Daga WAKILIN MU
A safiyar Talata (02/02/2021), wasu da ake zargin ‘yan fasa-ƙwauri ne suka kai wa jami’an Hukumar Yaƙi da Fasa-ƙwauri na shiyyar ‘Zone A’ hari yayin da suke bakin aiki a kan babban hanyar Abeokuta a jihr Ogun.
Bayanan da jaridar Manhaja ta samu sun nuna cewa, waɗanda lamarin ya shafa sun yi haka ne domin tirjiya daga kamun jami’an a daidai lokacin da suke ƙoƙarin arcewa da shinkafar ƙetare maƙare cikin motocinsu.
Bayanai sun nuna cewa, bayan da jami’an Kwastam suka kama motocin ne sai wasu ɓatagari da ke goyon bayan ‘yan fasa-ƙwaurin suka haɗa kansu suka far wa jami’an don su hana su wucewa da shinkafar da suka kama.
A ƙarshe dai jami’an na Kwastam sun yi galaba a kan ɓatagarin bayan musayar wuta da suka yi wanda haka ya yi sanadin jam’ian Kwastam uku da soja guda sun ji rauni.
Mataimakin Konturola Usman Yahaya, ya bayyana cewa, jami’an da suka ji rauni na ci gaba da samun kulawa a wata asibiti da ke Legas.
Yahaya ya jinjina tare da yaba wa jami’an game da jaruntar da suka nuna. Sananan ya gargaɗi matasan yankin da lamarin ya shafa da su daina bari ana amfani da su wajen yi wa tattalin arzikin ƙasa illa.