Hukuma ta yi ɗamarar farfaɗo da birnin Abuja

Daga FATUHU MUSTAPHA

Duba da yadda ayyukan ɓata-gari irin sace-sace da lalata kadarorin gwamnati da na ɗaiɗaikun mutane ke ta ƙaruwa a ƙwaryar birnin Abuja, hakan ya sanya Hukumar Abuja ƙarƙashin jagorancin Ministan Abuja, Malam Muhammad Musa Bello ta kafa kwamiti na musamman da zai tattara bayanan adadin ɓarnar da aka tafka.

Sakataren Hukumar Abuja, Engr. Umar Gambo Jibrin, shi ne ya jagoranci ƙaddamar da kwamitin a ranar Litinin.

Babban aikin da aka ɗora wa kwamitin shi ne, ya zagaya birnin Abuja kaf tare da tattara bayanan da suka danganci lalata kadarori da sace-sacen kayayyaki da suka faru a birnin da nufin gyara na gyarawa da kuma hana aukuwar hakan a gaba.

Kwamitin wanda zai gudana ƙarƙashin shugabancin Daraktan Ayyuka na Musamman na Hukumar Abuja, Arc. Eze C. Sunday, na da makonni huɗu ne kacal don ya kammala aikin da aka ɗora masa.

Domin cim ma nasarar aikinsa kwamitin ya tsinto jami’ai daga ɓangarori daban-daban waɗanda za su yi aiki tare don haƙa ta ci ma ruwa.

Don haka ne ma kwamitin ya sake kakkafa wasu ƙananan tawagogi har guda goma don su yi aiki a gundumomi biyar da ake da su a birnin Abuja, inda za su zagaya saƙo-saƙo don tattara bayanan da ake buƙata. Kwamitin ya nemi haɗin kan mazauna Abuja don taimaka masa wajen iya sauke nauyin da aka ɗora masa.

Hukumar Abuja ta ce tana sa ran maida kayayyakin da aka sace da ma waɗanda aka lalata kafin saukar damina domin sake raya birnin ya koma kamar yadda aka san shi a baya.

Duka waɗannan bayanai na ƙunshe ne cikin wata takardar bayani wadda aka raba wa manema labarai ta hannun sakataren kwamitin, Richard A. Nduul, wadda Manhaja ta samu nata kwafin.