Tsohon gwamnan Legas ya rasu

Daga AISHA ASAS

Allah ya yi wa gwamnan farar hula na farko a jihar Legas, Lateef Kayode Jakande rasuwa.

Marigayin ya bar duniya yana da shekara 91.

A halin rayuwarsa, Jakande wanda tohon ɗanjarida ne, ya yi gwamna a Jihar Legas daga 1979 zuwa 1983.

Haka nan, ya riƙe muƙamin Ministan Ayyuka a zamanin mulkin marigayi Sani Abacha.

An haifi marigayin ne a ranar 23 ga Yulin 1929, a Legas.

Gwamnan Legas, Babajide Sanwo-Olu, ya nuna alhinin dangane da rasuwar, tare da bayyana marigayin a matsayin babban rashi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *