Editor

9513 Posts
Marigayi Momoh: “Dattijo mai dattako, mai kishin ƙasa, ɗan jarida abin koyi” – inji Tinubu

Marigayi Momoh: “Dattijo mai dattako, mai kishin ƙasa, ɗan jarida abin koyi” – inji Tinubu

Daga UMAR M. GOMBE Tsohon Gwamnan Jihar Legas kuma jigo a jam'iyyar APC mai mulki, Chief Bola Tinubu, ya bayyana marigayi Tony Momoh a matsayin "Dattijo mai dattako, mai kishin ƙasa kuma ɗan jarida abin koyi." A saƙon ta'aziyya da ya fitar ta hannun mai taimaka masa kan sha'anin labarai, Mr Tunde Rahman, Tinubu ya bayyana alhininsa dangane da mutuwar Tony Momoh. Yana mai cewa, "Na tuna wata tattaunawar da aka yi da shi da na karanta a ɗaya daga cikin jaridun ƙasar nan a 'yan kwanakin da suka gabata, inda ya bayyana irin son da yake yi wa ƙasarsa…
Read More
DSS ta yi gargaɗi kan take-taken neman tada rikici a ƙasa

DSS ta yi gargaɗi kan take-taken neman tada rikici a ƙasa

Daga AISHA ASAS Hukumar Tsaro ta DSS, ta yi gargaɗi kan take-taken da wasu mutane da kuma ƙungiyoyi ke yi na neman haddasa rikicin addini da na ƙabilanci a wasu sassan ƙasa. Jami'in Hulɗa da Jama'a na Ƙasa na hukumar, Dr Peter Afunanya, shi ne ya yi wannan gargaɗi a wani bayani da ya yi a Abuja, a ranar Laraba. Ko a ranar 11 ga Janairun da ya gabata, sai da hukumar ta yi makamancin wannan gargaɗi inda ta ce, akwai wasu da ke mummunan tanadi don tayar da rikicin addini a ƙasa. A cewar DSS, wuraren da ake hari…
Read More
Bankin Zenith ya ciri tuta

Bankin Zenith ya ciri tuta

Daga FATUHU MUSTAPHA A karo na huɗu a jere, bankin Zenith ya sake zama bankin da ya ɗara takwarorinsa ingancin tsarin gudanarwa a Nijeriya kamar yadda mujallar Banker Magazine ta nuna. Daga jerin bankuna 'yan sahun gaba su 500 da mujallar ta nuna a 2021, ta ayyana Bankin Zenith a matsayin bankin da ke kan gaba wajen tsarin aiki a Nijeriya. Mujallar ta nuna cewa, ƙarfin jarin Bankin Zenith ya kai Dalar Amurka milyan 275 wanda hakan ya sa ya zama bankin da ya samu cigaba daga matsayi na 392 a 2020 zuwa matsayi na 390 a 2021 a matakin…
Read More
Myanmar: Magoya baya sun buƙaci a sako Suu Kyi da sauransu

Myanmar: Magoya baya sun buƙaci a sako Suu Kyi da sauransu

Daga WAKILIN MU 'Yan jam'iyyar National League for Democracy a ƙasar Myanmar, sun yi kira da a sako Aung San Suu Kyi tare da sauran jagororinsu da aka tsare a Talatar da ta gabata. Suna masu bayyana juyin mulkin da sojojin ƙasar suka yi a ƙasar a matsayin al'amari da ya yi wa tarihin sojin ƙasar tabo mara kyau. Da sanyin safiyar Litinin da ta gabata sojoji suka kama Suu Kyi da ta kasance shugabar jam'iyyarsu tare da shugaban ƙasar, Win Myint. Bayan juyin mulkin, ba tare da ɓata lokaci ba sojojin suka naɗa wani tsohon janar, Min Aung Hlaing,…
Read More
Perez ya harbu da cutar korona

Perez ya harbu da cutar korona

Shugaban ƙungiyar ƙwallon ƙafa na Real Madrid, Florentino Perez, ya harbu da cutar korona. Ƙugiyar Madrid da kanta ta sanar da hakan a shafinta na 'Twitter' a Talatar da ta gabata. Inda ta ce, “Real Madrid CF na sanar da cewa an gano shugabanmu Florentino Perez ya kamu da cutar korona bayan gwaje-gwajen da aka yi masa, duk da dai bai nuna wata alamar kamuwa da cutar ba." Da wannan, ana sa ran Perez ya shafe sama da mako guda a killace har sai an tabbatar ya rabu da cutar kafin ya koma bakin aiki a Santiago Bernabeu.
Read More
Jami’an kwastam sun yi kamu a  Ogun

