke fama da su da zimmar Bazoum zai taimaka wa Buhari wajen yaƙi da matsalolin idan ya lashe zaɓe mai zuwa. Bazoum bai bar Nijeriya ba…
Read More
Hukuma ta yi ɗamarar farfaɗo da birnin Abuja

Hukuma ta yi ɗamarar farfaɗo da birnin Abuja

Daga FATUHU MUSTAPHA Duba da yadda ayyukan ɓata-gari irin sace-sace da lalata kadarorin gwamnati da na ɗaiɗaikun mutane ke ta ƙaruwa a ƙwaryar birnin Abuja, hakan ya sanya Hukumar Abuja ƙarƙashin jagorancin Ministan Abuja, Malam Muhammad Musa Bello ta kafa kwamiti na musamman da zai tattara bayanan adadin ɓarnar da aka tafka. Sakataren Hukumar Abuja, Engr. Umar Gambo Jibrin, shi ne ya jagoranci ƙaddamar da kwamitin a ranar Litinin. Babban aikin da aka ɗora wa kwamitin shi ne, ya zagaya birnin Abuja kaf tare da tattara bayanan da suka danganci lalata kadarori da sace-sacen kayayyaki da suka faru a birnin…
Read More