09
Feb
Daga AISHA ASAS 'Yan kasuwar man fetur sun ce bisa la'akari da yadda abubuwa ke tafiya a kasuwar ɗanyen mai ta duniya, kamata ya yi farashin fetur kan lita guda ya zama tsakanin N185 zuwa N200 a Nijeriya. Bayanan da Manhaja ta kalato sun nuna an samu tashin farashin fetur a kasuwar mai ta duniya a makon da ya gabata wanda hakan ya sanya 'yan kasuwar nuna damuwarsu kan yadda ba a aiwatar da cikakken shirin sakar wa 'yan kasuwar mara ba a harkar man fetur, lamarin da ya hana samun sauyin farashin litar fetur sama da watanni biyu A…