Jami’an kwastam sun yi kamu a Ogun

Daga WAKILIN MU A safiyar Talata (02/02/2021), wasu da ake zargin 'yan fasa-ƙwauri ne suka kai wa jami'an Hukumar Yaƙi da Fasa-ƙwauri na shiyyar 'Zone A' hari yayin da suke bakin aiki a kan babban hanyar Abeokuta a jihr Ogun. Bayanan da jaridar Manhaja ta samu sun nuna cewa, waɗanda lamarin ya shafa sun yi haka ne domin tirjiya daga kamun jami'an a daidai lokacin da suke ƙoƙarin arcewa da shinkafar ƙetare maƙare cikin motocinsu. Bayanai sun nuna cewa, bayan da jami'an Kwastam suka kama motocin ne sai wasu ɓatagari da ke goyon bayan 'yan fasa-ƙwaurin suka haɗa kansu suka…
Read More
China ta haramta wa ɗaliban firamare shiga aji da waya

China ta haramta wa ɗaliban firamare shiga aji da waya

Daga FATUHU MUSTAPHA Kasar China ta sanar da ɗaukar matakin haramta wa ɗalibai 'yan firame da na sakandare yin amfani da wayoyin salula a cikin aji. China ta ce, ta ɗauki wannan mataki ne domin kare ɗaliban daga fitinar intanet da kuma 'TV game' da kan hana ɗalibai maida hankali kan karatu yadda ya kamata. A wata takardar sanarwa da Ma'aikatar Ilimin ƙasar ta raba wa makarantu a Litinin da ta gabata, ma'aikatar ta ce daga yanzu ba a yarda ɗlibai a makarantun firamare da sakandare su riƙa amfani da wayoyi a aji ba. Tana mai cewa, "Duk ɗalibin da…
Read More
Rasuwar Momoh: Na rasa babban amini – inji Buhari

Rasuwar Momoh: Na rasa babban amini – inji Buhari

Daga UMAR M. GOMBE Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya bayyana alhininsa dangane da rasuwar amininsa Prince Tony Momoh. A wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Femi Adesina ya fitar a Litinin da ta gabata a Abuja, Shugaba Buhari ya bayyana cewa, marigayin ya kasance tare da shi a duk faɗi-tashin da ya sha. Yana mai cewa, "Samun kwatankwacin marigayin wajen biyayya a fagen siyasa, abu ne mai wahalar gaske. Zan yi rashin sa matuƙa." Jaridar Manhaja ta kalato Buhari ya yi tuna baya inda ya ce, "Marigayi Momoh ya ba da gagarumar gudunmawa a matsayinsa na Shugaban Sashen Yaɗa…
Read More
Sadarwa: Gwamnati ta tsawaita wa’adin shirin haɗe layukan sadarwa da lambar NIN

Sadarwa: Gwamnati ta tsawaita wa’adin shirin haɗe layukan sadarwa da lambar NIN

Daga FATUHU MUSTAPHA Gwamnatin Tarayya ta ƙara wa'adin shirin haɗe Lambar Shaidar Ɗan Ƙasa da layukan sadarwa da makonni 8 domin bai wa 'yan ƙasa isasshen lokaci don su sada layukan sadarwarsu da lambar NIN. Sabon wa'adin da gwamnatin ta tsayar yanzu, shi ne zuwa ranar 6 ga Afrilu mai zuwa. Daraktan Hulɗa da Jama'a na Hukumar Sadarwa ta Ƙasa, Dr Ikechukwu Adinde, shi ne ya ba da bayanin haka a ranar Talata. Inda ya ce, Ministan Sadarwa Isa Pantami ne ya ba da umarnin tsawaita wa'adin bayan taron kwamitin sanya ido kan shirin haɗe lambar NIN da layukana sadarwa.…
Read More
Tsoffin hafsoshin Nijeriya: Ba ritaya ba ce, kora ce – Shehu Sani

Tsoffin hafsoshin Nijeriya: Ba ritaya ba ce, kora ce – Shehu Sani

Daga AISHA ASAS Sanata Kwamared Shehu Sani, tsohon ɗan majalisa mai wakiltar Kaduna ta Tsakiya a Majalisar Dattawa ta takwas, mutum ne wanda ya yi suna wajen faɗa wa gwamnati gaskiya komai ɗacin ta tun lokacin da sojoji ke mulkin ƙasar nan. Kuma ɗan gwagwarmaya ne sannan shugaban Ƙungiyar Kare Haƙƙin Ɗan’adam, CRC. A wannan hirar da Manhaja ta yi da shi, ya nuna illolin da ciwo bashi kan iya jawowa, da kuma yin gugar zana ga gwamnatin Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari a kan batun ritayar da manyan hafsoshin tsaron ƙasar nan su ka yi bayan yekuwar da jama’ar ƙasar…
Read More