‘Yan bindiga sun yi garkuwa da mutum 4 a Tungan Maje

Daga AISHA ASAS

Wasu ‘yan bindiga sun kai hari a Tungan Maje da ke yankin Gwagwalada, Abuja, inda suka yi garkuwa da wasu mutum huɗu.

Al’amarin wanda ya auku a tsakar daren wannan Lahadin, sai da ‘yan bindigar suka shafe kimanin sa’o’i uku suna abin da suka ga dama a Tungan Maje kafin daga bisani suka yi awon gaba da wani tsohon jami’in Hukumar Kula da Shige da Fice ta Nijeriya (NIS) Abdulahi Idris Rakieu da wasu mutum biyu daga iyalan gidansa.

A cewar jaridar TheCable, harin ya shafi wani mai suna Olusola Agun, wanda shi ya zama cikon na huɗu na mutanen da ‘yan ta’addar suka sace a harin da suka kai.

Sahihan bayanan da Manhaja ta tattaro sun nuna maharan sun zo ne sanye da kakin sojoji, inda suka samu shiga gidajen mutane ta haurawa katanga da kuma fasa taga.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *