05
Feb
Daga AISHA ASAS Haɗaɗɗen Kwamitin Ƙungiyar Ma'aikatan Jami'o'i (NASU) da kuma Ƙungiyar Manyan Ma'aikatan Jami'o'i (SSANU), ya tsayar da ranar Juma'a (05/02/2021) a matsayin ranar da mambobin ƙungiyoyin biyu za su soma yajin aiki na sai baba-ta-gani sakamakon gazawar da suka ce gwamnati ta yi wajen biya musu buƙatunsu. Tun farko, sai da ƙungiyoyin suka bai wa gwamnati wa'adin makonni kan ta magance musu matsalolinsu ko kuma su tsunduma yajin aiki. Shugaban SSANU Muhammed Haruna, ya shaida wa Manhaja cewa, babu wata yarjejeniya da ƙungiyoyin suka cim ma da gwamnati kan janye ƙudirin shiga yajin aikin. Yana mai cewa, tattaunawar…
