Editor

9513 Posts
Mace da kwalliya aka san ta

Mace da kwalliya aka san ta

Daga MARYAM ABDURAHMAN Mace da kwalliya aka san ta, wacce ba ta kwalliya ba ta cika mace a zahirin ta ba. Babu mace mummuna sai dai macen da ba ta kwalliya. Sai dai kwalliyar ma kala-kala ce, wasu kwalliyar suna su ka tara, don ba zai yiwu a shafa 'foundation' a fuskar da ba ta da haske a yi tsammanin samun kwalliyar raɗau ba. In nace haske ba ina nufin farin fata ba, ina nufin ƙyalli na gyara. Yawancin mutanen mu suna tsorata da maganar kayan gyaran jiki don tsadar su, a rashin sanin su da kuɗi ƙalilan za su…
Read More
Wata baƙuwar cuta ta fara kashe mutane a Sakkwato

Wata baƙuwar cuta ta fara kashe mutane a Sakkwato

Daga UMAR GWARANYO Gwamnatin Jihar Sokoto ta fidda wata sanarwa mai bayyana ɓarkewar wata sabuwar cuta a wani ɓangare na jihar. Sanarwar mai ɗauke da sa hannun Gwamna Jihar, Aminu Waziri Tambuwal, ta bayyana cewa mutane huɗu sun mutu daga cutar. Haka kuma sanarwar ta nuna adadin mutanen da suke asibiti a halin yanzu suna karɓar magani sun haura 20. Gwamna Aminu Waziri Tambuwal ya ce, “A yanzu haka mutane 24 na karɓar kulawa a asibitoci daban-daban a faɗin jihar. Amma an ƙirƙiri wani kwamiti da nufin bincikar cutar tare da gano maganin ta da rigakafin ta." Gwamnan ya ce…
Read More
Nijeriya za ta fi Indiya cin gajiyar kasuwancin fasaha a nan gaba, inji NITDA

Nijeriya za ta fi Indiya cin gajiyar kasuwancin fasaha a nan gaba, inji NITDA

Daga UMAR M. GOMBE Shugaban Hukumar Bunƙasa Ilimin Fasahar Zamani NITDA, Malam Kashifu Inuwa Abdullahi, ya bayyana cewa shirye-shiryen hukumar wajen bunƙasa kasuwanci ta fuskar amfani da kafofin intanet a Nijeriya sun yi nisa, inda Nijeriya za ta zarta Indiya damar kasuwancin fasahar zamani. Babban Daraktan ya shaida haka ne ga manema labarai a babban ofishin hukumar dake Abuja, a yayin da yake bayyana matakan da hukumar ke ɗauka don ganin Nijeriya ta bi sahun ƙasashen duniya a fanin kimiyya da fasahar zamani a ɓangaren kasuwanci. Ya ce hukumar ta zo da wani tsari da ake kira 'Strategic Roadmap' wanda…
Read More

Sababbin hafsoshin Buhari

An daɗe ana kira da roƙo ga Shugaba Muhammadu Buhari da ya sauya manyan hafsoshin sojan ƙasar nan masu jagorancin rundunonin tsaro, amma ya na ƙi. Sai da ta kai Majalisar Tarayya ta zartar da ƙudirori a kan lallai ne Shugaban ya kori hafsoshin, amma dai maganar ta wuce ta bayan kunnen sa. Dalilai biyu su ka sanya aka riƙa yi masa wannan kiran. Na farko shi ne, wa’adin hafsoshin ya wuce, har ma ana ganin sun fara cin wa’adin wasu hafsoshin domin tun a cikin 2015 aka naɗa su. Dalili na biyu kuma shi ne gazawar da ake ganin…
Read More
Shin in Fulani makiyaya su ka fice daga Ondo salama ta samu?

Shin in Fulani makiyaya su ka fice daga Ondo salama ta samu?

Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA Wa’adin da Gwamnan Ondo Rotimi Akeredolu, ya bai wa Fulani makiyaya su fice daga dazukan jihar sa, ya haddasa muhawara mai zafi tsakanin kudanci da arewacin Nijeriya. Muhawarar ta dogara ga yadda mai sharhi ko ra’ayi ya ke ganin abun. Ga masu ɗaukar makiyaya ko Fulani makiyaya cewa ’yan Arewa ne ko ma ’yan’uwan su ko ma a ce su na dangantaka da Musulunci ko da ma a iya samun mabiya adddinin Kirista a cikin su da waɗanda ba su san ko “Ba Sin Mi Ara Ba...” to, za su ɗauki wa’adin da Akeredolu ya ba…
Read More
Lokacin siyasa ne lokacin da na fi so – Farida Abubakar

