Hukumar Kwastam ta kama haramtattun kayayyaki

Daga WAKILIN MU

Ofishin Hukumar Yaƙi da Fasa-ƙwauri ta Ƙasa na ‘Zone C’, ya ce ya samu nasarar kama kayayyakin da aka haramta shigo da su cikin ƙasa wanda harajinsu ya haura milyan N869 a Janairun da ya gabata.

Kayayyakin da ofishin ya ce ya kama ciki har da katan 1,024 na magungunan da ba a yi musu rajista ba, da shinkafar ƙetare buhu 1,046, da katan 62 na sabulun, da mota ƙirar Toyota da dai sauransu.

A cewar Comptroller Yusuf Lawal, haƙƙinsu ne tabbatar da cewa ana kiyaye dukkan ƙa’idojin da gwamnati ta shimfiɗa dangane da haramcin shigo da shinkafa da sauran kayayyaki daga ƙetare.

Don haka ya ce za su ci gaba da inganta matakan aikinsu don ci gaba da yaƙar harkokin fasa-ƙwauri a kan ruwa da tudu a yankin Kudu maso-kudo da Kudu maso-gabas.

Jami’in ya bada tabbacin cewa za su ci gaba da hana ‘yan fasa-ƙwauri sakewa ta yadda kullum za su kasance cikin tafka hasara.

Lawal ya yi yabo tare da nuna godiyarsa ga takwarorinsu bisa irin haɗin kan da sukan ba su a bakin aiki. Haka ma ya yaba wa jami’an hukumarsu bisa ƙwazon da suke nunawa wajen yin abin da ya kamata.

Duka waɗannan bayanan na ƙunshe ne cikin takardar bayani wadda ta fito ta hannun mai magana da yawun hukumar na ‘Zone C’, Jerry Attah.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *