A shirye muke mu samar wa makiyaya wuraren kiwo – Gwamnonin Arewa

Daga AISHA ASAS

Gwamnonin Arewa sun yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta tallafa musu da kuɗaɗen da za su yi amfani da su wajen samar da gandun dazazzuka a sassan yankinsu don amfanin makiyaya.

Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin Arewa kuma gwamnan jihar Filato Simon Lalong shi ne ya yi wannan kira yayin wani shirin talabijin da aka yi da shi a Talatar da ta gabata. Yana mai cewa, da dadewa gwamnonin Arewa sun yi na’am da shirin samar da gandun dazuzzukan.

Ya ce duba da yadda harkokin sace sacen mutane ke ta ƙaruwa da kuma batun umarnin ficewa da aka bai wa Fulani makiyaya a wasu wurare, samar da wuraren kiwo ne zai fi zama hanyar da za a bi don daƙile matsalar tsaron da ake fuskanta.

Don haka ya ce, “Muna shawartar Gwamnatin Tarayya da tallafa wa jihohin da suka shirya samar da wuraren kiwon da kuɗade.

“Ba wai mun ce yin hakan ya zama wajibi a kan jihohin da ba su shirya ma hakan ba ne, amma kuma akwai jihohin Arewa da dama wadanda a shirye suke su aiwatar da hakan.

“Muna buƙatar kuɗaɗe domin soma aiwatar da wannan aiki don zaunar da makiyaya wuri guda. Ta haka kawai za a iyamaganin matsalar tsaron ƙasar nan.

“Sai dai jihohi na fama da rashin kuɗi da kuma rashin ƙarfafa musu guiwa.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *