Jami’ar Bauchi ta yi sabon suna

Daga AISHA ASAS

Majalisar Zartarwa ta Gwamnatin Jihar Bauchi ta aminta da batun sauya wa Jami’ar Bauchi, Gadau, suna zuwa Jami’ar Sa’adu Zungur.

Sanarwar da Kwamishinan Ilimin Jihar Bauchi, Dr. Aliyu U. Tilde ya fitar, ta nuna an ɗauki matakin sauya wa jami’ar suna ne domin raya sunan marigayi Sa’adu Zungur (1915-1958) a matsayinsa na ɗaya daga cikin mazan jiya da suka bada gudunmawarsu wajen samun ‘yancin kan ƙasa.

A halin rayuwarsa, Malam Sa’adu Zungur ya riƙe muƙamin sakataren NCNC, ɗan gwagwarmayar sisaya ne wanda basirarsa ta yi tasiri wajen daidaita harkar siyasar Arewa, har wa yau mutum ne wanda Malam Aminu Kano ya riƙa a matsayin gwaninsa kuma mawaƙi ne shi.

Ma’aikatar ilimin jihar ta nuna farin cikinta kan yadda gwamnan jihar da majalisarsa suka taimaka mata wajen cika alƙawarin da ta ce ta ɗaukar wa iyalan marigayin wajen samar da abin da zai taimaka wajen hana sunan marigayin macewa.

Sanarwar kwamishinan ta nuna hatta shi kansa Gwamnan Bauchi, Sanata Bala Abdulƙadir Mohammed, ya yi matuƙar farin ciki da faruwar hakan.

Tare da cewa Majalisar Dokokin Jihar ta taka muhimmiyar rawa wajen cim ma nasarar sauya sunan jami’ar zuwa Sa’adu Zungur. Inda kwamishinan ke da tabbacin majalisar za ta sallama da zarar an kammala shirye-shirye aka kai batun gabanta.

Tilde ya ce wannan al’amari ne wanda tarihin ilimi a jihar Bachi ba zai taɓa mancewa da shi ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *