Editor

9513 Posts
Atiku ya roƙi gwamnati kada ta dakatar da hada-hadar kuɗaɗen intanet

Atiku ya roƙi gwamnati kada ta dakatar da hada-hadar kuɗaɗen intanet

Daga FATUHU MUSTAPHA Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa Atiku Abubakar ya roƙi gwamnatin Shugaba Buhari kada ta dakatar da hada-hadar kuɗaɗen intanet wanda aka fi sani da 'cryptocurrency' a Turance. A Juma'ar da ta gabata Babban Bankin Nijeriya (CBN) aya bada umarnin bankuna da dangoginsu su rufe duka asusun da ke da alaƙa da harkar kuɗaɗen intanet ba tare da ɓata lokaci ba. A wata sanarwa da ya sanya wa hannu Asabar da ta gabata, Atiku ya ce kamata ya yi gwamnati ta ɗauki matakin sanya wa harakar ido maimakon daƙile ta baki ɗaya. Tare da bada misalin yadda hada-hadar kuɗaɗen…
Read More
Amnesty International na neman wargaza Nijeriya – inji Lai Mohammed

Amnesty International na neman wargaza Nijeriya – inji Lai Mohammed

Daga AISHA ASAS Gwamnatin Tarayya ta zargi Ƙungiyar Kare 'Yancin Ɗan-Adam ta Duniya (AI) da take-taken neman wargaza Nijeriya da gangar ta hanyar ɗora zarge-zarge a kan gwamnati da kuma sojoji. Ministan Labarai da Al'adu, Alhaji Lai Mohammed ne ya yi wannan zargi yayin wata hira da wata tashar talabijin ta yi da shi a Juma'ar da ta gabata a Legas wadda Hukumar Dillancin Labarai ta Nijeriya (NAN) ta bibiya. Ministan ya bayyana haka ne a matsayin martani ga wani rahoton ƙungiyar a kan yaƙi da batun take 'yancin ɗan-Adam a faɗin duniya inda ta nuna an yi zargin an…
Read More
CBN ya haramta wa bankuna hada-hadar kuɗaɗen intanet

CBN ya haramta wa bankuna hada-hadar kuɗaɗen intanet

Daga BASHIR ISAH Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya bai wa bankuna umarnin su rufe duk wani asusun ajiya da karɓar kuɗaɗe a banki da ke da alaƙa da cinikin kuɗin intanet (cryptocurrency). A Juma'ar da ta gabata CBN ya aike wa bankunan umarnin nasa zuwa bankuna masu karɓar ajiyar kuɗaɗe (DMB) da hukumomi masu hada-hadar kuɗaɗe (NBFI) da makamantansu, a kan su gaggauta daƙile dukkan asusun da ake amfani da su wajen hada-dahar kasuwar sulallan intanet (bitcoin). Idan dai za a iya tunawa a Janairun 2017 ne CBN ya bayyana cewa ana amfani da hada-hadar kuɗaɗen intanet irin sulallan bitcoin…
Read More
Ciwon daji: An damu da shi kuwa?

Ciwon daji: An damu da shi kuwa?

Daga IBRAHIM SHEME Majalisar Ɗinkin Duniya ta ware ranar 4 ga Fabrairu ta kowace shekara a matsayin Ranar Yaƙi Da Cutar Daji ta Duniya, wato a turance 'World Cancer Day'. Muhimmancin ranar shi ne mutane su tuna da irin ɓarnar da cutar ke yi da matakan da ya kamata a ɗauka don rigakafi da kuma hanyoyin magance ta. A jiya Alhamis ne wannan rana ta kama a bana. Abin mamaki, ban ji inda aka yi wata yekuwa ko gangami don tunawa da ranar ba a jiya. Akwai 'yan labarurruka da ƙungiyoyi masu yaƙi da cutar su ka ɗan yaɗa, su…
Read More
INEC za ta samar da sabbin mazaɓu a faɗin Nijeriya kafin zaɓen 2023 – Mahmood Yakubu

INEC za ta samar da sabbin mazaɓu a faɗin Nijeriya kafin zaɓen 2023 – Mahmood Yakubu

Daga WAKILIN MU Nan da lokacin da za a gudanar da babban zaɓe a Nijeriya, Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) za ta samar da ƙarin mazaɓu a faɗin ƙasar. Shugaban kwamitin wayar da kan masu zaɓe a hukumar (IVEC), Mista Festus Okoye, shi ne ya bayyana haka a Abuja. Kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito, a cikin Agustan 2014 INEC ta gabatar da buƙatar samar da ƙarin mazaɓu 30,027, inda arewacin ƙasar za ta samu mazaɓu 21,615 yayin da kudu za ta samu 8,412. Wannan ya janyo ce-ce-ku-cen da ya sa INEC ta watsar da shirin. Shugaban hukumar, Farfesa Mahmood Yakubu, ya…
Read More
Hukumar Kwastam ta tara bilyan N4b a cikin wata guda

Hukumar Kwastam ta tara bilyan N4b a cikin wata guda

Daga FATUHU MUSTAPHA Hukumar Yaƙi da Fasa Ƙwauri ta Ƙasa reshen Oyo/Osun ƙarƙashin jagorancin Comptroller AR Abdulkadir, ta ce ta samu nasarori da daman gaske wajen aiwatar da harkokinta. Yayin ganawar da ya yi da manema larabai a Alhamis da ta gabata, Comptroller Abdulkadir ya ce a watan Janairun da ya gabata kaɗai sun tara wa gwamnati kuɗin shiga da ya kai sama da bilyan N4.895. Ya ce tsakanin Nuwamba da Janairun da suka gabata, sun yi nasar kama ɓatagari da dama da kuma kayayyakin fasa ƙwauri wanda a kiyasce harajinsu ya haura Naira milyan 393. A cewar jami'in, kayayyakin…
Read More
NUJ ta yi gargaɗin a sako mata ɗanta da aka sace

NUJ ta yi gargaɗin a sako mata ɗanta da aka sace

Daga AISHA ASAS Ƙungiyar 'Yan Jarida ta Ƙasa (NUJ) reshen Birnin Tarayya, Abuja, ta yi kira da a gaggauta sako mata ɗanta Okechukwu Nnodim ma'aikaci a Jaridar Punch. Bayanan da suka fito daga ƙungiyar sun yi zargin cewa har gida wasu 'yan bindiga suka bi Nnodim suka yi gaba da shi, bayan da suka yi harbe-harbe a iska da bindigoginsu. Takardar da ƙungiyar ta fitar wadda shugabanta Comrade Emmanuel Ogbeche da sakatarenta Ochiaka Ugwu suka sanya wa hannu, ta nuna yadda ƙungiyar ta yi tir da wannan ɗanyen aiki, tare da neman a sako Nnodim ba tare da wani sharaɗi…
Read More
Mun shirya wa yin zaɓen cike gurbi a Neja, cewar INEC da ‘yan sanda

Mun shirya wa yin zaɓen cike gurbi a Neja, cewar INEC da ‘yan sanda

Daga WAKILIN MU Kwamishinan Zaɓe mai zama a Jihar Neja (REC), Farfesa Samuel Egwu, ya ce Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta gama shiryawa tsaf domin gudanar da zaɓen cike gurbi da za a yi a Mazaɓar Tarayya ta Magama/Rijau da ke jihar a ranar Asabar, 6 ga Fabrairu, 2021. Egwu ya faɗi haka ne a ranar Alhamis lokacin da ya ke tattaunawa da wakilin Hukumar Dillancin Labarai ta Nijeriya (NAN) a Minna. Ya ce hukumar sa ta gama duk wani shirin yin zaɓe mai inganci da tsare gaskiya, domin kuwa ta horas da ma'aikatan zaɓe mutum 1,258 saboda zaɓen.  Ya…
Read More
An samu ɗimbin cigaba a ƙarƙashin APC – cewar Bello

An samu ɗimbin cigaba a ƙarƙashin APC – cewar Bello

Daga BASHIR ISAH Ministan Abuja Malam Muhammad Musa Bello ya ce, gwamnatin jam'iyyar APC ta samar da cigaba masu yawa tun bayan kama mulki a 2015. Bello ya bayyana haka ne a lokacin da ya karɓi baƙuncin kwamitin shirin sabunta rijistar mambobin APC na Abuja a Alhamis da ta gabata. Yana mai cewa, "Waɗanda suke mazauna Abuja, ko masu yawan ziyartar ta a 2015, sun san akwai bambanci da Abuja ta wancan lokaci da ta yanzu." Daga nan, Bello ya nuna gamsuwarsa dangane da naɗa Hon. Sanda Umar Garba da aka yi a matsayin Shugaban Kwamitin Kula da Shirin Sabunta…
Read More
Cutar Korona: An samu ƙarin mutum 1,340 da suka harbu a faɗin ƙasa

Cutar Korona: An samu ƙarin mutum 1,340 da suka harbu a faɗin ƙasa

Daga FATUHU MUSTAPHA A halin da ake ciki, birnin tarayya, Abuja da jihar Legas da River da kuma Oyo, su ne jihohin da ke kan gaba wajen samun mafi yawan waɗanda suka harbu da cutar korona a tsakanin sa'o'i 24 da suka gabata. Bayanan Cibiyar Daƙile Yaɗuwar Cututtuka ta Ƙasa (NCDC), sun nuna an samu ƙarin mutum 1,340 da suka kamu da cutar korona. Ƙarin da cibiyar ta ce ya shafi wasu jihohin ƙasar nan su 22, ciki har da Abuja 320, Lagos 275, Rivers 117, da kuma Oyo 100. Sauran sun haɗa da Sakkwato 3, Kaduna 31, Katsina 14,…
Read More