Tsohon ɗanwasan Super Eagles ya rasu

Daga WAKILIN MU

Tsohon ɗan wasan Super Eagles Yisa Sofoluwe, ya rasu.

Sofoluwe ya rasu ne a Talatar da ta gabata a Asibitin Koyarwa ta Jami’ar Legas bayan fama da ya yi da lalurar ƙwaƙwalwa.

Tun farko sai da aka kai marigayin wata asibiti a yankin Ikorodu kafin daga bisani aka ɗauke shi zuwa asibitin jami’ar Legas.

A halin rayuwarsa, marigayin ya buga wa Nijeriya wasa da dama, ciki har da gasar cin kofin Afirka (AFCON) a 1984 da 1988.

Haka nan, ya samu zarafin buga ma wasu manyan ƙungiyon ƙwallon ƙafa na ƙasa, irin su 3SC da Julius Berger da Abiola Babes da sauransu, wasa. Marigayin ya shahara ne a fannin tsaron gida yayin wasa.

An haifi Sofoluwe ne a ranar 28 ga Disamban 1967, inda ya bar duniya yana da shekara 54.