Lokacin siyasa ne lokacin da na fi so – Farida Abubakar

Daga AISHA ASAS Hajiya Farida Abubakar mace mai kamar maza, wadda ta ke da kishin neman na kanta ba tare da jiran miji ko iyaye sun yi mata hidimar ta ba, kuma macen da ta riƙi sana’ar gasa Burodi da hannu bibbiyu, wadda har ta kai ta matsayin da ta ke a yanzu. mace ce da ya kamata mata su yi koyi da ita, domin ta haɗa taura biyu a lokaci guda, wato aiki da kasuwanci. A wannan hirar da wakiliyar mu ta yi da ita, masu karatu za su ji yadda ta fara wannan sana’a. Masu karatun mu za…
Read More
Rashawa: SERAP ta buƙaci a binciki ɓacewar biliyan N4.4 a Majalisar Tarayya

Rashawa: SERAP ta buƙaci a binciki ɓacewar biliyan N4.4 a Majalisar Tarayya

Ƙungiyar Kare 'Yancin Zamantakewa Da Yaƙi Da Cin Hanci (SERAP), ta yi kira ga Shugaban Majalisar Dattawa Dr Ahmad Lawan, da takwaransa na Majalisar Wakilai ta Ƙasa, Femi Gbajabiamila, a kan su buƙaci hukumomin yaƙi da rashawa su binciki badaƙalar ɓatan dabon da kasafin biliyan N4.4 na Majalisar Tarayya ya yi kamar yadda rahotannin binciken ofishin Babban Jami'in Bincike na Ƙasa suka nuna. A wata wasiƙa da ta samu sa hannun mataimakin daraktan SERAP, Kolawole Oluwadare, ƙungiyar ta ce, "Ta hanyar kwatanta jagoranci nagari a kan wannan batu, Majalisar Tarayya za ta iya nuna wa 'yan Nijeriya cewa ɓangaren yin…
Read More
China: An cafke mutum 80 masu haɗa jabun rigakafin cutar korona

China: An cafke mutum 80 masu haɗa jabun rigakafin cutar korona

Daga WAKILIN MU Rahotanni daga ƙasar China sun nuna hukumomin ƙasar sun cafke wasu mutum 80 bisa zarginsu da harkar haɗa jabun maganin allurar rigakafin cutar korona. Wani kamfanin dillancin labarai na ƙasar, Xinhua ya ruwaito cewa, ana zargin tun a watan Satumban da ya gabata waɗanda lamarin ya shafa suka soma harkar haɗa jabun rigakafin korona tare da sayar wa mutane da sunan magani mai inganci. Hukumomin ƙasar sun ce, jabun rigakafin korona guda 3000 suka kama waɗanda aka yi aikin haɗawa a sassa daba-daban a ƙasar. Kafin wannan lokaci, China ta samar da allurar rigakafin cutar korona da…
Read More
An kammala musabaƙar Ƙur’ani karo na 35 a Jos

An kammala musabaƙar Ƙur’ani karo na 35 a Jos

Daga UMAR M. GOMBE A Lahadin da ta gabata aka kammala musabaƙar karatun Alƙur'ani karo na 35 a garin Jos, Jihar Filato, ƙarƙashin Ƙungiyar Jama’atu Nasril Islam (JNI). Da yake jawabi a wajen taron, Babban Sakataren JNI, Sheikh Khalid Aliyu Abubakar, ya yi kira ga iyaye da su kula da tarbiyyar 'ya'yansu da kuma ba su ilimi mai inganci domin samun zaman lafiya da tsaron da ake fata a ƙasa baki ɗaya. Ya ce, "Wajibi ne a kan iyaye su tabbatarda sun bai wa 'ya'yansu nagartacciyar tarbiyya tare da ilimantar da su." Yana mai cewa, "sha'anin tsaro shi ne ƙashin…
Read More
Yaƙi Da Matsalar Tsaro: Zulum ya ƙalubalanci shugabannin tsaro su kyautata alaƙa da takwarorinsu

Yaƙi Da Matsalar Tsaro: Zulum ya ƙalubalanci shugabannin tsaro su kyautata alaƙa da takwarorinsu

Daga AISHA ASAS Gwamnan Jihar Barno, Babagana Umara Zulum, ya ƙalubalanci sabbin shugabannin tsaro da su assasa kyakkyawar alaƙar aiki a tsakaninsu da ƙasashen da Nijeriya ke maƙwabtaka da su, wato Chadi da Kamaru da kuma Nijar. Kazalika, ya shawarci manyan hafsoshin da su kasance masu haƙuri da kuma sauraron jama'a a halin aiwatar da ayyukansu. Gwaman ya faɗa wa jami'an haka ne sa'ilin da ya karɓi baƙuncinsu a fadar gwamnatin jihar a Lahadin da ta gabata yayin da suka yi ziyarar aiki ta farko a jihar. Shugaban tsaro Major-General Leo Irabor, shi ne ya jagoranci takwarorinsa Major-General Ibrahim Attahiru…
Read More